π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
ππππππ
π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
©PERFECT WRITERS FORUM
(P.W.F)❤️
πππππ
*KHALEEL*
πππππ
Written by Maryam S bello {MSB}✍π»
http://MaryamSBello.blogspot.com
February 2017π
PAGE
✍π»✍π»33&44✍π»✍π»
Ta juyo da sauri har ta kusa cin karo da shi, da hanzari tayi baya. Ta d'aga ido tana k'are masa kallo sanye yake cikin farar singileti da bak'in gajeren wando, sai takalmin Adidas, yayi murmushi yace
"Yanzu kin kyauta kenan? Har kika tashi sallah bazaki tashe ni ba ko, shikenan alhaki ya hau kanki"
Juya tayi da sauri tayi kamar bata jishi ba, sannan ta juya tayi cikin gida.
Biyo ta yayi harda d'an gudunsa yace
"Hanifah! Muje ki bani abinci yunwa nakeji"
Kamar ta bigeshi ya fad'i k'asa haka take ji don takaici da haushi. Tace
"Ko kunya wai ni zaiyi wa shagwab'a da wata shegiyar shigarsa sai kace wani yaro"
Da sauri ya cimmata tare da chafko hannunta yace
"Kinma isa yarinya ki barni biya, mu shiga tare"
Haushi ya turnik'e ta, ta fara kicinyar k'wace hannunta amma ina! Ta kasa dole ta hak'ura suka k'arasa ciki tare.
Ya zauna kan kujera Hanifah ta zuba masa tsurar doyar da ko soyawa batayi ba, ta had'o masa ruwan tea ta tura masa gabansa, sannan tasamu wuri ta zauna tana fuskantarsa tana jiran ya gama ta kwashe kayan kamar yadda yayi mata umarni!
Yana ci yana karkad'a kai da k'afa yana d'an girgiza kansa, har ya kammala babu wani complain kamar yadda Hanifah ta buk'ata, sanin cewar Khaleel mutum ne shi mai son varieties na abinci, yana son ya ga an cika masa abinci kala kala kamar yadda Ammi ke masa, bama kamar da safe koda rana. Haushi ya kama Hanifah taso ace yaci abincin yayi complain ko ta ji dad'i.
"Tattara kayan ki same ni d'aki na"
Ya fad'a tare da mik'ewa tsaye. Tace to tare da watsa masa wata uwar harara wane zata zazzago da idonta waje.
Zaune yake kan carpet ya baja takardu a gabansa yana duddubawa, nuna mata kusa dashi yayi alamun ta zauna, ta zauna fuskar nan tamau kamar hadari, ya kalleta sai yaji dariya ta ku6uce masa, ya sunkuyar da kansa k'asa yayi dariyarsa sannan ya d'ago yana kallonta yace.
"Hanifah kenan, kina fa burgeni ba kad'an ba, wannan fuska taki kamar tsohuwa taga zaki"
Ta k'ara tsuke fuska. Khaleel ya girgiza kansa ya soma magana
"Wannan takardun na rabon gadonmu ne wanda aka bani saboda haka na d'auki kaso na dama harda wannan gidan wanda Abbanki ya fara ginawa shine ya mallaka min shi halak malak, ku kuma ga naku keda Saif, idan ma kinason zuwa sai na kaiki, idan kuma sai Saif ya dawo nan da wata biyu a lokacin ya kammala masters d'insa to ba matsala, zaki iya ajewa har sai ya dawo, kud'ad'en kuwa, kowa na tura masa a account d'insa"
Ta kwashi takardun zata mik'e ya ce
"Sorry ban gama magana ba y'alla6ai"
Ta gyara zamanta amma ko uffan bata ceba, ya cigaba.
"Ina so ki sanar dani irin motar da kikeso zan bada ayi miki order, don ki samu ki fara koya"
Da sauri ta d'ago tana dubansa, annurin fuskarta ya bayyana, batason lokacin da dariya ta ku6uce mata ba, komai ta tuna kuma sai ta d'aure fuska tace
"Bana son motarka ka rik'e kayanka, bana buk'ata"
Yayi dariya yace
"Dama ay bance kinaso ba dole, idan har baki sanar dani ba toh zan siyo miki duk wacce ta kwanta min a rai"
Tace
"Wannan kuma za6inka ne kai kaji zaka iya"
Ita kanta tayi mamakin yadda akayi ta iya fad'a masa magana haka.
Daga haka bai k'ara magana haka itama ta mik'e tayi dak'inta da sauri.
*******
Zaune Hanifah take a d'akinta, tunani ya isheta tare da mamakin chanzawan Khaleel lokaci d'aya.
Yau sati biyu da bikinsu, amma abin mamaki tun ranar da abinnan ya faru ta fad'a masa magana bai k'ara mata magana ba, gashi dai wulak'ancin yau daban na gobe daban take masa, amma ko uhm bai ce mata, kamar idan ta kai masa abinci ta zauna zaman jira ya gama, tana lura zai ci abincin kad'an sannan ya k'ura mata ido, sai ta zo mik'ewa da sauri zai riga ta tashi.
Ga bata yi masa wani abin da'di daga doya sai dankali babu ko k'wai da safe kenan, da rana kuwa dama farar taliya takeyi idan yaso yaci da manja wannan ruwansa, ita babu abinda ya dame ta.
Haka to abubuwan ke gudana, zaman kurame sukeyi a gidan, idan kuwa ita Hanifah ta ga dama sai ta ya6a masa magana son ranta, amma ko uhm bai ce mata, irin abin yafi ciwo kayi ta magana a maida ka kamar wani banza.
Kullum Hanifah ke riga Khaleel tashi, da ta tashi zatayi kitchen don had'a kalaci, idan Khaleel ya tashi zai gyara gadon ya share d'akin ya goge, da kansa yake jona abin turaren wuta.
Gaba d'aya ya zama wani shiru shiru, duk wani fad'ansa, da nuna isa da gadara duk ya sauke su, ya maida kansa kamar wani yaro, a lokacin ita kuma Hanifah ta baje kolin iskancinta kala kala.
A haka motar Hanifah ta iso, sabuwa dal agogo a leda, KIA bak'a wulik! Kuma ya bada umarnin koya mata da kansa, sai a nan taga Khaleel d'in da, cikin ikon Allah kuwa cikin sati d'aya ta k'ware ba inda bata shiga.
*******
Ranar wata saturday Hanifah bata tashi da wuri ba, ta duba agogo k'arfe takwas da rabi ta kalla ba Khaleel kusa da ita, wato ramawa yayi kenan.
Ko wanka batayi ba ta fad'a kitchen, tana cikin soya dankali Haruna d'an aiken su ne yayi sallama, hannunsa d'auke da da katon d'in su swan, da lemuna, ya dire yana gaishe da Hanifah. Ta amsa ba tare data kalle shi ba.
Bayan ta kammala ta nufi d'akinta don yin wanka, abin mamaki Khaleel ne tsaye yana jera gugar Haninfah da aka kawo jiya da yamma, tsaye tayi turus ta cika da mamaki! Yanzu sauk'in kansa har ya kai haka? Kai ina yaudara ce ko kin manta halinsa? Mugu fa ne wanda baya son farin cikinki, haka tayi tsaye tayi ta sak'e sak'e a ranta.
D'agowa yayi suka had'a ido ya sakar mata murmushi.
"Kinga yau ban tashe ki ba ko? Naga bakya sallah sannan kin sha fama da ciwon ciki ga bakiyi bacci da wuri ba, sheyasa na k'yale ki don na kula baccin yana miki dad'i bana son na katse miki shi"
Bata tanka ba har ya gama zubarsa dama shi take jira ya gama, da ya lura bata tanka ba sai yayi shiru har ya gama gyara kayan.
Haka suka zauna kan dinning kamar kullum har ya gama, ta mik'e ta tattara kayan ta kai kitchen ta dawo a lokacin baya wurin, ta gyara wurin ta kimtsa sannan ta nufi d'aki.
Tana shiga d'aki nan ma taga baya nan, taji dad'i sosai, shirin wanka tayi ta fad'a toilet.
K'arfe sha biyu saura ta kammala ta fito, kitchen ta nufa ta d'ora farar macaroni dama akwai miya a fridge ta d'umama, abincin kenan kullum daga taliya sai macaroni amma ko a jikinsa.
Ta jera kan dinning, ta hau karanta wani online novel a wattpad mai suna Bond.
Sai dai 6angate d'aya na zuciyarta na tunanin dalilin da yasa ya Khaleel ya chanza mata, gashi kullum addu'arta d'aya Allah yasa masa tausayinta ya sallame ta daga wannan auren wanda take ji tamkar tana kurkuku ne.
K'ara shigowar message taji, ta mik'e zaune tana dubawa, ga abinda aka ce.
"Gaisuwa a gareta Hanifah tare da fatan alkhairi, bazan iya bayyana miki da ko ni wanene ba,amma abu d'aya zuwa biyu nakeso na sanar da ki. Na farko!
"Kin yaudare ni, kinyi aurenki ashe dama haka kike mayaudariya, to ki sani baki ci bulus ba sai na d'auki mataki akan haka, sannan abu na biyu!! Na baki nan da wata d'aya kiyi getting rid of that your stupid husband and come back to me, or else you left me with no other choice than to....
Kinsan dai sauran, zan iya yin komai don na cimma ma burina. Bisslama na barki lafiya"
Tashi tayi zaune tana zaro idanu waje, gumi take had'awa duk kuwa da sanyin ac d'in da ke d'akin. To wannan waye? Kuma a ina ya samu number ta?" Shine tambayar da take ta jera kanta kenan, can kuma ta zabura ta mik'e zaune tare da fad'in Deen....!
MSB✍πΌ
No comments:
Post a Comment