Sunday, 12 February 2017

KHALEEL Page 3&4

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀


 ®TALENTED WRITER'S GROUP(TWG)✍🏻

                 🎀🎀🎀🎀
                  *UNCLE*
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
                 🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


I dedicated this page to Zee Elkaseem, Aunty zee, jameela K mashi, Rash, chuchu, susu, first lady💙 and my kawaye zee and faty (One love)💝
 

              PAGE

✍🏻✍🏻✍🏻3&4✍🏻✍🏻✍🏻



*FARKON LABARI*


Gida ne na gani na fada a cikin  Unguwar Rimi dake cikin garin kaduna, katafaren tsakar gidan an kakkafa canopies (rumfuna), mutune ne zaune ko wane daka kalle shi kasan ba lafiya ba, cikin gidan kuwa bakajin komai sai koke koken mata, Ammi ce zaune rungume da Khaleel yaro dan shekara hudu yana ta kuka, ta shafa kansa tana ta rarrashi. Idanun Ammi sunyi jajir sun kankance saboda kuka, mijinta da dan uwansa tilo daya, da ya rage masa duk fadin duniya yau gashi sun koma ga Allah tare, abokin shawarsa kwaya daya tak, su tashi tare su fadi tare, yau babu ko dayansu,  mummuman hadari sukayi a hanyar kano kuma dukansu sun rasa ransu. Ita kadai tasan me takeji a cikin zuciyarta har wani zafi take mata. Wata mata ce dauke da yaro dan kimanin shekara biyu yana kuka aka mika ma Ammi shi, ta kalli Khaleel zaune a gefenta sai taji duk tausayinsa ya kama ta, wanda hakan ce ta kasance da Saif shima ta kalle shi sai taji tausayinsa saboda dukkansu sun rasa uba, bama kamar Khaleel da bashida uwa kwata kwata baisan dadinta ba, saboda wurin haihuwarsa ta rasa ranta, kuma mahaifinsa ya kasa aure shi ya cigaba da kula dashi har ya fara girma, gashi shima babu shi a yau. Kuka take wiwi tana tuno da rayuwarsu.
Hadarin ya faru ne da daddare da misalin goma sha dayan dare. Don haka washe gari da motar asibiti aka dauko gawarwakin.
Mutane suka shiga tittodowa don hallartar jana'izar (Alhaji Usman{mahaifin Khalel) da kuma Alhaji (Abdul'aziz {maigidan Ammi}) babban mutum ne wanda ya taka matakin minister sannan tarihin Nigeria bazai ta6a mantawa da shi ba, sunyi rashi babba bayaga miji na gari ga Ammi, mutum ne shi mai matukar saukin kai da sanin ya kamata.

Ammi tasha kuka har ta gode Allah, sai dai da yake macece mai imani da riko da addini cikin kwanaki uku da rasuwar mijin nata ta dawo hayyacinta kuma cikin nutsuwarta. Tana ta ansar gausuwar kowa, sai dai bata uhm bata uhm amma idan anyi mata ta'aziya zata ansa.
A ranar da akayi sadakar bakwai, an tattara komai nasu da suka mallaka an adana banki, inda aka tabbatar sai matasan sun girma tukunna za'a soma basu dukiyarsu.
Sannan Ammi ta dauki ragamar kula da Khaleel har karshen rayuwarta.

***<***


Cikin sati biyu Khaleel ya sake har ya fara sabawa da Saif, ya shiga ran Ammi kwarai dama Khaleel yaro ne mai shiga rai babu wanda zai kalle shi baice yana sonsa ba.
Bayan kyau da Allah ya bashi, ga hazaka wato hazikin yaro ne mai kwarjini hade da nutsuwa ta ban mamaki. Ammi ta dauki kaunar duniya ta dora kan marayun nan wanda take ganin amana ce Allah ya damka mata.
Yadda take kula dasu sai ya zamto sun dena ambaton babansu, Ammi da kanta ta sawo ma Khaleel kayan wasa ba iyaka wannan shine ya dauke masa hankali har ya sake ya saba da ita.


***<***


Ammi ce zaune a katon falonta tana kallon tashar zee world da remote a hannunta, Khaleel na game da wata abar game na yara, ta duba agogon da ke makale a bango tace Khaleel a je ayi sallar la'asar kafin teacher (malam) yazo, ya amsa da to a yayinda ya ja hannun Saif suka shige daki, ta bisu da kallo har cikin ranta tana jin tausayi da kaunar Khaleel. Itama tashi tayi ta dauro alwalla ta fara sallarta.


***>***

Khaleel yaro ne mai hazaka fiye da tunanin DAN ADAM, tun yana karaminsa  yanada wasu bawa da Allah ya bashi da dama, ga kyau ga kyan hali, ga nutsuwa da rashin son wasa a makaranta, ta ko ina Khaleel abin alfahari ne ga iyayensa.
Rashin iyayensa da yayi ko sau daya ba ta6a sanin wani abu ba wai shi maraici tunda ya dawo hannun Ammi, tsaye take kansa farin cikinsa hade da walwalarsa.
Ga shi da shegen wayau ga tambayar tsiya, duk sanda yayi tambaya aka aunata za'a ga hankali da tunaninsa har akanyi mamakin yadda akayi yayi wannan tambayar. Akwai ranar da ya tambaye Ammi meyasa bata haifo masa yar kanwa ba, duk da tasan a lokacin tana da ciki don kuwa mijinta Abdul'aziz da ciki na kimanin wata daya ya mutu ya barta. Ta kanyi murmushi kurum tace
"Allah ne mai badawa Khaleel"
Aikuwa tun daga wannan ranar Khaleel bai kara fashin yi mata addu'ar Allah yasa a haifa masa yar kanwa.




MSB✍🏼

No comments: