Sunday, 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 31 to 35

TAGWAYE NE? Na Maryam s bello {31 to 35}
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

This page is dedicated to my sisters Bilkisu Ammani (Chuchu), Maryam Gafai, Asma'u Isa, Asma'u Mashasha, Asma'u Ammani, Hafsat Kabir, and Meesha luv thanks for the support ILYSM❤️😘

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

31

Tabbas Alhaji Ahmad ya ba Abba mamaki zaune yake a falo kan kujerar zaman mutum uku, kallo daya zakayi masa ka tabbatar da damuwar da ta mamaye saman fuskar tasa, sai yanzu ma ya soma tunanin chanzawar abokin nasa tun bayan dawowarsa daga turai, ya soma tunanin dalilin da ya hanashi zuwa duba shi a lokacin da bashi lafiya, ya tunano da irin rayuwar da sukayi a baya, wanda ya zamto damuwar daya ta dayan ce. Kuma shi ya tabbatar da cewar ya ga sakon nasa da ya tabbatar da ya aika masa ta waya. Ya numfasa tare da cire gilashin idanunsa, tabbas zumuncin zamani yanada rauni... Sallamar Adnan ce ta katse masa tunani, ya juyo da dubansa ga dansa tare da amsa sallamar. Adnan ya karaso ciki ya zauna kusa da Abban nasa, bayan ya gaishe sa, Abba ya amsa yana mai duban dannasa cike da tausayawa, tukunna ya numfasa ya soma magana.

"Adnan?"

Ya dago da fuskarsa yana mai duban Abban tukunna ya amsa.

"Na'am Abba"

Abba yana dubansa da kyau yace.

"Adnan, kaga yadda lamari ya juye ko? To abinda nake so da kai ka dauki komai a bisa kaddara daga Allah, wanda babu wanda ya isa ya kaucewa tasa kaddarar, ba dubara ta bace, ba kuma iko na bane, kar kace zakayi fushi dan kaga hakan ta faru da kai, ina so ka dauki komai a matsayin hukunci daga Rabbil izzatu, ala kulli halin ana so mutum ya kasance mai neman za6in Allah, ina so ka dauki Khadija a matsayin wadda Allah ya za6a maka, kar kaga an baka da ita haka nan ba tare da an shawarce ka ba kace zaka wulaqanta ta, itama ka dauke ta kamar ko wace mai gata, saboda wani 6angare na jikina ya aminta da ita a matsayin diyata, kuma ina sa ran ganin mahaifiyarta a ko wane lokaci, ga mahaifin Fatima nan ya aiko a kwashe mata kayanta, zuwa gobe sai a zuba ma Khadija nata, ni na dauki nauyin yi mata komai, insha Allah zuwa jibi komai zai kammmala, sai a dauki matarka a baka, Allah ubangiji yayi maka albarka ya zaunar da ku lafiya, ka riqe yarinyar mutane amana Adnan"

Jikin Adnan yayi sanyi ainun, a sanyaye ya amsa tare da ba Abba tabbacin riqe ta amana. Har cikin ran Abba yaji dadi, daga haka Adnan ya saki jiki sukayi hirar su irin ta da uba, cikin hirar ne Abba ke masa batun jarabawar Khadija da zasuyi sati biyu masu zuwa, Adnan ya tabbatar masa da zatayi insha Allah. Daga haka suka miqe gaba daya don sauke farali kasancewar lokacin sallar la'asar tayi.

* * *
Duk wannan budurin Badiya bata san anayi ba, tun safe ta bar gidan a cewarta bata iya jure ganin Adnan ya auri wata tana gani, bata dawo ba sai bayan sallar isha'i kallo daya zakayi mata ka dabbatar da kukan da tayi yanayin fuskar ta ta nuna hakan, da shigar ta ta fara jiyo hayaniyar mutane a falo, gabanta ya fadi, ta dake ta qaraso ciki gami da yin sallama, daga nan ta wuce daki zuciyarta na suya.

Kan gado ta fada tare da runtse idonta gam, ta rasa me ke mata dadi a duniya, a wannan yanayin Hajiya Abu ta risketa, a hankali ta kira sunanta, Badiya ta bude idonta da suka kada zuwa ja ta miqe a sanyaye, Hajiya Abu ta zauna kusa da ita tare da dafa kafadarta.

"Badiya nayi zaton ma kinji labarin yadda lamarin ya juye"

Da sauri ta dago

"Lamari kuwa? Na me?"

"Uhm Badiya sai dai kiyi haquri amma aure da Khadija aka daura bada Fatima ba!"

Kamar saukar aradu haka taji sunan Khadija har cikin qwalwarta, ta dafe qirji tare da zaro idanu waje.

"Anty wace Khadijar?"

"Akwai wata Khadijah da kika sani ne bayan ta nan gidan?"

Badiya ta rude ta gigice.

"Khadija fa kika ce Anty? To garin yaya ya auri Khadija ina Fatimar?"

Nan Hajiya Abu ta labarta yanda akayi tun daga kiran Alhaji Ahmad har yadda Abba ya hada auren Khadija da Adnan.

In banda Innalillahi ba abinda Badiya ke fadi, tana hawaye take fadin.

"Amma duk duniya kowa yasan yadda nake qaunar Adnan amma ba'ayi min adalci ba da za'a bashi Khadija bayan gani, to wallahi tunda akayi min haka aka wargaza min farin cikina nima sai na wargaza nata, sai na hana ta jin dadin da ta hana ni, sai ta gwammace dama bata auri Adnan ba"

"Ke Badiya ki shiga hankalinki, kibi a sannu fa ke bakisan ba'a shiga tsakanin mata da miji ba? Kiyi hattara fa!"

"bazanyi ba, ke dama Anty tun tuni kika bi kika tsane ni akan nace sai Adnan, to wallahi ina nan aka bakana sai na aure shi ko ta wane hali sannan ita Khadija sai ta banbance tsakanin aya da kuma tsakuwa"

"Lallai Badiya tayi nisa kuma batajin kira, ko da yake laifin nawa ne tun farko da nake biye mata nake kuma taya ta son Adnan din, a yanzu da baniso kuma abin ya faskara" Hajiya Abu ta fadi cikin rai, tare da miqewa tsaye.

"Ki dai yi tunani Badiya, ki nemi za6in Allah ni tuni na tuba na koma ga Allah kema kizo ki tuba ki koma kan hanya madaidaiciya" tana gama fadin haka ta fice.

Badiya tayi kwafa, tana nan akan bakanta na auren Adnan!

* * *
Heenad na kan gadon asibiti bata san inda kanta yake ba, sai da ta kwashi awa takwas tukunna ta farka, Mami ke tsaye kanta tana mata sannu, ita kuwa ba abinda take fadi sai.

"Mami an daura auren ko? Na shiga uku Mami dan Allah ku kwance auren nan wallahi mutuwa zanyi idan aka kaini gidansa"

Da qyar Mami ta samu Heenad tayi shiru sai faman ajiyar zuciya takeyi. Dan dai Mami ta samu ta kwantar da hankalinta yasa tace mata ba'a daura ba, Mahaifinki ya hana.

Wani sanyin dadi ya mamaye mata zuciya, duk da tana cikin yanayi na ciwo hakan bai hanata miqewa zaune ba, zuciyarta fes wani qarfi yazo mata ta miqe tana fadin.

"Na warke Mami mu tafi gida"

Haushi Mami takeji na halin diyar tata bako kunya sai wannan jin dadi takeyi.

"Heenad meye haka? Kya yi haquri dai likitan yazo ya sallame ki ko?"

Kafin Mami ta rufe baki likitan ya shigo shida Daddy, sai da ya tabbatar ta warke kuma

Zata iya tafiya gida ya sallame ta.

Daddy ya tura aka kwaso ma Heenad kayanta kaf aka jibge su store din gidannasu. Duk wanda ya kalli Heenad yasan cikin nishadi take, cike da farin ciki ta kira Abida ta sanar mata an fasa aure, yanzu tana da dama da zata nemi masoyinta har suyi aure, saboda takaici ma Abida kasa ce mata komai tayi illa addu'ar shiriya.
* * *
Khadija an dirje ta, ta zama fara qal, dama gata fara sai fatar ta ta qara haske har wani sheqi takeyi, kyawunta ya qara bayyana, Abba da kansa ya sa aka dauketa aka je wurin siyan furnitures wai ta za6a, ita dai, bata iyawa, wai kunya sai su Bilkisu suka taya ta za6a don suna matuqar son auren da Khadija don yarinyar ta masu, nan dai suka za6ar mata masu kyau gado set biyu, da kujeru set daya masu kyau, komai ready made aka siya mata, ga tv katuwa da tv stand, ga kayan kicin, komai dai na more rayuwa an siya mata, ga kayan sawa kala kala, su english wears, costumes da kayan kwalliya na zamani, basu suka gama ba sai da daddare wajajen goman dare, a gajiye suka dawo, washe gari aka tafi jere, gaskiya Abba yayi mata gwaninta, me zatace da mutanen nan? Sai dai Allah ya saka musu da alkhairi, tana kwance saman gado ta soma tunanin kalar rayuwar da zata fuskanta, nan 6abgaren tana tunanin yadda Badiya ke qaunar Adnan, dayan 6angaren kuma yadda aka yi auren, ta numfasa sannan ta rufe idonta kafin ta bude. Haka dai tayi ta saqe saqe kafin 6arawo bacci yayi awon gaba da ita.

Maryam S belloπŸ’–
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

This page is dedicated to all members of Kiddies Friends Forever one love Allah ya barmu tare☺️❤️😍

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

32

Washe gari misalin takwas da minti sha biyar aka shirya Khadija cikin wani baqin leshi mai adon silver flowers, Ummi da kanta ta yafa mata katon gyale wanda ya rufe duk illahirin jikinta hartta fuskarta ba'a gani, ba'a abinda ake ji dakin sai sheshekar kukanta, Bilkisu ce ta jawo hannunta har falon Abba, wanda ya aiko kiranta don yi mata nasiha. Qasa ta raku6e ta zauna tana matsar qwalla. Abba ya kalle ta tukunna ya fara magana.

"Yata Khadija"

Har cikin ranta taji dadin yadda ya kirata da yata, bata dago ba kuma bata motsa ba, amma Abba ya tabbatar da tana sauraronsa.

"Khadija abinda nakeso da ke shine ki sani shi aure ba abin wasa bane, anayin aure don tabbacin zama na har abada, aure ibada ne, yi nayi bari na bari shine zaman aure, kar ki yarda kiyi sa insa da mijinki, ki zamto mace mai haquri, juriya da kuma dauriya akan zaman aure. Khadija tsafta, ladabi, byayya sune ginshiqin zaman aure, kar ki zamto mace mai raina mijinta, kar ki zamto macen da bata ganin mijinta da daraja, kisani aljannarki tana tafin qafar mijinki har sai ya daga sannan ki wuce, saboda haka ki dage da kyautatawa mijinki ya kasance yana mai alfahari da ke kinji Khadija Allah yayi miki albarka ya bayyana miki da mahaifiyarki, Allah ya baku zaman lafiya"

Sautin kukanta ya qaru, su Bilkisu dake tsaye bakin qofa suma kukan sukeyi don jin Khadija sukeyi tamkar yar uwarsu.

Abba ya numfasa sannan ya kalli matansa Ummi da kuma Hajiya Abu yace.

"Kuna da abinda zaku ce da yar taku?"

Ummi tayi murmushi

"Duk abinda zamu ce ka riga ka fada Alhaji, fatan mu Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyiba"

Suka amsa da amin

Hajiya tace.

"Haka ne"

Abba ya cigaba

"Shikenan ki tashi a kaiki gidan mijinki Allah ya bada zaman lafiya"

Su Asma'u suka kamo ta tana kuka suna kuka ba kamar Bilkisu da tafi kowa yin kuka. Nan su Ummi sukayi mata addu'a sosai sannan aka sa ta mota sai gidan Adnan lol.
Bayan sun isa wata Hajiya Jamila sister Ummi ce (maman Adnan) ta kamo hannun Khadija bayan sun isa kofa tasa Khadija ta shiga da qafar dama tare da yin bismillah, haka aka wuce da ita dakinta da ya qawatu da kayan more rayuwa kamar ko wace mai gata, gefen gado aka zaunar da ita tana cigaba da matsar qwalla, kafin su Hajiya Jamila su tafi sai da suka qara yi mata nasiha akan zaman aure, su Bilkisu sai zolayarta suke, haka suka tafi suka barta cike da kewar juna.
Tana nan har qarfe goman dare bata bar kukan ba, ga kanta dake barazanar yi mata ciwo a dalilin kukan da taci, kwance take kan filo hawaye kawai ke zuba daga idanunta.

Qarfe goma da rabi ya shigo dauke da baqar leda, a lokacin har ta soma bacci, qarar ta6a qofa ya farkar da ita, ta miqe da sauri tare da ja baya har tana danganewa da gado tana kallonsa a tsorace kamar wacce taga dodo. Sai dai ta kasa dauke idanunta daga kansa yadda yayi kyau cikin shadda ruwan hoda yayi kyau har ya gaji. Ga wani irin kwarjini da Allah ya zuba masa (uhm bari dai inyi shiru haka nan)

Gefen gadon ya zauna yana mai kallonta, ta basa tausayi matuqa, ya sassauta murya sannan yace.

"Zo kici abinci nasan kina jin yunwa"

Shiru tayi gabanta sai dukan tara tara yake.

Ganin bata sauko ba yasa ya qara cewa

"Kizo kici abinci mana ya za'ayi ki kwana da yunwa"

Cikin rinnaniyar muryarta data dakushe tace

"Na qoshi"

Tabbas yasan qarya take kawai dai ta fada ne.

Saboda haka sai ya daure fuska yace

"Kinsan dai bazai yiwu ba abani amanarki sannan na barki ki da yunwa ko?

kinga sakko kici abinci mana" yayi stating in a serious tone.

Ganin ba alamun wasa a tattare da shi ya sanya ta sakko, ta ci kazar kadan tasha ruwa, daga haka ya kwashe kayan ya kai fridge ya fada dakinsa. Bayi ya shiga yayi wanka da ruwa masu zafi sosai sannan ya fito ya shafa mai ya sanya doguwar jallabiya mai ratsin fari da blue.
Itama Khadija a nata 6angaren wanka tayi ta dauko kayan baccin da Ummi ta siya mata cikin kayyakinta mai dan dama dama dark pink riga da wando na cotton rigar batada dogon hannu amma ta kai cinyarta, sai wandon har qasa, ta dauko dan karamin gyale ta daura saman kanta sannan ta kwanta can gefen gado, taja bargo ta rufe har kanta, ba'a dauki lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita daman kanta ke ciwo.
Adnan na gama kimtsawa ya zauna bakin gadon dakinsa yana nazari tare da addu'ar Allah ya bashi ikon kyautata mata. Minti biyu ya fito ya nufin dakin da Khadija take koda ya shiga ya iske tayi bacci shima kwanciya yayi yana mai fuskantarta, ba'a dau lokaci ba bacci yayi gaba dashi.
Da asuba Khadija ta riga tashi domin data duba agogo qarfe hudu da rabi ta nuna, qarar ruwa ya farkar da Adnan, shima bayi ya shiga yayi alwalla ya wuce masallaci.

Khadija bata tashi daga kan sallaya ba har sai da gari ya fara haske, sannan ta miqe ta fada bayi tayi wanka, ta fito daure da towel, ta shafa mai ta taje dogon gashinta, sannan ta dauko wata rigar yar kanti doguwar riga ja ce ta dan kama ta, kasancewar lokacin sanyi yasa ta dauko rigar sanyinta ta sanya ta daura dankwalin rigar sannan ta sanya yan kunnen kalar kayanta marasa nauyi. Tana kammala ta gyara dakin tas, tana shirin fitowa Adnan ya shigo dakin, gaishe shi tayi ya amsa fuska sake sanann ya ce ta sako su karya bata musa ba illa bayanshi da tabi.

* * *
Heenad na kwance saman gadonta tana latse latsen wayarta, ta shiga nan ta fita nan, har ta kai ga shiga instagram tana duba pictures, cikin dm ne ta kaga new message ta bude, sunan ta gani ansa "Khaleel__Ibrahim" "salam" tagani, tayi tsaki ta amsa da "Wslm" sannan ta fita, ba'a dauki lokaci ba ya dawo mata da reply.

"Hey beautiful, nikam kin min kama da wata matar friend dina but naga ba ke bace i think kama ce kawai"

Ta karanta bata masa reply ba kawai ta share sa ta cigaba da abinda takeyi.

Haka dai kullum sai Khalil ya turo mata da message tun tana ignoring har ta fara masa guntun reply, misali yace mata salam, zatace wslm, ko kuma idan yace ya kike tace lfy. Haka dai kullum har dai daga qarshe yayi following nata batayi following back ba.

The next day taga abinda ya razanata wato tana shiga instagram ta ci karo da hoton Adnan a cikin explore, da da farko bata gane ba sai da ta tabbatar da sunansa ne tayi clicking over 80 comments, daga masu cewa nice pic sai masu yaba kyawunsa, gabanta ya yanke ya fadi tana shawarar ta tura masa messg ta ci karo da comment na wata budurwa tana fadin.

"Haba Adnan meye duniya ashe kayi aure ko ka sanar dani, well ya amarya Allah ya bada xaman lfy"

Wani irin yanayi ta shiga da bazata iya misalta shi ba, hannunta na shaking zuciyarta na harbawa, ta fasa wani iriin ihu sanann ta zube kan gadon tana kuka kamar wacce aka aiko ma da saqon mutuwa.
Maryam S belloπŸ’–

πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

This page is in honor of all the members of MU SHA KARATU, KHALEESAT HAIYDAR NOVELS, RASH KARDAM NOVELS 1, HAUSA NOVELS NA CHUCHU, HAUSA NOVELS NA XARAH MUH'D AND LASTLY DANDALIN MEESHA LURV✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

33

A wannan yanayin Mami ta risketa hankali tashe tayi zaton ma wani mummunan abin ya same ta, dagon kanta tayi ta shiga lallashinta, sai da ta tsagaita da kukan da takeyi tukunna Mami ta shiga tambayarta abinda ya sameta.

Tana sheshekar kuka ta ce.

"Na shiga uku Mami, ashe wanda nake qauna na kuma fasa aure saboda shi har na nemi na tozarta ku saboda shi, ashe aure yayi, na shiga uku Mami, yanzu ya zanyi ina zan saka raina, yayi aurensa ya barni Mami" ta kuma fashewa da wani kukan.

Haushi ya turniqe Mami taja tsaki tana fadin.

"Lallai Fatima na qara tabbatar da bakida hankali, wallahi Heenad tun wuri ki nutsu ki shiga hankalinki, in banda hauka ta yaya zaki bari har zuciyarki ta kamu da son wani wanda baki sani ba? A dalilinki na qin amincewa da aurennan kika tozarta abokin mahaifinki ya gama tara jama'a kika sa babanki ya watsa masa qasa a idanu, shi kuma mahaifinki harda biye miki wai a fasa auren, wallahi da ba ke kadai na haifa ba da tuni zan bada yar uwarki a aura masa kuma na tabbatar da zata amince bazata musa min ba"

 Mami tayi shiru, tayi murmushin da yafi kuka ciwo sannan ta cigaba.

"Fatima da ace mun isa da ke da duk za6in da mukayi miki zaki amsa da hannu bibbiyu, inaji da baki fuskanci wannan yanayin da kike ciki ba, kinsan muhimmancin iyaye kuwa? Wallahi da kin auri mutumin nan Allah kadai yasan yadda rayuwarki zatayi haske, yanzu da Allah ya tashi kama ki gashi nan shi wanda kike hauka akansa yayi aure wanda in zaki yanka sa baisan da wata Fatima a duniya ba har yasan kina sonsa. Nidai a matsayina na uwa bazan gaji da yi miki addu'ar shiriya ba, da ke wata ce wadda tasan inda ke mata ciwo da kin nutsu kin fidda miji an miki aure, amma nasan hakan bamai yiwuwa bane, sai dai ina nan ina miki addu'a ba dare ba rana akan rayuwarki ta inganta kema" jikin Heenad yayi sanyi, ta goge hawayen da ke zubo mata ta matsa kusa Mami ta rungume ta tana kuka.

"Mami na tuba ku yafe man abinda nayi muku, nasan ban kyauta muku ba amma bazan kuma ba, wallahi sharrin zuciya ne Allah ya huci zuciyarku Mami"

Mami tayi hamdala ta dago Heenad.

"Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana, ranar da Heenad zata gane kuskurenta"

Bayan fitar Mami ne saqon Khalil ya sake shigo mata ta dm, wannan karon numberta yake tambaya idan zata basa, nan ma batayi niyyar basa ba sai da yayi ta mata magiya tukunna ta basa, ba'a dauki lokaci ba yayi mata message ta whatsapp, nan ma dai kamar yadda ta saba amsawa a taqakice haka ta amsa wani lokacin ma sharewa takeyi, shikam Khalil a nasa 6angaren tun da ya dora idanu akanta yaji zuciyarsa ta aminta da ita, duk da yaga alamun batayi na'am da shi ba hakan bai hana sa cigaba da binta ba, abu daya ke damunsa duk lokacin da ga pictures dinta ba'a abinda yake gani sai fuskar Khadija, sai dai ko sau daya bai ta6a tambayarta ba ko tana da wata sister ba, sai dai kullum sonta dada qaruwa yake a cikin zuciyarsa, amma ita Heenad bawani sonsa take ba sai dai duk lokacin da ta tuno da maganar Mami sai ta kasa yi masa wulaqanci.

* * *
Badiya ce a dakinta take ta kai da kawowa, daga ganinta kasan tunani ne fal ranta, Zee ce ta shigo bako sallama tace.

"Babe..."

Shiru tayi ganin qawarta tata cikin wannan yanayin da sauri ta qarasa tare da dafa kafadunta.

"Bady....!"

Firgit Badiya ya dawo hayyacinta tare da sauke ajiyar zuciya.

Kamo tayi suka zauna kan gado sannan Zee ta shiga tambayar Badiya meyafaru.

badiya ta numfasa tana kallon qawar tata tukunna tace

"Zee kema kinsan tatsunniyar gizo bata wuce ta qoqi ma'ana dai ina tunanin hanyar da zan bi na auri Adnan"

Zee tayi murmushi ta dafa Badiya

"Dama nasan da haka, sai dai mamakin da kike bani shine, ke dai gaki kina son Adnan, sai dai shi baya sonki a haka zaki aure shi? Kina tunanin samun farin cikin da kike buri kenan?"

Badiya tayi wani shu'umin murmushi

"In banda abinki qawata, nifa ko bai soni ba yanzu tabbas nasan daga baya zai soni amma ni yanzu damuwa na shine auren Khadija da yayi tunanin hanyar da zanbi in wargaza farin cikinsu yaji ya tsane ta kinga daga nan sai insan dubarar da zanyi na ganin na mallake shi ko ba haka ba?"

Zee ta kyalkyale da dariya

"Tabbas haka ne kuma kisani Badiya ina tare da ke, kuma ina taya ki son duk abinda kike so kawo kunnenki kiji"

Badiya ta matso kusa da Zee ta miqa mata kunnenta, Zee ta rada mata wata magana wadda ni Maryam banji me suke cewa ba na yi iya kokarina amma basu bari naji ba.

Bayan Zee ta gama rada ma Badiya, cike da farin ciki Badiya ta rungume qawarta tana ihun murna.

"Lallai Zee na yarda ke dinnan sai dai a barki na gode da shawarar da kika bani kuma insha Allah nan ba da jimawa ba zan fara aikwatar da nawa shirin"

Daga haka hirar tasu ta tashi har suka fice daga gidan.

* * *
Kullum Ummi ke aiko ma su Khadija da abinci, tun Adnan bai sakin jiki da ita har ya fara dan janta da hira, gashi har sun kwana hudu da tarewa amma ba'a abinda ya ta6a shiga tsakaninsu, suna zaman lafiya daidai misali, Adnan bai ta6a wulaqantata ba ko sau daya, itama kuma tana yawan kiyaye duk wani 6acin ransa, haka ta cigaba da karatunta hankali kwance, gashi ta goge tayi fresh da ita, tayi kyau.
BAYAN SATI DAYA
Yau satin su Khadija daya da aure, yau ta kama lahadi ba makaranta, Khadija na kicin kasancewar ta fara girki, sanye take cikin wani material dinkin riga da siket background din kalar sararin samaniya (sky blue) anyi mashi adon flower orange da green, ta gama dafa kus kus da miyar da taji kaji da vegetables da kuma salad, sai ta hada zobo mai sanyi, ta kammala tana dorawa saman table aka doka sallama, ta daga kai bayan ta amsa sallamar, ta razana ganin Badiya cikin wata irin shiga ta matsatsun kaya, da tafiyar yanga ta qaraso ta zauna kan table din tana yatsina fuska. Ta kalli Khadija sama da qasa sannan ta shiga bude abincin da ta girka, ta ta6e baki.

"Ba sabonba mage an waye, wai kenan don ki burge Adnan kike wannan girkin da kwalliyar haka?"

Khadija tayi murmushi.

"Ban ta6a yin abu ba don na burge wani ba, amma kisani Adnan mijina ne idan ma nayi ne don na burge shi ay ba matsalar ki bace saboda haka idan har wurin Adnan kika zo to ya fita, saboda haka ki yo gaggawar fita"

Da mamaki Badiya ke kallon Khadija ta daga hannu tana tafi.

"Wow! What a wonderful performance, ta miqe tsaye ta taka har inda Khadija take, tukunna ta shiga zagaye ta tana hararta.

"Ina so ki bude kunnenki da kyau ki saurare ni, ai dama na gargade ki a baya, to kar ki manta da gargadin, sannan da kike cewa in fita yes zan fita amma zan dawo, bazan gaji ba har sai na wargaza farin cikinki, na sa Adnan ya kore ki tukunna zan huta, ki riqe wannan"

Duk da Khadija tana shakkar Badiya hakan bai hana ta magana ba.

"Naji kin dau alwashin wargaza farin cikina, to ki sani Allah baya bacci kuma shi ba azzalumin bawa bane, kar ki manta da wannan"

Badiya tayi wani shi'umin murmushi.

"Good girl na gode da kika san haka, ai nima nasan da haka amma kamar yadda hausawa ke cewa shi SO makaho ne baya ji sannan kuma SO kurma ne baya gani, to hakan ce ta kasance dani, nidai na fada miki kar ki yarda ki shishige ma Adnan domin yafi qarfinki"

Ta shafi gefen fiskarta tana murmushi.

"Na barki lafiya" daga haka ta fice tana dariyar mugunta.

Khadija ta sauke ajiyar zuciya tana addu'ar neman tsari daga mutum da aljan.

Maryam S belloπŸ’–
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

This page is for you dota Sumayya GireiiπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

34

Ba'a dauki tsawon lokaci ba Adnan ya dawo a lokacin Khadija ta fito daga wanka daure da tawul, koda ya dawo ya dudduba bai ganta ba sai yayi zaton ma bacci takeyi sanin halinta na son baccin rana, amma sai da ya fara zarcewa dakinsa ya watsa ruwa duk da ana sanyi amma gajiyar da ya kwaso wanka kawai yakeson yi, bayan ya fito farar riga ya sanya da baqin wando, eternity for men ya fesa kadan a jikinsa sannan ya fito ya shiga dakin Khadija a lokacin tana shafa mai, sallama yayi gami da tura qofar dakin, turus yayi bakin qofar ganin yanayin da ya risketa, bayanta yake kallo fari qal kamar balarabiya har wani yello takeyi, da dogon gashinta da ya sauko har bisa gadon bayanta, jin motsin qofa ya sanya Khadija saurin juyowa, ido biyu sukayi wanda yayi sanadiyar sa Khadija rudewa, har wata kyarma takeyi ganin yadda Adnan yake qare mata kallo, qafafuwansa kasa daukarsa sukayi jikinsa yayi sanyi qalau, ita kuma Khadija da gudu tayi cikin bayi ta rufe tana maida numfashi ta dafe zuciyarta da takejinta kamar zata hudo kirjinta, ta runtse idonta gam a lokacin da kunya ta mamaye ta.

Adnan kuwa da qyar ya lalla6a ya koma dakinsa dama ce mata zaiyi ta sauko su gaisa da abokinsa Khalil, gadonsa ya fada yana jin wani irin sabon yanayin da bai ta6a ji ba, ya miqe a sanyaye ya koma ya zauna saman kujerar dakinsa ya jingina tare da lumshe idanu, da sauri ya bude ganin surar Khadija dake masa yawo a kai,

"Ya salam! Wai meke faruwa ne?"

Ya furta a hankali a lokacin da ya saki huci mai qarfi, komawa yayi ya jingina jikin kujerar yana mai kara lumshe idanunsa.

Ita kuwa Khadija tafi minti biyu cikin bayi tana mai tsananin jin kunyar Adnan, anya zata iya sake hada idanu da shi? Nan dai tayi tsaye tana shawarar ta fito ko ya tafi, sai tayi kamar zata bude sai kuma kunya ta kama ta, ta kara minti daya tukunna ta saduda ta murda kofar bayin ta leko da kanta, ta kalli ko ina taga baya nan sannan tayi hamdala ta fito, da sauri ta fiddo wata doguwar rigar yan kanti baqa da ja ta zumbula ta sanya hijabi, ta koma kan gado ta zauna tare da dauko filo ta maqalqale kamar za'a kwace mata filon, ta runtse idanunta gam kunya duk ta mamanye ta.
Da qyar Adnan ya daidaita nutsuwarsa yayi ta maza ya fito ya koma dakin nata, tana nan zaune kan gado ta takure itada filo, jin an bude qofa ya sanya ta qara runtse idanunta gam bugunta zuciyarta sai qaruwa yake yi.

Ya zuba mata idanu, sannan yayi murmushin da baisan lokacin da ya fito ba. Da qyar ya yi magana yace mata.

"In kin gama ki fito ku gaisa da Khalil yana falo"

A hankali tace to sannan ya fita. Da qyar ta sauko kamar wadda qwai ya fashewa a jiki ta bi bayansa.

Zaune ta iske su a falo suna hira sama sama lokaci daya suna latse waya. Sallama tayi, duk suka amsa mata, ta zauna ta gaida Khalil cikin ladabi ya amsa yana murmushi hade da zolaya, amma can kasan zuciyarsa hoton Heenad kawai ke masa yawo a kai, duk da a hoto ya ta6a ganinta amma gani yake kamar har ta 6aci. Bayan sun gama gaisawa ne Adnan ya umurce su da suje su ci abinci, shida Khalil suka miqe tare amma Khadija kasa tashi tayi, don bata tunanin zata iya sake kallon Adnan bare har taci abinci tare dashi. Tana cikin maganar zucin nan ne Adnan ya dawo tare da kiran sunanata, qin dagowa tayi bare ma ta kalle shi. Shima daurewa yayi yace.

"kizo muci abinci mana Khadija"

A hankali ta amsa kanta na qasa

"Naci nawa"

Bai qara cewa komai ba ya koma wurin Khalil suka soma cin abincin tare.

A sanyaye Khadija ta miqe ta koma dakinta.

Suna tsakar cikin abincin ne Adnan ya kalli Khalil bayan ya kai loma yace.

"ya naga yau kamar cikin nishadi kake? Ko dai kayi babban kamu?"

Khalil ya fadada murmushinsa bayan ya kur6i zobo yace.

"Ka fiye zolaya Adnan to me ka gani?"

Shima murmushin yayi yace

"Ai duk wata amsa tana saman fuskarka Khalil, ni na san akwai magana a qasa sai dai kaqi fada min kawai"

Yayi tsai yana kallon Adnan cike da nishadin yadda yake jin zuciyarsa fes yace.

"Tabbas haka ne, kuma yadda muke da kai banida niyyar 6oye maka komai, ranar nan ne na hadu da wata yarinya a instagram, tunda na ganta naji ta kwanta min a raina, sai dai matsala guda daya danake fuskanta shine taqi sakin jiki dani, amma a shirye nake da in jawo hankalinta gare ni, yanzu dai na samu ta bani number wayarta, muna gaisawa kuma idan na kirata ma tana dauka, sai nake ganin kamar ban mata ba shine kadai damuwa ta"

Adnan ya numfasa.

"Kar ka damu Khalil komai dan a hankali ne, dama dole sai a hankali zata soka, kai dai kayi ta jan ra'ayinta har ka dace, idan aka dan kwana biyu ka jaraba tambayar address din gidansu, idan ta baka kaje ni nasan idan ta ganka zata soka, babu yadda za'ayi mace ta ganka tace bakayi mata ba"

Adnan ya qarasa yana kashe mai ido.

Sai kuma suka kyalkyale da dariya su duka.

Khalil yace

"Kasan wani abu, yarinyar tana kama da..."

Wayar Adnan ce ta soma ruri.

Ya kalli Khalil yace.

"Sorry please" ya dauka da sauri, minti daya ya kammala tare da miqewa tsaye.

Khalil ya kalle shi da mamaki

"Ah ya haka? Ina kuma zaka?"

Adnan cikin damuwa yace

"Wallahi yanzu doctor James ya kirani wai an kawo wani patient emergency yace inyi sauri in zo, don yana bukatar taimakon gaggawa.

Khalil ma ya miqe da sauri.

"Ba damuwa mu je tare"

Daga haka Khalil ya fita, Adnan kuwa sai da ya sanar ma Khadija zai fita tukunna ya fito da sauri suka ficce daga gidan.

* * *

BAYAN KWANA BIYU

Heenad tana kokarin sanya kayan bacci wayarta ta soma ruri, batayi yunqurin dauka ba har sai data kammala, a lokacin kuma kiran ya sake shigowa, ta dauka tare da cewa

"Hello"

Ya lumshe idanu yana jin wani abu na ratsa masa dukkan illahirin jikinsa.

Sallama yayi gami da cewa

"Ya kike?"

Lafiya lau kawai tace.

Sun dauki tsawon minti biyu Khalil na janta da hira amma amsarta daga eh, a'a sai kuma uhm. Daga qarshe ya katse hirar tasu tare da cewa.

"Heenad ina ga lokaci yayi da ya kamata ki bani dama inzo gidanku mu gana ko ya kika ce?"

Uhm kawai tace

Khalil yayi murmushi

"Bance dole yanzu ba amma duk lokacin da kika shirya ki turo mun da address din gidanku ni kuma insha Allah zaki ganni, ko da bayan duniya kike Heenad zan iya zuwa"

Murmushi kawai tayi tace to.

Daga haka yayi mata sallama tare da dadadan kalamai na tsatsan son da yake mata.

A ranar Heenad ta kwana wasiwasin tura address dinta, bayan dogon nazari ta dauko wayarta gami da tura masa.

Khalil na kwance yana tunanin yadda Heenad take a zahiri wayarsa tayi qarar shigowar saqo.

Ya dauka ganin Heenad ya sa shi saurin budewa har yana kyarma.

Murmushi yayi mai nuni da tsatsan farin cikin da yake ciki, bazai iya kwatanta yadda yakeji a zuciyarsa ba.

Reply ya tura mata da sauri.

"Nagode cutie! Thank you so much, sai kin ganni insha Allah"

A ranar Khalil haka ya kwana mafarkin Heenad har garin Allah ya waye.

Maryam S belloπŸ’–

πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

35

Washe gari bayan Heenad ta tashi daga bacci wajajen qarfe takwas na safe ta fito a lokacin Mami na kicin tana hada ma Daddy kalaci, ta shigo ta gaida Mami, Mamin ta amsa tana mai murmushi, Heenad ta kama mata, bayan sun kammala ne Mami ta ga kamar Heenad nasan ta fada mata wata magana don haka sai ta kamo hannunta suka zauna falo kan kujera. Mami ce ta soma magana.

"Fatima meya ke damunki ne naga kamar da magana a bakinki"

Heenad ta sosa kai, ba tare da ce uffan ba.

Mami ta sake magana cike da damuwa

"Fatima idan har da magana a bakinki ki fada min mana, idan baki fada man ba wa kike dashi da zaki fada masa?"

Sai a sannan Heenad ta soma magana tana inda inda.

"Mami.... Mami, da...ma wani Kha...lil ne ya ganni yana sona shine yace in bashi dama ya...zo wurina"

Mami ta fadada murmushinta.

"Allah sarki dama wannan ne yasa kike 6oye min? To ai babu damuwa ki bashi dama yazo mana, burin ko wane iyaye su aurar da yayansu, idan har yazo aka bincika akaga na gari ne kinga ba shikenan ba?"

Heenad ta dan daure fuska idanunta suka ciko da qwalla ta sadda kanta qasa tana wasa da yatsunta.

Mami ta dafa kafadunta.

"Fatima ina so ki sani ita rayuwa ba kullum bane mutum yake samun abinda yake so, zakiga abinda kike son ba alheri bane, sai kiga Allah ya chanza miki da mafi alheri, kar kibi son zuciyarki kice sai abinda zuciyarki keso dole zaki samu, ki nemi za6in Allah shine za6i kinji ko?"

Heenad ta gyada kai, a lokacin da wasu hawayen sukayi nasarar sakowa, da sauri tasa hannunta ta share.

Mami ta kalle ta cike da tausayi tace

"Tashi kije ki karya bari naje na sanar da mahaifinki"

To tace sannan ta miqe jiki a sanyaye.
Daddy na kan gado yana danne danne a laptop Mami ta shigo da sallama, dakatawa yayi ya dago da dubansa gareta gami da amsawa. Zama tayi gefensa tace.

"Ga kalacinka can an gama, amma inaso muyi wata magana da kai sai dai bansani ba ko sai ka karya tukunna?"

Ya maido hankalinsa gareta tare da tashi zaune yace.

"A'a ba dole sai na karya ba wace irin magana ce ina jinki"

Ta sauke ajiyar zuciya tana dubansa.

"Heenad ce ke sanar dani tayi sabon saurayi yace yana sonta da aure, wai anjima ma zaizo su gana..."

Da sauri Daddy ya katse ta

"Ina fatan dai bake kika takura ta ba da zancen aure?"

Da mamaki Mami tace

"Haba Alhaji nima yanzunnan take sanar dani..."

Ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu

"To ya isa haka, ai nasan halinki ne sheyasa ki kira min Heenad din inji daga bakinta tukunna zan yarda"

Mami ta qule

"Wato ita bazai yarda da ita ba har sai ya tambayi shawarar diyarsu" a cikin ranta take zancen.

Ta daure dai ta miqe, Heenad na tsakar karyawa Mami ta kira ta, bata musa ba ta miqe tabi bayanta.

A tare suka shigo dakin, Mami ta zauna inda ta tashi Heenad kuma ta zauna qasa kusa da Mamin.

Daddy ya kalli Heenad yace.

"Yar baba yanzu nike jin wani sabon zance daga wurin mahaifiyarki na cewar zakiyi baqo anjima haka ne?"

Heenad ta gyada tace

"Eh"

Daddy yayi murmushi

"To shikenan, duk abinda kike so ina taya ki sonsa, idan yazo kuka gana ki turo min shi inyi magana dashi, kinsan ance idan yaro zaizo wurin diyarka to ya nemi izinin iyayenta, kinga idan yazo duk wasu tamboyin da ya dace zan masa, tashi kije Allah yayi miki albarka"

"Amin" tace tukunna ta miqe ta fice daga dakin.

Mami ta kalli Alhaji

"Yanzu ai ka gamsu ko?"

"Eh na gamsu mana" ya fada a lokacin da ya miqe tsaye.

"Muje mu karya mana"

Bata ce komai ba illa bayansa da ta bi.

* * *

Tun qarfe bakwai na dare Khalil ya kira Heenad yace mata da anyi sallar isha'i zaizo. Mami ta taimaka mata ta shirya cikin wata purple atamfa dinkin riga da skirt, Mami da kanta ta daura mata dankwali, tasa mata dan kunne da sarqa kalar kayanta, Mami tace ta gyara fuskarta.

Heenad ta kalli Mami tace

"Gaskiya Mami kwalliyar nan tayi yawa, yau fa zai fara zuwa kar yaga kamar na zaqe"

Dariya Mami tayi

"Kefa bakida wayau, ina yawa a wannan kwalliyar? Da Allah ni ki shafa ko yar hoda ce"

Heenad na zum6uro baki ta murza hota, Mami ta dauko mata gyalen da ya shiga da kayanta ta miqa mata, ta fesa turare masu sanyin qamshi, bayan sun kammala Mami ta kalli Heenad.

"Kinyi kyau Fatima, ga snacks da drinks can nayi muku order idan yazo sai ki kai masa, dan Allah kar ki masa wulaqanci kinji yar albarka?"

Sai Heenad ta tsinci kanta ta son bin shawara Mami ko ba komai ta faranta mata rai.

Minti biyu tsakani Khalil ya kirata ta daga, kafin tayi wata magana Khalil yayi saurin cewa.

"Cutie gani na iso fa ina kofar gida"

Uhm kawai tace sannan ta kuma cewa,

"Ka yi ma guards magana kace wurina kazo zasu rako ka har falo"

Cike da murna da zakwadi ya fito daga motar, yayi yanda tace masa, yayi sa'a sun yarda dashi, har falon baqi aka rako Khalil, sannan guard din ya kira ta a waya ya sanar mata baqonta na falo.

Mami ta sanar mawa zataje gashi nan ya zo. Mami tasa mata albarka sosai.
Tun daga bakin qofa ta jiyo qamshin turarensa, ta shiga gami da yin sallama.

Tunda ta qaraso Khaleel ke kallonta tun daga sama har qasa, kyawunta yake ayyanawa a ransa, sai dai bugun zuciyarsa ya qaru ne a lokacin da ya hango Khadija a tattare da Heenad, shikam wannan kama tayi yawa ko tagwaye ne sai haka.

Muryarta mai sanyi yaji ta ce

"Ina wuni?"

Sak muryar Khadija wannan abu da daure kai yake.

Ya daure dai suka gaisa sosai, suka dan yi hira sama sama duk jikin Khalil ya mace, daga qarshe ya kasa haquri yace.

"Wai nikam in tambaye ki?"

Ta gyada kai

"Allah yasa na sani"

"Wai kina da yar uwa ne?"

Khadija ta girgiza kai alamun a'a

"Banida kowa ni kadai ce wurin iyaye na, da mu biyu ne amma ta rasu tunda aka haife ta koma wani abin ne?"

Ya jinjina kai, to indai haka ne kamar tayi yawa ainun.

"A'a babu komai kawai kina min kama da wata ne"

Murmushi tayi tace

"Ok"

Sun dan ta6a hira kadan inda duk cikin hirar Khalil ke magana, ita kuwa Heenad daga uhm, a'a da kuma eh, shidai Khalil ya bayyana mata sonta da yake da aure kuma baya son a dauki lokaci mai tsawo.

Heenad kuwa a nata 6angaren babu ko digon sonsa acikin zuciyarta haka zalika kuma bataji ta tsane sa ba, duk da Khalil bayada wata makusa a tattare da shi, fari ne dogo, yana da kyawunsa daidai misali.

A lokacin ne Hauwa ta shigo dauke faranti a hannunta, ta gaishe su bayan ta ajiye tukunna ta sanar da Heenad Daddy na son ganinta.

To tace bayan ta kalli Khalil tace

"Ina zuwa"

Ya gyda kai a lokacin da GUGUWAR SOnta tayi awon gaba dashi. Bayan ta fita ya lumshe idanunsa kafin ya bude, yana ayyana kyanta na zahiri dana hoto, ashe tafi kyau a fili? Ya fada cikin rai, a lokacin ne kuma Heenad ta dawo tace.

"Daddy na son ganinka"

Bai musa ba illa tashi da yayi yabi bayanta"

Maryam S belloπŸ’–

No comments: