Sunday, 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 41

πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤
    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ
        πŸ’šπŸ’™
            πŸ’™


MSBπŸ’–


maryamsbellowo.wordpress.com



*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*



41



Badiya ta furzar da iska ta tako, taku na qasaita ta iso dab da Heenad, Heenad ta hade hannuwanta wuri daya as in tayi crossing hannyenta sannan ta daure fuska tana kallon Badiya ido cikin ido alamun bata tsoronta. Badiya tayi wata shu'umar dariya tukunna ta dora.
"Aikin banza kawai! Wai shin ma in tambaye ki ita Khadijar batada baki ne? Sai kece zaki na shigar mata fada, bazata birgeni ba sai na ga ta qwatar ma kanta yanci ba, kuma mu zuba nida ku zamu ga wanda zaiyi nasara tsakanimu, sannan magana ta gaba, ki sani ke ba Khadija bace no matter what, kama ne kawai ku keyi amma ko wane cikin ku daban yake, sannan magana ta qarshe na miki alqawarin auren Adnan sannan na kori Khadija daga gidan na zauna ni kadai"
Heenad tayi shewa tace
"Aikin banza aikin wofi harara a duhu, kalle ki da Allah da wani qazamin jikinki kike iqirarin auren dan gayu kamar Adnan, ke kanki kinsan yafi qarfinki wallahi, sannan kina tunanin shi daqiqi ne da zai aure ki haka kawai ba sonki yake ba? Haha no way yarinya kinyi qarya, sannan kisa ma ranki ni Heenad ta nuna kanta na miki katanga da gidannan har abada baki ba auren Adnan wala boka wala malam basu isa su sa ki auren Adnan ba kije ki gama haukan ki, kiyi ka gama shashasha marar aikin yi..."
"Kar ki qara ce min shashasha, gaki nan babbar shashasha marar hankali ma kuwa..."
Kafin ta qarasa Heenad ta wanke ta da lafiyayyen marin da sai da taji dif na daqiqai. Tana shirin qara kai mata wani marin Khadija tayi saurin riqe mata hannu.
"Qyale ta haka nan Heenad bana son tashin hankali"
A fusace Heenad ta jiyo tana kallon Khadija
"Wallahi Khadija idan zaki zage ki qwatar ma kanki yanci ki dage, wannan sanyin naki shi ya janyo miki har wannan ballagazar ta raina ki"
Badiya ta dawo daidai dafe da kunci
"Kika mare ni?" Ta fada a fusace
Heenad tayi saurin cewa
"Wacece ke da baza'a mare ki ba? Kadan kika gani ma wallahi, ina gargadin ki tun wuri ki shiga hankalinki don bakisan halina ba banida mutunci da kike ganina nan" Heenad ta qarasa tana huci.
Badiya ta dauki jakarta da ta watse qasa da wayarta da murfin ya 6alle ta tattara ta dago tana kallon Khadija.
"Zan dawo ne bari wannan marar kunyar ta tafi"
Heenad ta qyalqyale da dariya.
"Ko yaushe kika dawo Khadija zata bani labari kuma zan biki har gidanku naci mutuncinki"
Badiya bata kuma cewa komai ba ta bar gidan don ita yanzu ta fara tsorata da Heenad.

Bayan fitarta Khadija ta kalli Heenad cike da damuwa tace.
"Heenad don Allah ki bar biye mata kuna tashin hankali haka babu dadi  bakisan halinta ba ne, batada zuciya dawowa zata kuma yi fa"
Heenad tayi murmushinta mai kyau ta kamo hannun Khadija suka zauna kan doguwar kujera suna fuskantar juna.
Heenad ta kama hannun Khadija cikin nata tana murmushi.
"Sister kinsan Allah? Ki dena mata sanyi sheyasa take miki haka, kar ki qara nuna kina tsoronta ki dage kici mutuncinta dole ta qyale ki wallahi"
Khadija ta girgiza
"To meye ribar hakan?"
Heenad tace
"Mts akwai riba babba ma kuwa na farko zata qyale ki na biyu dole ne ta fara tsoronki wallahi sister ki dena mata sanyi just promise me zaki qwatar ma kanki yanci"
Khadija tace
"To amma Heenad...."
Heenad ta daga mata hannu
"Just promise"
Khadija tayi murmushi
"Shikenan na yarda"
Haka suka wuni ranar, daga kallo sai hira, har dare ya tsala.


* * *

Washe gari Heenad ta kai Khadija salon aka gyara mata gashinta ya qara baqi sai sheqi yake, sannan aka tsantsara mata jan lalle a hannu da qafa, daga salon wani shop suka je Heenad ta kwaso mata turaruka da man gyara fata mai sa laushi, ta kwaso mata english wears kala kala.
Basu suka dawo ba sai bayan la'asar bayan sunyi sallah suka ci abinci, nan Heenad ta hau koya ma Khadija yadda zatayi amfani da mayyukannan, harda su scrub, duk ta koya mata, sannan ta koya mata sanya kaya da iya kwalliya, wata riga da wando ta dauko mata cikin kayan da suka siyo, baqin dogon wando matsate (skin tight) da wata top iya cinya kalar pink mai siririn hannu, Heenad na murmushi tace.
"Kinga wannan sister?"
Ta nuna mata
"Su zaki saka ranar da Adnan zai dawo, idan kika saka ki gyara gashinki kar kisa dankwali ko gyale, bari dai zan koya miki"
Khadija ta sadda kanta qasa
"Anya zan iya yin haka kuwa?"
Heenad ta harare ta da wasa
"Kefa banza ce wallahi, dan ma kin samu na baki masu dama dama? Da wadancan nace ki saka fa?" Ta fada tana nuna mata sauran kayan da ke baje kan gado.
"Wayancan ma sakawa zakiyi a hankali kar ki qara burguza wannan hijabi nidai don Allah Khadija"
Ta kuma jawo hannunta gaban madubi ta zaunar da ita kan stool suna fuskantar madubin. Heenad ta zagayo ta gabanta ta koya mata kwalliya amma bamai yawa ba, sai data tabbatar da ta iya sannan ta kyale ta"
Bayan sun gyara dakin, kicin suka koma Heenad ta soma koya ma Khadija girkin zamani tana yi tana zolayarta wai bata iya komai ba sai shinkafa da taliya. Nan suka yi ta dariya gwanin sha'awa.
Duk iskancin Heenad Mami ta koya mata girki kala kala don Mami bata wasa da wannan fannin, tun Heenad bata so har ta saki jiki ta koyi abubuwa.


* * *


Washe garin ranar da Adnan zai dawo tunda safe Heenad ta tashe Khadija, suka gyara gidan tas, suka baza turaren wuta masu sanyaya zuciya, suka kunna duka ac din gidan, Heenad ta fesa freshner, sannan suka dunguma kicin, abinci kala kala sukayi masa masu dadi, da drinks homemade don Khadija ta kula Adnan yafi son homemade drinks. Nan ma kala kusan uku suka hada masa, suka jera komai kan dinning. Sannan suka sa drinks din a firij, bayan sun kammala komai suka kara jona turaren wuta.

Qarfe uku saura kwata Adnan yayi mata text kan cewa ya kusa isowa, gabanta ya hau dukan tara tara.
Heenad ta sa tayi wanka ta shiirya cikin wannan kayan riga da wando, ta gyara mata gashinta ya bazo kan bayanta, batayi mata kwalliya ba saboda tafi kyau ba kwalliya, ta feshe mata jikinta da turaruka masu qamshin dadi, koda suka kammala Heenad ta kalli Khadija baki galala tace
"Wow sister! Kinganki kuwa? Nasan yau idan Adnan ya ganki hmm"! Ta qarasa tana kashe mata idanu, Khadija ta dake ta da wasa tana hararta.
Kafin Heenad ta tafi sai da ta qara koya mata zaman aure kamar yadda Mami take koya mata, sukayi bankwana kamar kar su rabu.

Bayan tafiyarta da kamar minti hamsin taji qarar shigowar mota, gabanta ya tsananta bugu, tayi ta karanta innalillahi a ranta, qofar a kulle take shiyasa taji ana qwanqwasawa. Ta miqe jiki ba qwari ta bude qofar, daga bakin qofa Adnan ya saki baki yana kallonta, ko gezau, tunda yake bai ta6a ganinta haka ba, ta daure ta saki murmushi mai taushi tukunna tace.
"Sannu da hanya" ta kar6i jakar da ke hannunsa ta matsa alamun ya shigo. Jiki ba qwari ya shigo yayi tsaye bakin qofa a yayin da yake cigaba da kallonta.
Tana shirin tafiya ya riqo mata hannunta gam sannan ya kirata da wata irin murya da baisan yana da ita ba.
"Khadija!"
Har tsakiyar kanta a yayinda ta runtse idanunta gam gabanta ya bada dam!
A hankali ta jiyo amma bata dago ba kanta na qasa.
Kallonta yake a yayinda da zuciyarsa ke harbawa, ya daure ya ce.
"Khadija...."
Ta dago ba shiri idanunta suka kai cikin nasa idanun a yayinda shima ita yake kallo, haka sukayi tsaye suna kallon juna ido cikin ido!



Kuyi manage da wannan ba yawaπŸ˜˜πŸ˜…


Maryam S belloπŸ’–

No comments: