ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
maryamsbellowo.wordpress.com
*πTagwaye ne? π*
48
Da kanshi ya hada mata ruwa wanka, ya tsugunna daidai gwiwowinta ya cire mata kayan da ke jikinta sannan yaja hannunta har toilet.
Sai da ya tabbatar ta shiga kwamin sannan ya wuce kicin da kansa ya bude oven kaji ne manya guda biyu wadanda ta gasa ga wani ruwa ruwa (romo) na fita a jikinsu, yaji albasa da tumatir harda dan tarugu. Sai ya jawo shi gaba daya ya dora kan tire hade da dauko wuqa, ya bude firij ya dauko fresh milk da juice mai sanyi da ruwa da wani salad mai dadi ya wuce daki dasu.
Ya iske har ta fito tayi shafa'i da wuturi amma bata 'daga ba daga kan sallayar ba, ya aje gabanta, ta dago ta dube shi da idanunta da suka koma kanana saboda kuka, taji tausayinsa duk ya kama ta, a hankali ta furta "Sannu da kokari"
Sai yayi murmushi kawai yana tsiyaya lemon grapes cikin kofin tangaran (glass cup) yasa mata a baki.
Kar6a tayi ta sha sosai don bata san ma tana jin yunwa haka ba, hartta naman shi ya yayyanka mata ya dinga yagowa da fork yana sa mata a baki.
Batasan sanda itama ta zage ta fara bashi a baki ba.
Sai da suka take kaza daya harda rabi, don ko wanensu bai san cewa yana jin yunwa har haka ba.
Abubuwa da yawa sun biyo baya daga ciki harda hira mai dadi da qarin fahimtar juna.
Don haka sai ta fara tunanin ashe tana son mijinta har haka sannan tana da lafiya kamar ko wane DAN ADAM, batasan hakan ba sai yau.
Har karfe hudu na asuba amma dukkansu basuyi bacci ba, ta zuba mishi idanu sai taga ya mata kwarjini, tana daga kwancen take fada masa taimakon da zai mata, hada ruwan dumi da dettol, yayi yanda tace.
Sai da ta fito wankan ta dora alwala, ya bata panadol, bayan sallar asuba sabon peji (page) Khalil ya bude mata gaba daya ya qara gigita ta.
Haka ya cigaba da shayar da ita mamaki cikin fannin qauna da soyayya daban daban, gani take duk duniya babu caring and loving husband kamar Khalil dinta.
Washe gari tun daga daki Khalil ya soma jin qamshi na tashi, ashe Heenad ce ke girke girke kala kala, fitowa yayi bakin kofar kicin yana kallonta cike da sha'awar yadda take gudanar da aikin cikin nutsuwa, daki ya koma don yin wanka don fita aiki zuciyarsa fes, bayan ta kammala kicin ta koma ta dauko kula don zubawa Goggo, taje ta kai mata karo na farko data soma shiga dakinta tun zuwanta gidan!
Ba qaramin dadi taji ba ita dama bata dauka dazafi ba, ita kawai ramar da Khalil keyi ita tafi damunta amma dama ta lura yarinyar tayi sanyi.
Ta jawo kula mai pankasu da miya tace ta diba tace
"Na qoshi"
Inna tayi musu addu'a sosai ta koma sashensu ta tarar Khalil ya gama shiryawa. Bayan sun karya ya dauko jakarshi ya rataya ya kamo matarsa yayi mata kiss a kumatu sannan ya fice.
Tayi murmushi kurum sannan ta soma tattara wurin.
* * *
Adnan na zaune falo yana kallon tashar sports, da misalin biyu na rana, amma a zahiri hankalinsa na ga matarsa wadda ta fita tun safe wurin Umma don ta kirata tace zataje neman yan uwanta wannan dalilin ne yasa ta fice har yanzu bata dawo ba.
Ya tuno da yar siririyar muryarta da kuma kunyarta wadda tafi komai qayatar da shi.
Zuwa wannan lokacin Khadija ta gama mallake zuciyar mijinta da kyawawan halayenta, biyayya, kyautatawa da kuma uwa uba soyayya.
Karfe hudu saura yaje ya dauko ta, tunda ta shiga mota take motsa bakinta. Ya kalle ta da wutsiyar ido bayan ya maida hankalinsa ga titi yace.
"Baby" (sunan da yake kiranta da shi yanzu) ta dago da idanunta ta zuba mishi sannan ta amsa.
Yace
"Akwai abinda kike 6oye min ko?"
Ta girgiza kanta da sauri
"Dama...dama..." Sai kuma tayi shiru
Yayi murmushi bayan ya girgiza kansa
"Dama me?"
Ta dan kalle shi kadan tace
"Dama so nake ka bani izini naje can kauyenmu nagaida su Inna"
Ya daure fuska "me zakiyi musu? Bayan wulakanci da Inna da yayanta sukayi miki?"
Idanunta suka kawo ruwa
"Nasani amma hallacin da sukayi min baici ace na manta dasu ba wanda duk abubuwan da suka faru rashin fahimta ne"
Ya girgiza kansa cikin gamsuwa
"Shikenan naji amma ni da kaina zan kai ki ki gaida su sai mu dawo tare"
Tayi murmushi
"Nagode dama Heenad ma tace zata raka ni shine ta tambayi mijinta kuma ya amince mata"
Yayi murmushi
"Ba matsala"
* * *
Washe gari
Tun bakwai na safe Khadija ta shirya, ta shirya musu kalaci tana tsakar jerawa Adnan ya sauko cikin shirinsa na farin yadi mai taushi da kyau, ta dan kalleshi kadan tayi murmushi, shima murmushin yayi yana kallonta kamar ya hadiye ta don so. Bayan sun kammala Khadija ta shirya cikin brown material mai adon pink flowers a jikinsa, dinkin doguwar riga, hoto ta dauka ta tura ma Heenad tace ta sanya irinsu dama Mami ta siya masu iri daya harta gyale irin na Khadija ta sanya.
Bayan sun kammala suka shirya kai tsaye Heenad suka je daukowa wanda Khalil da Adnan suka sha mamakin yadda suka fito iri daya sak sai mutum ya dage kafin ya gane su.
Shima Khalil din ya shirya yana murmushi yace shifa da shi za'a, suka kyalkyale da dariya.
Tare suka shiga wurin Goggo suka gaishe ta nan tasa musu albarka da fatan dawowa lafiya, Husna sai kallonsu take cike da sha'awa. Adnan ke tuqi Khalil na mazaunin gaba inda TAGWAYEN ke zaune baya suna ta fama surutu.
Sun kama hanya inda awa uku ce zata kaisu Rugar Ardo.
Maryam S belloπ
No comments:
Post a Comment