Sunday, 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 53

๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ❤
    ๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ
        ๐Ÿ’š๐Ÿ’™
            ๐Ÿ’™


MSB๐Ÿ’–


maryamsbellowo.wordpress.com


®๐Ÿ“TALENTED WRITER'S GROUP (TWG)✍๐Ÿป


*๐Ÿ’•Tagwaye ne? ๐Ÿ’•*


53


     FOUR MONTHS LATER! (BAYAN WATA HUDU)!


Abubuwa sun faru da yawa a cikin watanni hudun da suka gabata, ciki harda auren Badiya da angonta mai suna Usman wanda yake sonta bayan zuwan da yayi suka gana, take ya amince da aurenta, yanzu haka tana can Zaria gidan angonta Usman. Sai qawar Badiya mai suna Zainab (Zee) bayan doguwar jinyar da tayi Allah yayi mata rasuwa, rayuwa kenan Allah kasa mu cika da kyau da imani.
Bayan nan kuma Khadija sun kammala jarabawar first semester dinsu wanda a yanzu haka hutu sukeyi. A watanni hudun da suka gabata Adnan da Khalil sun koma sabon gidansu da ke cikin Maitama, flat ne guda biyu a ciki, bayan shawara da suka yanke na komawa sabon gidan nasu don karfafa zumuncin da ke tsakaninsu, haka kuwa akayi gidajen iri daya ne sak kowa da nashi kuma kowa da gate dinsa, sai dai katon gidane ko daga gidan Khalil zuwa na Adnan da yar tazara. Sai wancan tsohon gidan na Khalil ya bar ma mahaifiyarsa da yar kanwarsa Husna.
Karin daukaka da girma da ya samu shi yasa har ya kara fadada gidansa ya kara gyare musu, gidan yayi kyau sosai.

Dan cikinta dan kimanin watanni hudu harda wani abu, tayi kyau ta qara qiba da kuma haske kadan, kana kallon dan tsinin cikinta da ya soma 6ullowa. Zaune take cikin lumtsuma lumtsuman kujerun falon, hannunta daya tana riqe da guava tana gutsira a hankali, a yayinda hannunta dayan ke riqe da remote tana neman tashar da zata kalla. Sallamar Heenad ce ta katse mata kallon, sanye take cikin doguwar riga marar hannu sai ta dora karamar hijabi a kai, itama cikinta ya dan 6ullo ana ganinshi. Da murmushi ta qaraso, Khadija ko kallonta batayi ba, murmushi tayi tasan fushi take da ita. Dafa ta tayi.
"Sister, kiyi hakuri please wallahi wayar ce ke charge ni kuma ina kitchen, bangani ba sai dazun nan, kiyi hakuri kinji?"
Bata iya fushi da Heenad koda tace zatayi sam bazata iya ba, dariya tayi tace
"Shikenan ya wuce amma kar ki qara Heenad ni na dauka ma wani abin nayi miki"
Daga haka hira ta 6arke tsakaninsu kamar ba gobe, sai karfe sha biyu Heenad ta miqe tana duba agogon wayarta.
"Bari na shiga gida ban dora komai na abincin rana ba, in biyo miki idan zanje islamiyya ko bazaki je ba?"
Khadija ta kalli Heenad
"Zanje mana ki biyo mani ko kuma idan na riga ki shiryawa zan biyo miki"
"Ok sai kin shigo" tace a yayinda da take kokarin fita daga gidan. Bayan fitarta Khadija itama ta miqe tayi kitchen don dora girkin rana.

Da daddare kuwa Khalil da Adnan suka dauki matayensu, wata katuwar shopping mall sukaje wadda babu ce ke babu a ciki, haka sukayi ta jidar kayan jarirai, tun Khadija da Heenad na hanawa don sunce yayi wuri a fara siyayya yanzu, amma fir Adnan yace babu ruwanta a ciki, haka suka jido kayan jarirai duk da basu san me zasu haifa ba amma haka su Adnan suka dage suka cika ledoji tun daga kayan sawa masu tsada, har zuwa kan su pampers. Hakan yasa basu dawo da wuri ba.
Haka dai rayuwar tasu ke cigaba da tafiya cikin nasarori, da falalar ubangiji iri iri!


     BAYAN WATA BIYAR!!


Wata rana su Heenad sun dawo daga kano wata gaisuwa da akayi a 6angaren Daddy,  sun dawo yamma lis, kafafuwan Khadija sun kumbura saboda zama wuri daya, jikinta yayi tsami matuqa.
Dama su Mami motarsu daban don haka gida suka wuce kai tsaye. Ita Heenad nata kafuwan basu kumbura ba amma tana cin 'data.
Adnan ya bude  mota ya zagaya ya fito da abar sonsa. Khalil ma jawo tasa matar yayi ya rungume abarsa, suna tafe Khadija ta dan duqe alamun gajiya ya zagayo da hannayensa rungume da qugun matarsa, da qyar take tafiya ita kadai tasan nauyin da take ji.
A haka suka karasa bakin qofa.

Da daddare ma haka Khadija tayi ta fama da ciwon baya da qugu, Kwana sukayi Adnan na massaging kafafunta da suka kumbura.



Maryam S bello๐Ÿ’–

No comments: