🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
🎀🎀🎀🎀🎀🎀
🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
®TALENTED WRITER'S GROUP(TWG)✍🏻
🎀🎀🎀🎀🎀
*KHALEEL*
🎀🎀🎀🎀🎀
(An samu chanjin sunan novel daga Uncle Khaleel zuwa *KHALEEL* akan wasu dalilai, da fatan za'a yi min uzuri)
Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻
February 2017💎
PAGE
✍🏻✍🏻9&10✍🏻✍🏻
Koda shigarsa bai bi ta kanta ba, bayan ya ajiye mata jakarta a falo, dakinsa ya wuce kai tsaye, rage kayan jikinsa yayi ya fada toilet, ya sakar ma kansa shower kasancewar ana zafi sosai, bayan ya fito ya kimtsa cikin kaya marassa nauyi ya fito ya nufi dakin Ammi, kwance take tana hutawa ya shiga da sallama. Ganinsa yasa ta tashi zaune tana murmushi.
Gaishe ta yayi bayan ya zauna, ta amsa a nutse tace.
"Har ka dawo Khaleel?"
Yace
"Eh Ammi na dawo, ina gama test din ma aka kirani daga makarantar su Hanifah"
Ta dan zaro ido kadan
"Lafiya dai ko?"
Yace
"Lafiya ba lafiya ba, wai batajin dadi shine suka ce na taho da ita"
"Subhanalillahi" ta fada tana kokarin mikewa tsaye "muje na ganta"
Tana gaba yana biye da ita a baya, dakin Hanifah suka shiga, a lokacin tana kwance ta kankame filo tana kuka, da sauri suka karasa dakin, Ammi ta zauna kusa da ita tare ta tabo ta, a yayinda Khaleel ke tsaye kusa da gadonta.
"Ke lafiya meyasame ki haka?"
Cewar Ammi, Hanifah ta dan bude ido kadan ta kalli Ammi, sannan ta kalli Khaleel dake tsaye fuskarsa cike da damuwa.
"Babu" tace da sauri tare da juya musu baya, ganin haka Khaleel ya fice daga dakin don ya basu wuri, ko ince ya bata freedom tayi magana da mahaifiyarta.
Shiru tayi a yayinda Ammi ta kara jefo mata tambaya.
"Aminatu wai bakiji na ne? Nace meyasame ki?"
Cikin muryar kuka tace
"Ciki na ke ciwo"
Ammi ta dan yi shiru alamar tunani can kuma tace
"Ko dai...?"
Tayi saurin cewa eh, murmushi Ammi tayi tace
"Tashi zaune muyi magana"
Ba musu ta mike tana share hawaye.
Ammi ta soma magana.
"To Hanifah girma ya soma kama ki, na tabbatar kinsan abinda hakan ke nufi, ki nutsu Hanifah, ba ruwanki da maza, idan kika bari namijin da muharraminki ba ya kama miki koda hannu ne zaki kwashi zunubi..."
Nan dai Ammi tayi mata nasiha mai ratsa jini da zuciya, ta kuma tsoratar da ita sosai yadda zata kare kanta daga rudin shedan, sannan ta dora da koya mata yadda zatayi wanka da sauransu.
Jikinta yayi sanyi, sannan kuma kunya ta kama ta.
Ta kuma ji dadi yadda Khaleel ya fita da ta shiga uku akayi maganar nan a gabansa.
********
A kwana a tashi ga mai yawan rai yau Khaleel ya tashi da farin cikin samun admission dinsa da yayi a kasar dubai. ((American University in Dubai(AUD) Architecture)). Da yaso ya tsaya Nigeria yayi karatunsa don kula da kannensa da kuma Amminsa, amma Ammi ta dage akan yafi da yaje can yayi karatunsa zai fi samun nutsuwa.
Tunda Hanifah ta samu labari dadi kasheta, murna takeyi sosai, a dakinta tayi ta tsalle tsalle. Ta zube kan gado tana fadin
"Finally, zamu rabu da kaya Allah na gode maka"
Jikin Khaleel yayi sanyi, yaji gaba daya ya tsani tafiyar, sai dai ya zai yi? Ilimi shine jigon rayuwa.
Ana saura kwana uku ya tafi ya kira Hanifah da Saif a falo, bayan sun zauna Khaleel ya soma magana cikin nutsuwa.
"Kamar yadda kuka sani nan da kwana uku insha Allah zan tafi karatu, na tara ku a nan ne don na gargade ku musamman ke Hanifah" ya nuna ta.
"Kar kiga bana nan kice zakiyi abinda kika ga dama, wallahi kowane motsinki zai dinga dawo min a kunne, soon zaki tafi SS1, Hanifah banda wasa, ki maida hankalinki kiyi karatunki, kinsan ko na biyu kika kwaso zaki sani ne, na daya nakeso na dinga ganin kinayi, sannan banda fashin zuwa islamiyya, nasan bakya wasa ta wannan fannin, Ammi ma nasan zata kula sosai, magana ta gaba banda kula samari, samarin zamanin nan ba wanda ya kaisu iya hure ma budurwa kunne koma su lalata ta, ki kula sosai, Allah idan naji labarin kina kula ko wane saurayi sai na sa6a miki, kuma zansa Ammi ta dinga kula da hakan, ki sani karatu kikaje yi, kuma shi zaki sa gaba, kin fahimta?"
Tayi shiru
"Nace kin fahimta?!!!"
Ya fada da karfi, ba shiri tace
"Eh"
Yace yauwa saura kai Saif, don Allah Saif ka kula kaga kaine babba yanzu, kasa ido sosai akan Hanifah, kaji? Sannan kaima ka kula da karatunka banda shiririta da wasa, kaga ka kusa zana WAEC dinka, dole sai ka dage sannan zaka zamu grade masu kyau, karatu da wahala amma idan akayi hakuri sai kaga komai ya wuce"
Saif yace "Insha Allah zamu kula sosai, kaima kuma Allah ya baka sa'ar abinda kaje nema"
Har cikin ransa yaji dadi yace
"Amin Saif, kaima idan ka gama sai ka fadi makarantar da kake so kaje"
Yace "Insha Allah"
Daga haka ya sallame su, Hanifah da za'a bata dama lokacin da ta shake Khaleel ta huta wannan irin takura haka? (A ganinta amma) tunda yayanta ne, ya ta iya?
Da zai tafi ya sayi waya mai kyau sabuwa dal, yaba Ammi yace ta aje ma Hanifah, amma kar a bata sai ya bukaci hakan.
*******
Bayan tafiyar Khaleel, suna waya da Ammi da Saif sosai, amma da zarar yace aba Hanifah zata kirkiri karya tace ko kanta ke ciwo, ko ta ruga toilet tace wanka take, haka dai kullum takeyi rannan sai da Ammi tayi mata jan ido tukunna ta ansa tana ta zum6ura baki, a dakile tace "hello"
Ya lumshe idanunsa bayan ya jingina da gado yace
"Hello lil sis ya kike?"
Tace "lafiya"
Yace "good ya karatu anayi sosai ko?"
Tace "eh"
Yace "Allah ya bada sa'a"
Tace "amin"
Haka sukayi sallama yana jin wani irin nishadi yana ratsa ruhinsa, zuciyarsa da kuma 6argonsa....!
Haka kullum sai Ammi ta tilasta mata tayi waya da Khaleel ba'a son ranta ba, duk da ya fahimci bason yin magana take dashi ba, baya so yayi mata dole sai ya dinga ce ma Ammi a kyale ta zasuyi waya anjima.
MSB✍🏼
No comments:
Post a Comment