๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐
♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐
๐๐๐๐๐๐
๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️
♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐
®TALENTED WRITER'S GROUP(TWG)✍๐ป
This page is for you sister Rash Kardam, words can't describe how grateful i am for your support, Allah ya saka miki da alkhairi ya bar zumunci one love dear๐❤️
๐๐๐๐๐
*KHALEEL*
๐๐๐๐๐
Written by Maryam S bello {MSB}✍๐ป
February 2017๐
PAGE
✍๐ป✍๐ป11&12✍๐ป✍๐ป
Duk da ba kalaman soyayya ya cika Hanifah din da su ba, sai dai idan ka nutsu a cikin kalamansa zaka fahimci kwantaciyyar kauna mai sanyi da ratsa da zuciya cikin kalaman nasa. Abinka ga yarinta sam Hanifah bata fahimtar karatunsa, ita har gundurarta ma yakeyi, Ammi kallonta kawai takeyi amma ta dade da fahimtar inda Khaleel ya dosa, kawai dai bataso tayi masa shishigi tana so ta kara tabbatar da zarginta tukunna, idan har hakan ne, to ta tabbatar data fi kowa farin ciki, don ta yadda da tarbiyyar Khaleel dari bisa dari, kuma ta tabbata zai kula da Hanifah tare da dora ta kan turba ta addinin islama, duba da yadda Khaleel ya ke da riko da addini abin yana matukar burge ta, idan har baya komai tofa zata iske sa yana sauraron karatun alkur'ani mai girma a cikin wayarsa, ko kuma yana karantawa, banda sauran litattafan addinin da ya iya sosai, sheyasa take ma Hanifah kwadayin auren Khaleel, sai dai tsoranta daya kar a bijiro mata da zancen auren ta watsa musu kasa a ido.
Bayan Saif ya kammala karatunsa inda ya zabi zuwa makarantar su Khaleel, yanzu haka ya tafi inda kuma Khaleel ke shirin kammalawa.
*******
Sun shiga hutun Christmas wanda su Hanifah zasu shiga ajin karshe a secondary, sannan lokacin yaye su Khaleel yazo
A satin gaba daya Ammi bata zauna ba, shirye shiryen dawowarsa takeyi sosai, an gyara masa inda zai zauna, hartta kayan da zai sa sai da Ammi tasa aka dinka masa irin namu na hausa kala kala daga kan su yadi zuwa shadda masu kyau da tsada.
Hanifah kuwa a nata 6angaren bata da walwala, koda Ammi tace za'ayi mata visa zasu tafi graduation, sai ta hade rai tace.
"Ammi gaskiya bazani ba assignment aka bamu mai yawa, kuma dole nayi"
Ammi ta daure fuska tace
"Basai ki tafi dashi can ba kiyi?"
Kamar zatayi kuka tace
"Don Allah kiyi hakuri kawai bana son zuwa"
Ammi ta rike baki cike da mamaki tace
"Yanzu kina nufin ni kadai zan tafi, sannan aka ce miki ke kadai zan bari nan?"
Idanunta cike da hawaye tace
"Eh ai bani jin tsoro"
Ammi tace
"To baki isa ba kina jina? Tafiya dole sai kinyi, kina tunanin da dadi aje ma kowa amma banda Khaleel? Ace ba kowa a danginsa, ke kinga hakan ne daidai?"
Tayi shiru tana kumbure kumbure, Ammi tace
"Badake nake magana ba?"
Tace
"Ammi baga Saif can ba?"
Ammi tayi saurin cewa
"Saif kadai zai halarci taron? Shima aka ce miki dadin zaiji idan baiga ko dayan mu ba?"
Hanifah tace
"Amma kuma..."
Ammi ta katse ta da fadin
"Wallahi kinji dai na rantse ko? To sai kinje dama ki tashi ki fara shiri"
Daga haka Ammi ta fita zuciyarta na tafasa, wai wace irin yarinya ce haka?
Koda Ammi ta fita kuka ta fashe da shi, sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta bude wardrobe nata ta fara fito da kayanta tana hawaye tana watsa su kan gado, haka ta shirya kayanta tas cikin akwati, tana yi tana share hawaye.
*******
Saukar sassafe sukayi a Dubai International airport, Hanifah tana ta kumbure kumbure na babu gaira babu dalili tun saukarsu LA QUINTA PHASE 2, wata unguwa ce da mariganyi Alh Abdul'aziz ya siya saboda zuwa don saukaka musu sauka a hotel, makeken mansion ne.
Cikakken saurayi dan shekara ashirin da tara ya zama katon gaske, kai kace dan shekara talatin da biyar ne zuwa da shidda, yana da wata irin halitta da kalar fata mai daukar hankali tare da fizge zuciya, duk macen da tasan me takeyi to tabbas zatayi rububin Khaleel, yana da kirar namijin duniya, girman da ya kara ya basu mamaki, dogo ne sosai mai ginannen jiki, bayada kiba haka ma bayada rama, ita kanta Hanifah da ta kalle shi ji tayi ya mata kwarjini sosai, ya kuma burge ta irin wadannan mazan ne Allah ke tsamewa a cikin al'umma wanda suka hada komai na rayuwa, they are lucky gaskiya. Tace ashe dama haka yaya Khaleel keda kyau?
Ba kuma ta ta6a ganin wanda hular ilimi tayi wa kyau ba, tayi tsaye kyam a kansa ta fiddo kyansa da kwarjininsa, baka gane wane jinsa ne idan ba saninsa kayi ba, saboda yadda ya murje ya koma bature sak! Saif na gefensa yana murmushi da jin dadin ganin mahaifiyarsa da kuma kanwarsa.
Fuskar Hanifah ba yabo ba fallasa tace
"Congrats ya Khaleel"
Kwayar idonsa tayi masa nauyi kallonta yake sannan yace idanunsa a lumshe.
"Na gode sosai lil sis"
Ammi da ke tsaye tana masa kallon yadda Khaleel dinta ya chanza ya rikide lokaci, tabbas ko addu'ar miji zatayi wa Hanifah takan ce kamar Khaleel.
Can ya hango ta ta saje da yan makarantarsu suna ta hira kamar dama ta sansu, kallonta yakeyi mai cike da kauna, Allah kadai yasan dimbin soyayyar da ke dankare cikin zuciyarsa a yanzu, tun tuni da soyayyar Hanifah ya girma da ita kuma yake rayuwa, bazai ta6a iya cewa ga adadinta ba!
At 21 yana ganin kamar lokaci yayi da ya kamata yayi aure to amma wacce yake ma kauna baya jin ta isa aure, gani yake da sauran lokaci gaba daya next year za ta cika shekara goma sha shidda (16 years) da haihuwa.
Baya jin zai iya son wata a fadin duniyar nan, Hanifah ce kadai take da mulkin zuciyarsa, yar uwarsa kuma jininsa HANIFAH.
Yaga mata kala kala, jinsi kala kala amma ba wacce ya gani kuma tayi masa sama da Hanifah..."
Dafa shi yaji anyi a kafada, firgit ya dawo daga duniyar tunani.
Saif ne ke masa kallon tuhuma.
MSB✍๐ผ
No comments:
Post a Comment