๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐
♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐
๐๐๐๐๐๐
๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️
♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐♥️๐
®TALENTED WRITER'S GROUP(TWG)✍๐ป
๐๐๐๐
*UNCLE*
๐๐๐๐๐
*KHALEEL*
๐๐๐๐
Written by Maryam S bello {MSB}✍๐ป
OMG!!! Hey Everyone, I just wanted to thank all of you and to let you guys know how wonderful it feels to have friends like you that can share on my special day. Thanks!Thanks so much, my birthday just wouldn't have been the same without a special wish from you all๐๐๐
๐❤️๐And again๐❤️๐
Thanks a ton for all the lovely wishes. I really cannot believe that I am so blessed in life. Thanks everyone, believe me, it really means a lot. Thanks for all the lovely wishes. Without you, I wouldn't have enjoyed so much. Thanks a lot!๐ฉ๐๐๐๐๐๐ป๐๐ป
PAGE
✍๐ป✍๐ป5&6✍๐ป✍๐ป
A lokacin da Khaleel na aji uku a fannin primary yayinda Saif ke aji daya. Khaleel ya fara lura da cikin Ammi nata kumbura yana girma, Khaleel sarkin wayau yayi ta tunanin da ne a cikin Ammi. Aikuwa idan aka bashi kudin makaranta sai yaje ya sayi kayan jarirai yana 6oyewa.
Khaleel duk ya kosa Ammi ta haifa masa kanwa, don a nasa tunanin idan ta fito ko kuda bazai bari ya ta6a ta ba.
Ranar wata juma'a da safe nakuda ta kama Ammi, cikin dauriya Ammi ta kira direba ya kaita asibiti, kafin goma na safe Ammi ta haifo kyakkyawar jaririyarta fara sol!
Tunda aka dauko su Khaleel daga makaranta akayi asibitin dasu, da gudu suka shiga dakin da Ammi take kwance, tunda ya dauki diyar yake murna, ya rasa inda zai sa ranshi don dadi, Saif yayi juyin duniya ya hana shi dauka, haka zai zauna rungume da ita yana ta kallonta. Ammi ta kallesu tana murmushi tace.
"Shima Khaleel karfin hali yakeyi, amma ba iya dauka yayi ba bare kai Saif"
Washe gari tunda safe aka sallami Ammi, gaba daya Khaleel dashi ake zaman barka, sannan baya bari a dauke ta ya dinga kuka kenan dole a hakura aje ta.
Ranar suna aka yi mata huduba da sunan kakarta wadda ta haifi babanta wato Aminatu, amma gaba daya Khaleel ya sa kuka shi Hanifah yake so a dinga kiranta, wai shi yana son sunan da dadi, Ammi ta kanyi murmushi don bata kaunar abinda zai bata ma Khaleel rai.
Bayan suna Ammi na shayar da Hanifah Khaleel ya shigo da leda a hannunsa, yana zuwa ya baje kayan baby kan gado yana nuna ma Ammi, bakinta bude take kallonsa, ta cika da mamaki!
Kaya ne masu kyau unisex, mamaki ya ishi Ammi tace masa.
"Ina ka samo wannan kayan?"
Yace "siya nayi Ammi, idan kika bani kudin makaranta a ciki nake dauka, tun sanda naga cikinki yana kumbura, Ammi ina son babyn nan idan ta girma zaki bani ita na aura?"
Da zuciya daya yake maganarshi, har ga Allah shi iyakar gaskiyarshi kenan,kuma abinda ke zuciyarshi kenan, ta kama baki tace.
"Khaleel kenan, wa ke kai ka kana siyo kayan?"
Yace
"Aminu direba yake kaini"
Daga nan Ammi bata kara magana ba don wayon Khaleel wani lokaci har tsoro yake bata.
***<***
Tunda aka haifi Hanifah Ammi bata san kukan ta ba, Khaleel ke rainonta bil haki, idan kuwa aka yi baki ya kankame ta ya hana a dauke ta, sai Ammi ta kwantar da murya ta lallashe shi ya basu ita.
Tuni ya koyi bada feeder, chanza pampers, tsarki, rannan har cewa yayi a goya masa ita, sai ma Ammi na kwa6arsa don da kansa yake cewa zai dora ta a bayansa, gashi dai dan karami!! Khaleel kenan.
Watanta hudu da haihuwa, girman Hanifah yana bashi mamaki sosai, ta zama kamar balam balam, gata active baby mai kuzari sosai. Ga gashi yala yala a kanta, tana zama daram kamar yar wata shidda.
Haka zai zauna yayi ta kallonta yana cewa
"My baby tana da kyau"
Tanada wata shidda ta iya rarrafe sosai, ta fara sanin mutane ga bata yarda da kowa sai shi. Ita dai Ammi ta zuba ma sarautar Allah ido.
Sai da ta cika wata goma cif a lokacin tana gudunta ko ina, ga shegen 6arna, ga rashin ji, shi kuma Khaleel baya son rashin jin da takeyi, har fada yake mata idan tayi abu kamar tana jinsa.
Kowa ya kalli Hanifah sai ya kara kallonta, fara ce tas, siririya mai dogon hanci, ga idanuta farare manya masha Allah, komai nata dai yayi daidai gwargwado.
***>***
Duka suna zaune kan table suna kalaci, Hanifah ta cika bakinta da dankali ta kuma bude shi ita dole sai tayi magana aikuwa ta kware, Khaleel dake gefenta yayi saurin mika mata ruwa ta amsa ta fara kwankwada da sauri. Ya rafta mata harara yace
"Bana hana ki cin abinci haka ba? Is a bad manner"
Ta kalle shi cikin ranta tace
"Ya Khaleel ya faye takura"
Ya kalle ta yana murmushi yace
"Ko kefa haka ya kamata kina cin abinci a natse kamar mace"
Ta aje cokalin ta tashi da gudu tayi dakinta don ita sam bata kaunar yadda Khaleel
Ke takura mata.
Bai tanka ba amma har cikin ransa baya jin dadin halin Hanifah.
MSB✍๐ผ
No comments:
Post a Comment