Tagwaye ne? Na Maryam S bello {36 to 40}
ππππ❤ ππππ
ππ
π
MSBπ
*πTagwaye ne? π*
36
Da sallama ya shiga falon Abba, Heenad kam data nuna masa hanya dawowa tayi, ya shiga shi kadai, Abban na zaune saman kujera yana kallon labarai Khalil ya doka sallama, ya dago gami da rage volume bayan ya amsa sallamar, qasa Khalil ya zauna kansa sunkuye yace.
"Barka da hutawa, ina wuni?"
Daddy ya amsa gami da gyara zama.
"Lafiya lau, Alhamdulillah"
Ya danyi shiru tukunna ya cigaba.
"Khalil ko?"
Khalil ya gyada kai yana dan murmushi.
"Madallah Khalil, dazu nake jin labarinka daga wajen mahaifiyar Heenad, shin Khalil da gaske kake da aure kake son Heenad?"
Khalil ya sunkuyar da kansa alamun kunya yace
"Tabbas haka ne, da aure nakeson Heenad kuma idan ba damuwa banason a dauki lokaci mai tsawo"
Daddy yayi tsai yana nazari tukunna ya numfasa.
"Haka ne... Sai dai wani hanzari ba gudu ba, akwai jarabawar da zata fara zuwa jibi, amma ba damuwa idan ma auren za'a sanya sai asa bayan ta qare"
Khalil yace
"Babu damuwa Allah ya basu sa'a"
"Amin, in ba damuwa zan iya sanin kai dan gidan waye?"
Khalil yayi shiru na yan daqiqai tukunna ya soma magana kansa na qasa.
"Sunana Khalil, sunan mahaifina Ibrahim Garzali, mu yan garin kano ne, sai dai daga baya ne aiki ya dawo da Abbana nan garin..."
Daddy ya tari numfashi
"Kar dai dan gidan Buba Garzali ne?"
Khalil ya girgiza kai da mamaki yace
"Eh"
Daddy ya fadada murmushinsa
"Ikon Allah, ai Garzali tare mukayi secondary school dashi, tun daga nan kowa ya kama gabansa, ni dama tunda ka shigo nake ganin fuskarsa a taka, ashe ma dansa ne da kansa"
Khalil farin cikinsa ya qaru ashe bazai sha wahala sosai ba, yayi murmushi.
Daddy ya cigaba
"Allah sarki Garzali mutumin kirki, yanzu yana ina?"
Annurin fuskar Khalil ya 6ace 6at hawaye suka cika idonsa ya sadda kai
"Allah yayi masa rasuwa shekarun baya da suka gabata"
A razane Daddy ya gyara zama
"Ya subhanalillahi! Ikon Allah, Allah ya jiqansa ya gafarta masa"
Khalil ya amsa da amin
"Ashe ba rabon zamu sake ganawa Allah sarki rayuwa"
Khalil yace
"Haka ne"
A sanyaye Daddy yace
"Indai kuwa haka ne bani bukatar dogon zance ka turo magabatanka na baka Heenad Allah yasa albarka"
Cike da farin ciki Khalil ya dago, wani sanyin dadi ya ratsa zuciyarsa yace
"Nagode! Nagode Abba Allah ya qara girma"
Da murmushi saman fuskar Daddy yace
"Jeka wurin Heenad din ku qarasa"
Khalil ya miqe ya kasa 6oye farin cikinsa sai washe baki yake kamar gonar auduga.
Heenad na zaune kan kujera tana latsa waya Khalil ya dawo sai murmushi yake ya zauna yana duban abar sonsa.
Ta dago ta dube shi, shima ita din yake duba yace.
"Yau ni din mai sa'a ne, na shigo da qafar dama"
Ta dago tana dubansa tace
"Bangane ba?"
Ya fadada murmushinsa
"Daddynki ya amince da aurenmu yama ce na turo magabata na ayi magana"
Gaban Heenad ya yanke ya fadi, ta daure tayi yaqe ta sadda kanta
Khalil yayi tsai yana dubanta, da damuwa saman fuskarsa
"Heenad sai nake ganin kamar ban miki ba ko?"
Da sauri ta girgiza kanta
"Ba haka bane..."
"To yaya ne?"
"Kawai dai..." Sai kuma tayi shiru
Khalil ya kalle ta
"Ban miki ba ko?"
Da sauri tace
"Wallahi a'a ni bance ba"
Na miki kenan, ya fada yana kashe mata ido
Sai ma ya bata dariya, dariyar da tayi ne ya sanya Khalil nishadi, ya duba agogon da ke maqale a hannunsa yace
"Ni zan tafi Heenad sai kuma gani na biyu idan muna raye" ya qarasa gami da miqewa.
Itama Heenad ta miqe
"Allah ya kaimu sai da safe"
Ya dube ta da fuskar shagwa6a
"Baza'a raka ni waje ba?"
Tayi saurin girgiza kanta
"Kayi haquri kaina ke ciwo"
A razane yace
"Subhanalillah! Jeki kwanta Allah ya sauwake" duk ya daga hankalinsa ya shiga damuwa.
Daga haka sukayi bankwana zuciyar Khalil fes, a yayinda ta Heenad tata akasin haka.
Koda Khail ya koma gida sai da ya kira ta ya ji jikinnata, bayan nan ma sai da ya aika mata da saqo kala kala na Get well Soon.
* * *
Adnan da Khadija na zauna falo suna kallon wani series na india mai suna "twist of fate" aka kwankwasa qofa, Khadija har ta miqe zata bude Adnan ya dakatar da ita.
"Yi zamanki bari na bude"
Sai da ya fara cewa waye, ya jiyo muryar Badiya tana fadin
"Badiya ce"
Kamar bazai bude ba, sai kuma ya bude can qasan zuciyarsa haushinta yakeji kamar ya shaqe ta.
A razane yake kallonta, yanayin shigarta sai a hankali, irin kayan arnar nan ta sanya masu zuwa club, yayi tsaki gami da tsuke fuska.
"Ke lafiya mekike yi min a gida da daddaren nan?"
Ta fara kukan munafunci.
"Dan Allah yaya Adnan kayi haquri wallahi motata ce ta sami matsala nan kusa da ku, to naga nan ne kusa ga dare yayi sheyasa na taho nan in yaso da safe sai in koma gida?"
Ya qara tsuke fuska
"Ki bari na baki kudin mota ki koma gida mana ai kin saba yawon dare so banga abinda zai hana ki komawa gida yanzu ba"
Ta qara sautin kukanta
"Sanin kanka ne yanzu sun rufe gida ka taimaka min dan Allah"
Yayi tsaki
"Naji amma gobe da sassafe ki tabbatar da kin koma inda kika fito"
Nan ta hau murna
"Na gode sosai gobe safiya nayi zan koma gida"
Ya maida gidan ya rufe suka koma falo, gaban Khadija ya fadi tana kallon Badiya tun daga sama har qasa.
Adnan ya kalli Khadija fuska daure
"ki kaita dakinki ta kwana gobe zata koma gida"
Haushi ya kama Badiya wato sai wani cewa yake gobe zan koma gida.
To Khadija tace gami da miqewa tsaye ta haye sama, Badiya tabi bayanta tana karkada jiki tana yanga, batasan Adnan ko kallonta baiyi ba yana can ma yana kallon tv, ta dan juyo kadan, haushi ya kama ta, ta saki dogon tsakin da har Adnan ya jiyo ya dube ta, haushi ya sanya ya miqe ya bi ta gefenta ya wuce.
"Oh no! plan A baiyi ba! amma ko da zan kai plan Z ne zan kai har sai nayi nasara"
Daga haka ta wuce daki, Khadija na tsaye tana jiranta duk ta qule.
Badiya ta shigo da takun isa da qasaita tana murmushi.
Ganin Khadija tsaye ya sanya ta kama kallon dakin tana murmushi. Kafin kuma ta dawo gaban Khadija tana kallonta cikin ido.
"Bazan iya jiran ranar da zan mallaki dakin nan ba, da zuciyar Adnan, a lokacin ne ke kuma kin qara gaba"
Khadija ta sadda kanta qasa hawaye cike a idanunta.
Badiya tana kallonta tace
"Meya faru? Kar dai kin fada tarkon sonsa kema!"
Da sauri Khadija ta juya mata baya ta goge hawayen da sukayi nasarar zubowa.
Badiya ta kyalkyale da dariya tana fadin.
"Ki bar asarar hawayenki a banza, in ma son Adnan kike to kiyi gaggawar fitar da shi daga ranki don Adnan nawa ne ni kadai"
Gaban Khadija ya yanke ya fadi, ta dake gami da juyowa tana dubanta.
"Na barki lafiya sai da safe"
Badiya ta jawo ta da sauri.
"Ina kike tunanin zaki je? Dakin Adnan? Nufinki can zaki kwana?"
Khadija tayi murmushinta mai kyau.
"Sosai ma zanje dakin mijina ko nayi laifi?"
Badiya ta dunqule hannunta ta naushi dayan.
"Wallahi baki isa ba kizo mu kwana nan mana tare ba inda zakije"
Khadija ta kyalkyale da dariya, don ma ta qara qular da ita sai ta wuce cikin drawer dinta, ta dauko wata irin rigar bacci baqa wadda da ka sa da kar kasa duk duk daya, Khadija ta daga rigar tana murmushi"
Badiya ta taho da sauri ta fizge rigar tana huci.
"Baki isa ba wallahi bazaki sanya wannan rigar ba" nan fa Khadija tayi baya Badiya ta bita, ta zille ta ruga a guje zata fita, Badiya ta fizgo ta tare da shaqe ta iya qarfinta.
"bari na kashe ki na huta shegiya aljana"
Khadija ta fara kakarin amai taji shaqa, tayi tayi ta qwace kanta ta kasa saboda Badiya kamar jikin maza gareta irin giant dinnan ce.
Badiya da gaske take kashe Khadija zatayi saboda idanunta sun rufe ga 6acin rai.
6angaren Adnan kuwa zai shiga wanka ya jiyo hayaniya ya fito da sauri ganin Badiya tana neman aika diyar mutane lahira, ya razana, ya yayi kukan kura ya fara qoqarin kwace Khadija.
"Sai na kashe ki wallahi..."
Shiru tayi a sanadiyar lafiyyayen marin da Adnan ya wanke ta dashi. Ta sake ta da sauri ga gami da fasa wata irin razannaniyar qara.
Tana sakinta, Khadija ta fada jikinsa tana neman numfashinta, idanunsa suka kada zuwa ja! Yana nuna Badiya.
"Ke bakida hankali, me kike qoqarin aikatawa kisa? Badiya kisa zakiyi? Da hankalin ki kuwa? Yayi kanta gadan gadan tare da fizgo ta daga dakin, sai ihu takeyi, bai tsaya nan ba sai da yayi sanadiyyar wurga ta waje yana huci yace.
"Ki koma gida yanzu zan kira Ummi a bude miki qofa gobe da safe zanzo gidan in sanar masu abinda kika aikata, tashi nace!" Ya wurga mata duba daya.
Ta tsorata matuqa ta fara roqonsa amma ina ransa a matuqar 6ace yake.
Da sauri ta miqe har tana tuntu6e ta fita da sauri dama motarta na wani wuri ta 6oye, don haka tana shiga ta ja ta bar unguwar da sauri gabanta sai faduwa yake.
Adnan na komawa dakin yaga har yanzu Khadija bata dawo daidai ba, daga ta yayi don yashe ya ganta qasa tana numfashi sama sama, ya dora ta kan gadon, wurin ajiye ta ne ya kalle ta yaga yadda ta wahala, ta basa tausayi sosai, bayan minti biyar ya zaune gefenta har sai da ta dawo daidai tukunna ya miqe har yanzu ransa a 6ace yake, ita kanta Khadija ta tsorata da yanayinsa, banda idanunsa da suka kada zuwa ja, har wasu jijiyoyi ake gani kwance saman wuyansa na 6acin rai!
Maryam S belloπ
ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
maryamsbellowo.wordpress.com
*πTagwaye ne? π*
Wannan page din na masu son Tagwaye su hadu neππto ga ranar ku tazoππΌππΌππΌ
37
Washe gari ta kama Monday, a ranar ne Khadija zata fara jarabarwarta (WAEC) tana kicin tana soya dankali, Adnan ya kunno kai yana sanye cikin suit kalar toka (ash) sai yar cikin fara da ratsin ash, kafin yayi wata magana qamshin turarensa ya tabbatar mata da ya shigo...
"Khadija ya jiki?"
Ta dan kalle shi tayi murmushi kadan tace
"Alhamdulillah lafiya ta lau ai"
Ya murmusa kadan shima yace
"Good... Idan kin gama hada kalacin ki kawo man ina falo, ki dan hanzarta saboda ina da emergency surgery qarfe takwas, kinga sai na fara dropping naki a school kafin na wuce"
To tace tare da qara himma wajen gamawa, bayan sun gama karyawa, tayi saurin fadawa bayi tayi wanka, ta sanya kayan makarantar ta ta kwashi litattafanta da duk wani abin amfani ta fito, a lokacin Adnan har ya fito bakin qofa ita kawai yake jira, a mota ma ba wanda yayi magana har ya sauke ta, a bakin gate din makaranta ne ta hadu da wata yar ajinsu mai suna Surayya Suraj, da sauri Surayya ta tari gaban Khadija tana mai murmushi, itama murmushin tayi mata bayan sun gaisa ne suka fara tafiya suna hira, har sun kusa aji Surayya ta jiyo ta kalli Khadija tace.
"Khadija dama kina da aure ko wannan yayanki ne?"
Khadija tayi murmushi kawai tana cigaba da tafiya
"Dan Allah fa nake tambayar ki?"
Khadija ta tsuke fuska
"To in banda abinki Surayya me zakiyi da aure na?"
"Babu komai nidai ki fada min"
Khadija ta sauke ajiyar zuciya
"Shikenan... Miji na ne"
Surayya ta zaro idanu waje tana fadin
"Wow! Khadija wannan zankadeden saurayin haka shine mijinki gaskiya kin dace"
Khadija ta qara tsuke fuska bata tanka ba, a daidai nan suka shiga aji.
Ta samu sit dinta ta zauna tare da bude litafinta domin qara nazari kafin su fara.
Bayan Khadija sun fito daga first paper ne tana zaune tana nazarin wanda zasuyi next wata yar ajinsu mai suna Samira Yusuf ta zauna kujerar kusa da Khadija tace.
"Khadija?"
Ta dago a hankali tana duban Samira tace
"Na'am"
Samira tana murmushi tace
"Dan Allah Khadija ki dan koya min Maths naga kin qware a nan sosai nikam ya shige min duhu"
Khadija tayi murmushi tace
"Ba damuwa"
Nan Khadija ta shiga koya ma Samira Maths har lokacin shiga second paper yayi.
Bayan sun qare ne Adnan ya zo daukar ta sai kallonsu akeyi har ta shiga mota.
* * *
Bayan Heenad ta dawo daga exams ne Khalil ke sanar mata yau zai turo magabantansa amma yayi magana dasu, zasu zo gaisuwa tare da kawo kudin neman aure daga nan har kayan sa rana zasu kawo, bayan Khadija ta gama karanta saqon Khalil ta whatsapp gabanta ya yanke ya fadi ta saki tsaki tana fadin.
"Zan aure ka ne bawai don ina sonka ba"
Ta sanar ma Mami saqon Khalil, Mami kuma ta sanar da Daddy.
Qarfe biyar na yamma suka iso, akayi musu iso har falon Daddy, bayan an gaggaisa, Kawun Khalil wato qanin mahaifinsa ya gabatar da kansa sannan sauran mazan guda uku suka gabatar da kansu a matsayin yayyun mahaifin Khalil, sun samu kyakkyawar tarba daga Daddy, don haka sunji dadi sosai, bayan an gama tattaunawa, suka bayar da kudin neman aure dubu goma, sannan aka bada kayan sa biki, an tsaida ranar auren wata daya masu zuwa, da Daddy yace asa wata biyu magabatan Khalil suka nemi alfarma wata dayan, kuma ya amince musu daga haka taron ya tashi.
Cike da zakwadi Khalil ya sanar ma Adnan abinda ya wakana, ya taya shi murna sosai koba komai zai huta da zancen Heenad.
* * *
BAYAN SATI DAYA
Yau ta kama Juma'a, Khalil da Adnan sun gama sallar magriba suna cikin mota, Adnan ne ke tuqi Khalil na zaune gaba suna hira. Cikin hirar ne khalil ke cewa.
"Gaskiya Adnan ya kamata ka raka ni wurin Heenad, baka ta6a ganinta ba, gashi har mun kusa sati biyu tare amman aminina bai ta6a raka ni zance ba"
Adnan ya dan kalli Khalil kafin ya maida kansa ga titi yayi murmushi.
"Nikam muje na ganta ko na huta da qorafi"
Khalil yayi murmushin jin dadi.
"To muje mana ni dama a shirye nake"
Khalil na gwada masa hanya suka iso.
Kasancewar guards sun san Khalil ya sanya suka barsu suka shiga, dama ya sanar da Heenad zuwansu harda abokinta.
Guard ya raka su har falo. Minti daya tsakani ta shigo falon, tsaye tayi sororo tare d qwalalo idanu waje, basu san ta shigo ba saboda ko wane wayarsa ce yake latsawa, ta dafe qirji tana karanto innalillahi wa inna ilaihir raji'un, ta koma baya da sauri ta fita daga falon, bazata ta6a mantawa da wannan fuskar ba...
Dakewa tayi ta fara tafiya kamar wacce qwai ya fashewa a jiki ta doka sallama, a tare suka amsa Adnan ne yayi saurin dagowa yana dubanta jin muryar Khadija, da mamaki yake kallonta tare da miqewa tsaye cikin firgici yana nuna ta. Itama tsaye tayi cak ta kasa wani qwaqwaran motsi, Khalil ya miqe da sauri yana kallon Adnan.
"Adnan lafiya dai?"
Cike da tsoro Adnan yace
"Baka gani ne? khadija fa ce tsaye a nan, meya kawo ta nan gidan?"
Khalil yayi murmushi ya dafa Adnan
"Kwantar da hankalinka ba ita bace kama ce kawai suke, wannan fa Heenad ce"
Khalil ya kalli Heenad yace
"Ki qaraso ki zauna mana"
Ta qaraso ta xauna gabanta sai dukan tara tara yake.
Adnan dai bai yarda kama ba saboda a iya saninsa ba'a kama haka sai dai ayi yanayi, in banda tagwaye babu irin wannan kamar a duniya.
Khalil ya numfasa ya kalli Adnan
"To Adnan ga matar da zan aura nan Heenad, Heenad ga abokina nan Adnan"
Gabanta ya yanke ya fadi
"Dama Adnan dinta shine abokin Khalil?" Ta tambayi kanta ashe zancen ya fito fili bata sani ba.
Adnan yayi tsai yana nazari tukunna yayi saurin cewa
"Dama kece wadda nake haduwa da ita, yarinya mai wulaqanci?"
Ta girgiza kanta alamun eh, Khalil fa kansa ya daure yace
"Wai meke faruwa ne ku fahimtar dani"
Adnan yace "ka bi a hankali zaka ji komai"
Nan Adnan ya labarta masa tun daga farkon haduwarsu har qarshe.
Cikin sanyin jiki Khalil yace
"Tabbas baki kyauta ba Heenad amma yanzu ai komai ya wuce ko?"
"Bai wuce ba!" Inji Adnan, sannan ya kunna wayarsa ya bude wani hoton Khadija wanda ya dauke ta bata sani ba ya miqa ma Heenad.
Da mamaki take kallon hoton, tabbas in banda bata san lokacin da akayi hoton nan ba da sai tace ita ce wannan, can kuma kamar ta tuna wani abu ta miqe jikinta na rawa tace.
"Anya wannan ba yar uwa bace?"
Sai kuma ta ruga da gudu wurin Mami tana haqi
Mami ta miqe a fusace tana fadin
"Lafiyarki kike gudu haka ina baqon naki?"
"Ma...mi duba hoton nan kigani nice?"
Mami ta duba hoton tace
"Kece mana amma ina ne nan kuma yaushe akayi hoton"
Heenad ta girgiza kanta
"Bani bace Mami, matar abokin Khalil ce"
Gaban Mami ya fadi ta dage qirji tana fadin
"Heenad anya ba yar uwarki bace wannan? Ina ji a jikina wannan yar uwarki ce muje wurin Daddy!"
Da gudu suka dunguma falon Daddy, shima da mamaki ya shiga tambayar lafiya.
Wayar Mami ta miqa masa, daga zaune ya miqe tsaye yana fadin wacece wannan?
Mami tace
"Matar abokin Khalil ce..."
"Ke Heenad kira min Khalil din"
Da sauri ta fice, can sai gata ta dawo Khalil da Adnan suna biye da ita a baya.
Daddy ne ya soma magana
"Khalil wacece wannan?"
Jikin Khalil yayi sanyi ya soma magana
"Matar abokina ce gaya nan Adnan"
Sai a sannan Daddy ya lura da Adnan ya miqe da sauri yana nuna shi.
"Adnan? Kaine?"
Adnan ya dago da sauri cikin daurewar kai yace
"Eh... Ni ne Adnan"
Daddy ya qwalalo idanu waje yana fadin
"Adnan Usman Buhari fa nake nufi?"
"Eh dansa ne"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!"
Duk su Mami suka miqe suma suna kallon Adnan.
Heenad ta fashe da kuka.
Daddy ya cigaba
"Adnan kalle ni, nine Alhaji Ahmad mahaifin Fatima wanda zaka aura aka fasa auren!"
Kafin Abba ya qara wata magana Adnan yayi saurin cewa
"Abba hoton wannan da kuka gani matata ce Khadija, bazan ta6a mantawa ina yaro aka haifi Tagwaye a nan gidan ba, daya ta rasu, sai dai na fara nazarin cewa wannan wadda ake zaton ta mutu bata mutu ba, akwai wani al'amari kullalle a tattar da lamarin, amma ko shakka babu Khadija yar uwar Heenad ce"
Mami ta miqe tana kuka, "Adnan don Allah muje ka kaini in ganta ko hankalina zai kwanta"
Adann yayi saurin cewa
"A'a Umma bari naje na kawo miki ita nima na qagu naji yadda lamarin yake"
Mami ta dakatar da shi da sauri
"A'a Adnan bazan iya haquri ba muje kawai, kowa ma haka yake cewa aje kawai ba yadda Adnan ya iya illa to da yace.
Minti talatin sun isa, da sauri suka fito daga motar Mami ce gaba Heenad na bi mata suna ta zuba sauri.
Adnan ya bude qofar gidan, Khadija ta fito daga kicin dauke da kofin shayi taga Adnan, tana shirin yi masa magana Mami ta kunno, Heenad na biye da ita.
Kofin Khadija ta yar a dalilil fuskar Heenad data ci karo da ita, Heenad ma nuna ta takeyi a yayinda Mami tayi mutuwar tsaye hawaye na bin kuncinta. Heenad ta taka har inda Khadija take, suka tsaya gab da juna suna kallon juna, kamar an tsaga kara an karya kamar tasu tayi yawa, cikin kuka Mami ta dafe qirji tana fadin.
"Yata! Dama kina raye?"
Adnan ya kalli Mami ya kalli su Khadija yana fadin.
"TAGWAYE NE????"
Kafin a bashi amsa wayarsa ta fara ruri, ganin Abbansa yasa ya dauka gami da yin sallama.
"Adnanu ka hanzarta ka kawo Khadija muna zaton anga mahaifiyarta ka kawo ta gida yanzu yanzu muna jiranku"
Maryam S belloπ
ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
maryamsbellowo.wordpress.com
*πTagwaye ne? π*
38
Cike da tsoro da kuma damuwa Adnan yace.
"Abba ne... Ana zaton anga mahaifiyar Khadija..."
Mami ta yi saurin cewa.
"Ba dai mahaifiarta ba domin batada wata mahaifiya sama da ni" tana hawaye take furta hakan.
Khadija ta fashe da kuka.
Mami kuka, Heenad kuka, Khadija ma kuka, dukansu an rasa mai lallashi wani. Ita Mami kukan jin ance Khadija nada mahaifiya amma ita tana da tabbacin ita ce ta haifi Khadija, Ita kuma Heenad kukanta bai wuce Adnan ba da tana ji tana gani yar uwarta ke auren shi wanda take da tabbacin Khadija jininta ce, tasan ta haramta gare shi har abada, saboda haka sai ta qara fashewa da kuka. Ita kuma Khadija abubuwa da yawa ke sata kuka, na farko Mami tace ita mahaifiayarta, ga kuma Ummanta an gani to ita yanzu wacece mahaifiyarta a cikinsu?
Adnan ya katse musu tunani da cewa
"Ya kamata ku zo mu tafi a warware mana qullin da ke qulle, duk kuka ba namu bane.
Basu musa ba illa bin bayan Adnan zasu kayi.
Cikin minti ashirin sun iso gidansu Adnan, ciki suka shiga da motarsu saboda dare, gaba daya suka dunguma ciki, a falon Abba sukayi tsinke, Abba na tsaye yana kai kawo shida su Isma'il a yayinda da Ummi da Hajiya Abu ke zaune kan kujera sun rafka tagumi, Khadija ce ta soma kalle kalle ganin inda Ummanta take sai dai wayam take gani, Abba yayi ma su Mami sannu da zuwa suka zauna, Heenad ma ta soma gaishe da Abba sai dai kallonta da zaiyi ya amsa ya hango Khadija itama tana shirin zaman qasa tana hawaye, kallonsu yake yi cikin firgici, ya kalli wannan ya kalli wancan, haka ma su Ummi da Hajiya Abu suka kama kallonsu cike da mamaki. Banda su Isma'il da suke masu kallon qurilla.
Ummi ce tayi saurin cewa
"Ina Khadija a nan?"
Hajiya Abu tace
"Nima bangane ta ba"
Adnan yayi murmushi ya nuna Khadija"
Ummi ta kuma cewa
"Wai meke faruwa ne bangane ba"
Adnan ya koro masu bayani tun daga farko har qarshe.
Abba ya numfasa yace
"Tabbas wannan lamari da akwai sarqaqiya a ciki, amma yanzu komai zai warware insha Allah" ya kalli Abba yace
"Babana a shigo da ita, a ga ko Khadija zata shaida ta a matsayin Ummanta"
Khadija ta miqe da sauri zata bi bayanshi, Abba ya tsaida ta ta hanyar daga mata hannu.
"Kar ki bishi Khadija yanzu zai shigo da ita ba nisa tayi ba"
A sanyaye ta dawo gabanta na cigaba da faduwa.
Falon yayi tsit ana jiran aga ikon Allah.
Minti biyar tsakani Abba ya shigo dauke da wata mata kan keken guragu, cikin firgici Khadija ta miqe.
"Umma!" Umma ta juyo a hankali ta kalli Khadija, take taji hawaye sun surnano mata, Khadija ji take kamar ta rungumo ta sai dai la'akkari da halin da take ciki ya sanya taja ta tsaye tare da fashewa da kuka.
"Umma ina kika shiga kika barni, meya same ki kuma?"
Mami hawaye suka zubo mata tace
"Nice mahaifiyarki Khadija"
Aka dunguro Umma tsakiyar falo sai raba ido take.
Khadija ta qarasa inda take tare da russuna wa ta kamo qarfen kujerar tana kuka. Sai kuma ta kwanta saman cinyar ta tana cigaba da kukanta.
Bayan an dan dauki tsawon minti daya babu wanda yayi magana, har sai da Umma ta kai dubanta ga Heenad da take takure wuri daya, take hankalinta ya tashi.
Abba ne ya katse shirun ta hanyar gyara murya tukunna ya dora.
"Dukkanmu mun taru a nan ne a bisa dalilin wadannan tagwayen da muka kasa gane shin TAGWAYE NE? Ko kuma daban daban aka haifesu, wanda babu wanda zai iya bamu amsa sai ku dinnan ku biyu, ya nuna Mami da Umma.
Mami tace
"Ni na tabbata Khadija yata ce saboda ni nasan tagwaye na haifa daya ta koma sai dai bisa ga yadda lamarin ya juye bana tunanin mutuwa tayi saboda hakan ina son a warwaye min abinda aka qulle"
Umma ma ta sauke ajiyar zuciya
"Nima banida abinda cewa da ya wuce Khadija yata ce tabbas nina haife ta ko shakka babu"
Falon ya kaurade da hayaniya, kowa na tofa albarkacin bakinsa.
Abba ya kuma cewa
"Ku duba girman Allah ku fada mana yadda lamarin yake kowanne mu a cikin duhu yake"
Nan falon ya kaurade da gardama Mami tace Khadija diyarta ce a yayinda Umma ke cewa Khadija ma diyarta ce, duk yadda aka dauki lamarin zaizo da sauqi ashe ba haka bane, da qyar Abba ya samu sukayi shiru, ya miqe jiki a sanyaye yace.
"Ina zuwa"
Can sai gashi da qur'ani izihi sittin ya dawo, ya zauna tukunna yace.
"Kufa nan ba yara bane, ko wace tasan inda ke mata ciwo saboda haka idan zaku 6oye mana ma to ga wannan ku dubi girman qur'ani, kuyi imani da abinda yake cikinsa, kunsan hukuncin wanda yayi rantsuwa da qur'ani akan qarya don haka ko wacce ta rantse da..."
Umma tayi saurin cewa
"Ran...tsuwa kuma? Ai ba sai na rantse ba Khadija yata ce"
Abba yace "dole ne ki rantse don a gano gaskiyar lamarin"
Nan fa Umma ta hau cewa ita fa bazata rantse ba sai da qyar Abba ya shawo kanta ta fara kuka sosai tana cewa zata fada.
Hankalin kowa ya dawo gareta, ta share hawayen fuskarta tukunna ta fara magana.
"Ku gafarce ni, Khadija kema ki gafarce ni, nasan abinda na aikata ban kyauta ba, amma a lokacin hakan nake ganin shine mafita gareni da kuma son biye ma zuciyata da taimkon yar uwarta har ta aikata hakan. Amma wallahi banida laifi...
"Da farko dai sunana Hasiya, mu yan jahar Bauchi ne can na taso tun iyaye da kakanni, a can na girma, ni kadai ce wurin iyayena, wanda suka dade basu same ni ba, sai daga baya aka haifeni, wannan dadewa da sukayi basu sami haihuwa ba shi ya sanya na taso cikin wani irin so da gata, bansan babu ba haka kuma bansan idan nayi laifi ba ace laifi nayi, haka na taso shagwabiya, yin abinda naga dama nakeyi, haka nayi makarantar masu kudi kasancewar mahaifina mai kudi ne sheyasa nake yanda naga dama, komai nakeso yi nakeyi, har Allah yasa na kusa gama makaranta sai dai me wata rana iyayena zasu Paris yawo suka yi hadari a jirgin sama suka mutu su duka, tun daga lokacin rayuwata ta sauya sai dai mahaifina ya bar mani dukiya mai tarin yawa.
Bayan wasu yan watanni na hadu da wani saurayi wanda nake mutuwar so, komai zan iya yi dan na faranta masa rai, shi kuma da yaga haka sai yayi ta min wayau yana wawurar min dukiya ni kuma sakarai ban gane ba, haka dai muka shafi wata biyu tare har daga baya ya bijiro min da maganar aure, ashe kuma so yake ya mallake min dukiya sannan ya gudu, ni kuma son da nake masa ya sanya na aure shi.
Da farko kamar gaske yana nuna min so da kulawa, yayi ta nuna yana qauna ta haka ni kuma na qara dilmawa cikin kogin sonsa sam idanuna sun rufe bana ganin laifinsa. Gashi ya hana ni karatu a cewar sa baya so ana gane masa ni yana kishina.
Haka dai muka shafe shekara biyar tare, ba haihuwa tun ina damuwa yana nuna min haihuwa ta Allah ce har na haqura, haka dai a hankali dukiyata ta fara qarewa.
Bayan shekaru goma da aure na sami ciki, nan na fara murna ashe shi kuma sam ba haka yaso ba bayason na haifi wanda zai mallaki dukiyata bayan shi, ashe shi yana nan yana neman hanyar da zai kashe min abinda ke ciki na, sai dai ko mai yayi baya nasara har na kusa kai watan haihuwa, nan na sa rigima nace bazan haihu nan qasar ba, ba yadda ya iya saboda bayaso na gane komai, yasa ya dauke ni muka tafi UK nida wata yar uwata.
A nan na zauna har haihuwata tazo muka tafi asibiti, sai dai shi yace man zai je ya dawo wai yayi mantuwa, bayan na kwashi minti talatin na haihu sai dai bansan me na haifa ba saboda nasha wahala ba kadan ba, bansan inda kaina yake ba.
Yar uwata mai suna Laila ita ke zama dani har aka zo mata da mummunan labarin cewar abinda na haifa ya koma, ta dimauta ta shiga tashin hankali ga tausyina tana ji yadda muka kwashi shekara da shekaru ba haihuwa amma farat daya na haihu babyn ya koma. Ta tashi tayi ta zagaye tana neman mafita saboda tasan idan na tashi zan iya mutuwa naji labarinnan.
Haka tayi neman mafita kafin ta sami labari an haifi yan biyu mata yanzu a asibitinnan, cikin sauri ta miqe tabi nurse din da taji tana maganar har dakin da jariran suke, a haka ta dawo dakina har yanzu bansan inda kaina yake ba, ta dauko jaririyar dana haifa ta fita da ita da sauri. Tana zuwa tayi sa'a bakowa dakin jariran, ta musanya mataciyar da mai rai, ta chanza masu abn rufa yadda bazaa gane ba ta fito da sauri ta koma dakina, a lokacin na farka ina kalle kalle, ina neman jaririna.
Ta shigo cikin murna ta miqa min jaririyar tace.
"Mace kika haifa"
Nayi murna sai dai banga mijina ba.
Na kalle ta nace "ina Sada ne?"
Tace itama bata sani ba tun dazu ya fita wai yayi mantuwa.
Ba'a juma ba wata nurse ta dawo dauke ta takarda wai inji Sada.
Aka miqe min na warware na fara karantawa kamar haka.
"Asalamu Alaikum gareki matata, nasan zakiyi mamakin karanta wannan wasiqa tawa, amma kafin nan ina so kiyi haquri da abinda xaki karanto.
Na farko dai dama ba sonki nake ba na aure ki kwadayin dukiyarki yasa na aure ki kuma alhamdulillah na kwashi rabona ke bama rabona ba har da rabonki na kwashe, ina so kisa a ranki bazaki sake ganina ba har abada, ga kudin komawa dai na bar miki ki koma qauye saboda nasan ba halin komawa birni don gidanku da gidanmu duka na hada na saida, aje a cigaba da cin kwaki da ruwa, hahaha! Allah sarki har kin bani tausayi, kiyi haquri fa haka rayuwa take wata rana qunci wata rana dadi. Kiyi haquri na yaudareki da nace ina sonki sam bana qaunarki!!! Daga qarshe ina so ki sani ni Sada na sake ki saki uku in kin samu miji kiyi aure, bissalam na barki lafiya.
Asiya Abdullahi"
Bayan na gama karantawa ban qara sanin inda kaina yake ba sai washe gari na farka, nayi kuka naji baqin cikin abinda Sada yayi min kuma har abada bazan ta6a yafe masa ba.
Bayan na dawo hayyacina aka sallame mu muka dawo qauye da zama, haka muke wuni ba ci ba sha saboda bamu dashi, ga bansan inda dangina suke ba ban dama ban ta6a zuwa inda suke ba.
Wata rana itama Laila ta kamu da rashin lafiya ga babu kudin kaita asibiti, haka tayi ta fama, ranar da zata mutu ne ta sanar dani Khadija ba diyata bace, ta nemi gafarata, ta kuma ce duk ranar da Allah ya hada ni da mahaifiyar Khadija ta asali na nema mata gafara, daga qarshe dai tace ga garinku nan. Nayi kukan rasa Laila dama ita kadai nake gani inajin dadin gashi yanzu ta tafi ta barni.
Haka muka cigaba da rayuwarmu mu biyu kadai har kika girma, wannan shine mafarin talaucinmu.
Umma ta numfasa tana kallon Mami.
"Tabbas nasan Laila bata kyauta miki ba, da ta raba ki da diyarki da kika dauki cikinta wata tara kika haifeta, don Allah kiyi haquri ki yafe mata kuskurenta, tabbas bani na haifi Khadija ba kece kika haife ta"
Gaba daya falon ya kaurade da salati.
Mami ta taso inda Umma take tace
"Na yafe miki Hasiya ba laifinki bane Allah ya yafe mana gaba daya"
Da sauri Heenad ta taso ta dago Khadija ta maqalqale ta tana kuka, itama Khadija kukan take kafin kuma ta saki Heenad ta juya ga Mami ta kamota ta maqalqaleta tana gunjin kuka, falon kowa sai da yayi hawaye, Adnan ya share hawayensa yana zancen zuci.
"Ashe dama ba ita bace ta mare ni kenan Heenad ce, haba no wonder naga Khadija cikin yanayin shigar nan"
Khadija ta share hawayenta ta kalli Umma.
"Umma akwai sauran abu daya da baki fada mana ba, ina kika shiga kika barni ko da yake naga halin da kike ciki amma garin yaya kika samu rauni?"
Umma ta share hawayenta tare da ajiyar zuciya tace.
Maryam S belloπ
ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
This page is for you kawalli Hauwee Bash❤️❤️❤️Allah ya raya mana Maryam da Asma'uπππ
maryamsbellowo.wordpress.com
*πTagwaye ne? π*
39
Ta hadiye wani qululun baqin ciki a lokacin da wasu hawaye masu daci suka gangaro mata, ta sa babban yatsanta ta share tukunna ta dora.
"Cikin dare da misalin biyu da kwata bacci ya qaurace ma idanuna, na tashi zaune ina tunanin yan uwana, gashi dai bansan inda suke ba amma zuciyata a ranar ta kasa samun sukuni so nike kawai in sa su a idanuna ko zan sami sukuni, saboda haka sai kawai na tashi na kama hada kayana da niyyar a yau dinnan zan kama hanyar garinmu, Allah yasa ma ina da wasu yan kudade hannuna, sai dai dalilin da ya sanya kika ga ban tafi da ke ba shine, yan kudaden da ke hannuna bazasu ishe mu mu tafi ba, kuma nasan idan na fada miki ba zaki yarda ki zauna ba, na kalle ki kina ta baccinki, tabbas nayi kuskure da na tafi na barki ba tare da nayi wani kwakkaran tunani ba, nayi kuka da baqin ciki sai dai a lokacin zuciyata ta makance da son sa yan uwana a idanuna, haka kuma na kudiri a raina cewar kwana biyu kawai zanyi in dawo, ashe Allah shi keda rayuwar mu gaba daya!
haka na sa kai na fice cikin daren nan na barki kwance kina ta bacci wanda na tabbata da safe zaki neme ni, ban zame ko ina ba sai tashar Bauchi koda naje aka ce sai safe zamu tashi, na zauna zaman jira har asuba mukayi sallah, bamu muka tafi ba sai takwas na safe, tsotsai wanda ba'a sa masa a rana, a ranar ne mukayi mummunan hatsari a hanyar mu ta zuwa, mutane da dama sun mutu nidai ban qara sanin inda kaina yake ba sai da kwana uku asibiti, haka na farka ba uhm ba uhm uhm sai dai ido, ba halin a tambayi yan uwana ko garinmu saboda ban magana, duk na karkare a kafa, haka nayi ta jinyar har na tsawon wata biyu tukunna suka sallame ni ban iya takawa, da qyar na dawo gida na zo na iske baki nan, bazan iya kwatanta miki tashin hankalin dana shiga ba, ina kuka na gurgura kaina naje gidan Inna Maria nayi tunanin nan kike, koda na shiga dama bahaushi yace shimfidar fuska tafi ta tabarma, tun daga nan nasha jinin jikina, bansamu
Kyakkyawar tarba ba daga Inna sai ma baqaqen maganganu da cin fuska, nayi mamaki ita ko tausayin halin da nake ciki ba tayi ba, na tambaye ta dalilil sauyin da nagani daga gareta tace munafuntar ta aka so yi, kaina ya daure kafin in qara magana Malam Sunusu ya shigo da sallama, shima ya jajanta mani bayan na bashi labarin halin da na tsinci kaina, nan ya bani labari tun daga farko har qarshe, ya dora da yadda ya sha nemanki amma bai same ki ba, baya can baya nan, haka dai daga qarshe ya haqura amma yana nan yana miki addu'a a duk inda kike, nan naci abincin rana wanda sai da Malam ya tilasta mata ta bani, daga nan na tattara na baro gidan na bazama nemanki, ga ni cikin wani mayuwacin hali amma haka nayi ta nemanki tunda koma menene nice sila, idan wani abin ya same ki Allah bazai barni ba.
Dazu qwatsam wurin wata asibiti naji ana cigiyata, an bada lambar waya ance duk wanda ya ganni yazo ga diyata Khadija. Nan na hau kukan murna, na gurgura na roki mai yin waya ya taimaka min banida kudi zanyi waya, mutumin kirki ya bani na kira aka dauka shine na bayayana kaina"
Tayi ajiyar zuciya tace
"Ki gafarce ni Khadija ki yafe min kinji abinda ya faru"
Nan Khadija ta rungume Umma tana kuka.
"Na yafe miki Umma na yafe miki"
Kowa falon sai da ya zubda qwalla saboda tausayi.
Bayan nan Khadija itama ta labarta mata tun daga tafiyar Umman har kawo yanzu da suke zaune a falon.
Umma ta qara kallon Mami tana zubda ruwan qwalla.
"Hajiya ki yafe min nasan ba'a kyauta miki ba, ga diyarki nan Khadija ta dawo hannunki kije kiji duminta taji naki, ku kuma ta kalli su Abba, nagode da riqe Khadija da kukayi har kuka sanya ta makaranta har kukayi mata aure a gaskiya babu abinda zance da ku sai fatan alkhairi Allah ubangiji ya saka muku da alkhairi"
Ta kuma kallon Adnan da ke zaune duk jikinsa ya mutu tace.
"Kaima nagode maka da ka auri Khadija ka riqe ta bisa amana ba tare da kasan ko WACECE ITA ba, Allah ya saka maka da alkhairi ya baku zaman lafiya" suka amsa da amin.
Mami ta tako inda Umma take tace.
"Babu damuwa haka Allah ya kaddara, kuma kema mun gode miki duk da kinsan Khadija ba yar ki bace amma kika riqe ta bisa gaskiya da amana, Allah ya saka miki da alkhairi ya baki lafiya insha Allah zamu taimake ki har sai inda qarfinmu ya qare zaki samu lafiya da yardar Allah"
Umma tayi murmushi
"Nagode qwarai Allah ya qara budi"
Duk aka amsa da amin.
Abba ya dora.
"Babu damuwa kar ki daga hankalinki ai shi da ma da na kowa ne kuma dama babu kyau wulaqanta DAN ADAM, saboda bakasan darajar da Allah ya dora masa ba, mu da muka riqe Khadija ban ta6a dana sani daidai da rana daya ba, na dauke ta tamkar yar cikina, kuma alhamdulillahi naji dadin riqonta da nayi gaskiya na jinjina miki a bisa tarbiyar da kika bata, ga nutsuwa ga hankali, ga ladabi ga kuma biyayya, kin cancanci lambar yabo.
Yanzu dare yayi sosai ya kamata a tafi a kwanta. Mami ta miqe Heenad ma ta miqe, Khadija tana so ta bi su Mami tana jin kunya, Adnan ne ya lura da hakan ya ce.
"Ya kamata ku tafi da Khadija taje gida taganku da mahaifinta, da yar uwarta"
Abba ya jinjjna.
"Haka ya kamata gaskiya, abinda za'ayi Adnan ka dauko mata kayanta ka kai mata taje ta kwana koda biyu ne tagansu"
Kafin su tafi sai da aka samo ma Umma makwanci Khadija ta taimaka mata tayi wanka taci abinci tukunna suka tafi gida.
Bayan sun iso, a bakin qofar shiga suka hadu da Daddy yana ta kai da kawowa, yana ganinsu yayi tsai cike mamaki yana kallon Khadija.
Sai kuma ya ware hannu yana zubda qwalla.
Da gudu ta fado jikinsa tana kukan farin ciki, ashe dama ita din YAR GATA CE! bata sani ba, sai da suka shiga falo suka zazzauna Daddy sai kallon yayanshi yake masu matuqar kama wanda ba'a ta6a bambance su, komai iri daya sak!
"Allah mai iko" ya fadi yana kara kallonsu cike da shauqin so irin ta da mahaifi, sun zauna dab da juna kamar za'a kwace ma juna su, Mami ma farin cikinta baya misaltuwa, haka sukayi zaune falo suna hira har wajen sha biyun dare, cikin qanqanin lokaci Khadija ta shaqu da Heenad fiye da misali, a ranar basuyi bacci ba haka suka kwana suna hira tsakaninsu, ko wace tana jin son yar uwarta cikin ranta"
Washe gari haka suka tashi cike da farin ciki tuni Heenad ta mance da yar uwarta ke auren masoyinta, haka Khadija tayi zamanta gidansu sam taqi yarda ta koma, Adnan sam bai ga laifinta ba saboda yanzu ne take sabawa dasu.
Khadija ta ga gata, kullum
Sai sun fita su duka shopping, komai iri daya haka ake siya musu, hartta waya sai da Daddy ya siya ma Khadija ya chanza ma Heenad tata, iri daya sak aka siya musu, duk inda suka je kallonsu akeyi yan tagwaye gwanin sha'awa! Biyu kyautar Allah..."
Kullum Daddy kesa driver ya kaisu exams idan angama ya je ya dauko ko wace ya maido ta. Da qyar aka samu aka maida Khadija gidan Adnan da alqawarin idan lokacin bikin Heenad ya taso zata dawo ta zauna har a qare.
Maryam S belloπ
ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
maryamsbellowo.wordpress.com
*πTagwaye ne? π*
40
Ranar da Khadija ta dawo da daddare tana zaune ita kadai a gida Adnan ya fita wajajen qarfe takwas saura, ta zura ma tv ido amma a zahiri hankalinta na ga yar uwarta wadda suka shaqu a yan kwanakin da sukayi, ta zurfafa tana tunani tare da ayyana kamanninsu, can kuma tayi murmushi wanda yayi sanadiyar lotaswar kumatunta duka biyun, banbancinta da Heenad wurin lotsawar kumatu ita na Heenad 6angare daya yake lotsawa sa6anin ita da duka biyun ke lumtsumewa. Ta jawo wayarta qirar iPhone 7 plus dinta, ta bude hotunan da suka dauka da Mami da Daddy, da kuma wanda suka dauka da Heenad, hankalinta ya karkata ga selfie din da sukayi cikin shiga iri daya wanda Heenad ce ta dauka, hoton ya qayatar da ita, ta gama kallon hotunan sannan ta soma tunanin duka rayuwarta da gararin da ta shiga, take kuma hawaye suka zubo mata, ta sa siririn yatsanta ta share, sai kuma tayi murmushi a lokacin da taji shigowar motar Adnan, bugun qirjinta ya qaru, ta daidaita nutsuwarta a lokacin da ya shigo falon da sallama, kallo daya zakayi masa ka tabbatar da gajiyar da ya kwaso, kan kujera ya zube tare da lumshe idanu yana murza kansa dake barazanar yi masa ciwo.
"Kodai baya jin dadi ne?"
Ta fada a ranta, tana so ta je tace masa wanka zeyi ko kuwa ta kawo masa abinci tana jin kunya, nasihar Mami ta tuna a ranar da zata dawo.
"Khadija, a yau ne zaki koma dakinki, abinda nake so da ke shine ki kula da mijinki shine gatanki a yanzu, ki jawo hankalinsa gareki, sai kin cire wannan kunyar Khadija idan ba haka ba kina ji kina gani wannan Badiyar zata qwace miki shi amma idan kika dage wajen faranta masa rai, zakiga chanji, sannan ki daina burguza wannan hijabin idan yana nan ga wasu kaya can na siyo miki na zaman gida, ki kasance kullum cikin tsafta dan Allah Khadija, kullum ya ganki fes, Allah yayi miki albarka"
Ta sauke ajiyar zuciya ta miqe kamar wacce qwai ya fashewa a jiki, koda ta isa inda yake sai ta kasa magana, tayi tsaye tana tunanin ta inda zata fara, sai motsa lips nata take a qarshe dai ta sudada tace.
"Sa....nnu da da...wo...wa"
Ya bude idanunsa kadan ya sauke su kan Khadija tukunna ya miqe zaune yana murmushi kadan.
"yauwa Khadija nagode"
Ta girgiza kanta kadan.
"Ya kamata kayi wanka ko abinci zaka fara ci?"
Ya dan bude idanunsa a sanadiyar nauyin da sukayi masa saboda ciwon kai yace.
"Wanka zanyi, bana ci abinci da daddare daga fura sai tea nake sha, amma inaga yau tea dinnan zan sha, ki hado min kar kisa madara ruwan lipton kawai sai zuma"
To tace a yayin da ta juya zuwa kicin.
Ya miqe da qyar ya shiga daki, kai tsaye bayi ya fada yayi wanka da ruwa masu zafi, ya fito ya tsane jikinsa tukunna ya shafa cream, jallabiya ya sanya kalar qasa, da dogon wando ya gama da minti sha biyar shiru ba Khadija ba tea, ya dauko wayarsa ya tura mata saqo kamar haka.
"Ki kawo min tea din daki bana jin dadi"
A lokacin tana tsaye kicin riqe da tea din da har ya huce, taji shigowar saqo, ta dauka bayan ta karanta, gabanta ya fadi. Anya zata iya shiga dakinsa? Bayan ta gama zancen zuci ta sanya tea din a microwave bayan yayi zafi ta soma tafiya sashen Adnan cike da tsananin tsoro da fargaba. A hankali ta tura qofar dakin da sallama, karo na farko da ta soma shiga dakinsa, wani irin sanyin ac hade da qamshin dadi ya daki hancinta, ta qarasa shiga, kwance yake saman gado rigingine dafe da kai, ta ajiye saman side drawer, sannan ta kalle shi tana shirin magana ya bude idanunsa, ta hade hannayenta tare da sunkuyar da kanta qasa tace.
"Ya jiki?"
Ya murmusa kadan sa'ilin da ya miqe zaune kafuwansa na qasa, kusa da shi ya nuna mata wai ta zauna, a kunyace ta zauna dan nesa da shi tana wasa da yatsanta. Yayi murmushi mai bayyana haqora yana kallonta, shi kansa ba zai iya misalta yanayin da ya shiga ba, cikin wata irin husky voice ya ce.
"Mijinki bayada lafiya amma bazaki iya kula da shi ba ko?"
Ta yi murmushi kadan tana girgiza kai alamun a'ah.
Shima murmushin yayi ya miqo mata kofin shayin.
"Oya ki dinga bani a baki"
Ta zaro idanu waje
"Baki son lada ne?"
Tayi shiru, ya maimata
"Lada fa zaki samu Khadija ki bani a baki mana"
Yanayin yadda yayi maganar ya sanya ta jin kunya da sauri ta sadda kanta qasa tana murmushi sannan ta sa hannu ta amshi kofin, ta riqe tana kallon kofin.
Ya kalle ta yace
"Ke fa nake jira"
Ta runtse idanunta a yayin da gabanta ya bada ras! A kasalance ta sa mishi a baki, ya lumshe idanu sa'ilin da wani abu ya ratsa mishi tun daga saman kai har tafin qafarsa. Haka Khadija ta dinga shayar da shi shayin nan har ya kammala, ta miqe zata fita daga dakin yace.
"Ya zaki fita tun yanzu ya kamata ki dan matsa min kai na ko zai daina ciwo"
Ta runtse idanunta tana mai tsananin jin kunya.
Ya koma ya kwanta yace
"Ina jira fa"
Ba yadda ta iya illa ta dawo ta matsa masa kan, Adnan har wani lumshe idanu yake, ko kuma ya bude ya qura mata idanu, ita kuma ta sadda nata qasa, kadan kadan take satar kallonsa, har bacci ya soma yi ganin ta gaji ya sanya yace.
"Nagode Khadija naji sauqi jeki abinki amma idan kin shirya kizo mu kwanta"
Gyada kai tayi alamun to sannan ta dauki kofin tea din ta fice.
Bayan fitarta Adnan yayi murmushi tare da lumshe idanu, wani irin sonta yaji yana ratsa dukkanin illahirin jikinsa, bai qi ba ta dawo yayi ta kallonta har safe.
Bayan Khadija ta kai kofin tea din ta koma dakinta ta sanya kayan baccinta riga da wando ta fito tana addu'a ga tsoro ga fargaba. Da qyar ta shiga dakin ta iske Adnan nata bacci, ta kalle shi tare da sakin murmushi yadda yake baccinsa sai yayi mata kyau, ta koma qarshen gado ta kwanta tare da takure kanta wuri daya, can taji Adnan ta gangaro inda take tare da maqalqale ta, take tsoro ya kuma cikata, da dinga kyarma kamar mai jin sanyi, Adnan ya miqe da sauri tare da kunna fitilar dakin yana kallonta yace.
"Kwantar da hankalinki Khadija ba abinda zan miki kiyi baccinki"
Ya dan matsa kadan daga inda take, sai a lokacin ta sauke ajiyar zuciya, Adnan kam ya kasa bacci sai kallon Fuskar Khadija yake da ke bacci, bazai iya kwatanta yadda take da kyau ba, ashe dama haka take? Ya tambayi kansa sa'ilin da ya kwanta yana kallonta, a haka bacci ya sace shi.
Haka Khadija ta farka da asuba ta ji Adnan riqe da ita gam, motsinta ya farkar da shi, ya miqe da sauri yana duba agogo ganin lokacin sallah yayi ya sanya ya miqe da sauri ya fada bayi, a yayin da Khadija ta fice zuwa nata dakin don gabatar da tata sallar.
Haka suke gudanar da rayuwarsu kullum son Khadija dada qaruwa yake a cikin zuciyarsa a yayin da Khadija ke fama da jin kunyarsa, amma ya kudiri aniyar kauda kunyar nan don tana cutarsa.
Bayan kwana biyu Abba ya biya aka fidda Umma waje zuwa qasar (Cairo) Ummi da Hajiya Abu ne suka raka ta don neman lafiyarta.
* * *
Satin Khadija daya da dawowa suka kammala jarabawarsu, a lokacin kuma saura sati biyu bikinsu Heenad, safiyar ranar tafiya ta kama Adnan Kano shida wani abokin aikinsu zasu gudanar da wani aiki sai sun kwana uku zasu dawo.
Tana zaune falo aka qwanqwasa qofa ta miqe tare da leqawa ganin Heenad ya sanya tayi saurin budewa cike da farin ciki.
Suka rungume juna suna murna, ta kalle ta da yar jakarta (kit) tana murmushi tace.
"Ya naganki da kit kwana zakiyi?"
Heenad ta girgiza kai tana murmushi. Dadi Khadija ta ji,ta ansa kit din daga hannunta ta kama hannunta suka shigo ciki.
Dakinta ta kai mata kit din ta dawo falo inda take zaune tana latsa waya. Ganin Khadija ya sanya ta saki murmushi.
Khadija ta qaraso tana murmushin itama bayan ta zauna ta shiga tambayar su Mami.
"Lafiya lau suna gaishe ki"
"Ina amsawa kin karya kuwa?"
Ta girgiza kai alamun a'a
Khadija tayi murmushi.
"Muje mu hada kalaci nima ban karya ba"
Tare suka shiga kicin suka dafa indomie da qwai, suka dawo falo suna hira suna ci har suka kammala. Khadija ta kai kicin don wankewa. Heenad na zaune nan taji sallama, ta miqe tana fadin waye tare da budewa.
Badiya ce tsaye da irin shigar data saba. Tana taunar cingam tana wani cika tana batsewa.
Ta harari Heenad daga sama har qasa tace
"Iyye akuyar daure an samu sake, daga nayi tafiya kwana biyu sai ki kama yin yadda kika ga dama ko? To baki isa ba wallahi kinyi kadan bani hanya na wuce ni"
Tana niyyar bangaje Heenad, Heenad ta sa hannu ta hankade ta tayi taga taga zata fadi.
A fusace Heenad ta soma magana
"Wacece ke? Har kin isa kizo gidan mutane kina musu masifa to baki isa ba wallahi don ke karamar yar iska ce wallahi"
Heenad ta taho a fusace zata dake ta Heenad ta riqe hannunta gam sannan ta wanke ta da mari.
Badiya zata qara magana ta kara jin saukar mari a dayan kuncin.
Heenad ta fizgo ta zuwa falo tana masifa.
"Nace ki fada min ke wacece karamar yar iska ni nan na fiki iya tashanci wallahi ke qaramar qwaro ce!"
Badiya fa abin ya bata mamaki yaushe Khadija tayi baki haka.
Jin hayaniya ya fiddo Khadija.
"Heenad lafiya nake jin hayaniya?"
Badiya ta miqe a razane tana ja da baya tana nuna Khadija da Heenad.
Muryarta na rawa take fadin.
"wacece ke? Ina Khadija a nan?!" Ta fada iya karfinta tana haqi.
Heenad ta yo kanta gadan gadan tana so ta qara wanka mata mari Khadija ta hana ta.
"Kyale ta haka Heenad"
Badiya ta fadi cikin daga murya.
"So dama labarin dana ji ke yan biyu ce ashe da gske ne? To bari kiji in fada miki ina nan akan bakana na wargaza farin cikinki sai kin gwammace dama baki aure Adnan ba domin nasha fada miki yafi qarfinki!"
Heenad ta kyalkyale da dariya.
"Kaji banza wai dama saboda mijin wata kike wannan haukan? To ki bude kunnenki da kyau ki jini, ke baki isa ba ki shiga rayuwar yar uwata ba, wallahi sai inda karfina ya kare akanta, saboda haka ki kiyaye!"
Maryam S belloπ
No comments:
Post a Comment