ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
maryamsbellowo.wordpress.com
*πTagwaye ne? π*
47
Bayan likitan ya gama bayani su Abba suka miqe jikinsu yayi mugun sanyi, haka suka fice daga dakin.
Koda suka je Badiya na ta kukan azaba, cikin tashin hankali Khadija ke kiran sunanta, Abba suka iso da sauri suna tambayar lafiya. Cikin kuka Khadija tace
"Wai qafarta ke ciwo"
A sanyaye Abba ya fice likitan ya samu yace a bashi yasa hannun yi mata aikin, bayan ya kammalla ya biya kudaden da ake buqata.
*4:30 PM*
Har yanzu an kasa sanar ma Badiya aikin da za'ayi mata, don kuwa qarfe biyar na yamma za'a shiga da ita, kowa da kowa na zaune dakin da aka kwantar da Badiya an zuba mata idanu don kuwa tace akwai maganar da zata fada.
Ta sauke ajiyar zuciya idanunta cike da nadama ta soma magana.
"Ku gafarce ni musamman Khadija da Adnan, Khadija duk wani tashin hankalin da kika shiga a gidanki a kwanakin baya nice sila, qawata takanas na tura ta wurin boka don tasa ayi miki aiki, sannan Abba kayi haquri nayi maka qarya nace zanje gidan gaisuwa wurin bokanya zamuje shine... Shine mukayi accident"
Dakin ya kaurade da salati, Khadija hawaye kawai takeyi, tabbas Badiya ta cuce ta amma Allah ba azalumin bawa bane ba.
Abba ya numfasa yace
"Ai dama kallonki kawai nakeyi tunda akace hanyar Dan ja hakan ta faru da ku nasan cewa ba banza ba, Badiya ba tun yau ba nake miki fadan ki kiyayi duniya bakiji, kullum cikin yi miki fada nakeyi amma bakyaji, wannan abun ina ragwanta miki ne saboda yayarki Zainab, kinyi tunanin bansan abubuwan da kuke aikatawa ba dake da yayarki ba komi kukayi ya na dawo min a kunne, ko kina tunanin bansan kunje wurin wani malami ba don ayi miki aiki kan Adnan, Badiya yanzu har ku kauce hanya meyakon ku roki Allah sai kuje kuna rokon bokaye da malamai? Duk haukan da kike kan Adnan nasani to kisani wannan ba soni bane hauka ne, sannan shi Allah ba'ayi masa wayau ko dole, duk zuwa da kikeyi gidansa kina ma matarsa rashin mutunci nasan komai komai, kawai kallonki nakeyi, har fadan da kukayi da Fatima yar uwarta nafasan komai. Yanzu gashi nan Allah ya kamaku ya sa kunyi hadari wanda a sanadiyyar haka sai an yanke miki qafa..."
Wata irin kururwa tayi hade da razzananiyar qara.
"Wallahi baza'a a yanke min qafa ba, wayyo Allah na shiga uku don Allah kar ku raba ni da qafata"
Abba ya miqe "komai ya faru da ke ke kika ja, sannan dama ABINDA AKE GUDU kenan shiyasa kullum nake dada ja miki kunne akan halin rayuwa bakyaji"
Daga haka ya fice daga dakin zuciyarsa a cunkushe, su Mami ma sunzo sun duba ta suka tafi, dakin ya rage daga Heenad sai Khadija sai kuwa Badiya da ke ta kuka kamar ranta zai fita.
Heenad ta kalle ta ta ta6e baki
"Dama ance ramin mugunta ka gina shi gajere idan ba haka ba kaine zaka rufta ciki kuma gashi nan kuwa kin fada tsindum cikinsa"
Khadija ta katse ta
"Don Allah Heenad kyaleta taji da abinda take ji ki tausaya mata mana"
Heenad tace
"Ai dama na tausaya mata amma fa dole a fada mata gaskiya komai dacinta"
Tana rufe bakinta likitan ya shigo cikin kayan tiyata kalar sararin samaniya (sky blue), cikin hikima sukayi mata allurar bacci suka ja gadonta su Adnan na tsaye aka shiga da Badiya kowa kam ya tausaya mata.
Ba'a fito da Badiya ba sai kusan shiddan marece kowa ya ganta sai yaji tausayinta, haka kuma bata farfado ba sai bayan isha'i. Da kyar ta sha tea shima in banda kuka babu abinda takeyi.
Washe gari su Ummi suka dawo shima daga airport kai tsaye asibitin suka wuce, koda Badiya taga yayarta sai ta fashe da kuka, nan ta rungume ta tana gunjin kuka, Ita Khadija kuwa farin cikin ganin Umma ya hana ta saqat, ta warke kamar ba ita ba. Badiya tayi nadama marar iyaka hade da dana sani a sanadiyar hakan taji tsanar Adnan don a tunaninta duk saboda shi ta rasa qafarta.
* * *
BAYAN KWANA BIYU
Heenad na dakinta tana shirin bacci, Khalil ya shigo hade da yin sallama, bata kalle shi ba amma ta amsa, zama yayi kan gado yana kallon yadda take taje dogon gashin kanta, cikin sanyin murya ya soma magana.
"Fatima"
Bata jiyo ba amma ta amsa
"Na'am"
Yaji dadin hakan, don haka sai ya cigaba.
"Fatima ina so ki fada min idan har baki sona ni kuma nayi miki alqawarin baki takardar ki bana so kina kwasar zunubi saboda abubuwan da kike min a matsayinki na matata, kinsan wannan abin da kikeyi zai iya kaiki ga wuta? Sheyasa na keso muyi magana ta gaskiya da ni da ke a yau, shin Fatima kina sona ko kuwa baki sona? Wallahi tallahi idan har kika ce baki sona yau dinnan zan baki takardarki!"
Ta tsaya cak, kirjinta ya bada dam! Ta runtse idonta kafin ta bude sannan ta juyo a hankali ta tako kamar mai tsoron taka qasa ta zauna dan nesa da shi, tana kallonsa, ta tsorata yanayin da ka ganshi, saboda yadda idanunsa suka rikide zuwa ja, sannan ga qwalla data cika idonnasa, ta sadda kanta qasa a yayinda da tausayinsa ya mamaye dukkannin illahirin jikinta a karo na farko!"
Hannunta ya kamo yace
"Ke nake sauraro"
Tayi shiru a yayinda qwalla suka cika mata idanu, ya lura da hakan amma sai ya basar saboda yana so tayi nadama sosai.
Ya cigaba.
"Fatima ki fada min gaskiyar abinda ke cikin zuciyarki game da ni, nidai a nawa 6angaren kinsan irin son da nake miki ba tun yau ba, ina qaunar ki amma zan iya haqura saboda farin cikinki" ya karasa muryarsa na rawa.
Hawayen da suka maqale mata sukayi nasarar saukowa. Yasa yatsansa ya share mata yana kallonta cikin ido.
Miqar da ita tsaye yayi yace
"Kin shirya rabuwa dani? Kin shirya barina? Sannan ni kuma na shirya rabuwa da ke domin samuwar farin cikinki"
Ta soma girgiza kanta da sauri hawaye kuwa wani na korar wani.
Rungumo ta yayi tsam a jikinsa yana shafar bayanta a hankali.
"Shikenan ya isa ki bar kukan hakan..."
Ta katse sa da sauri
"Don Allah ka yafe min abinda nayi maka a baya please"
Wani irin farin ciki ya ji wanda bai ta6a jin irinsa ba, a ranar Khalil sai da ya jiyar da Heenad dadin da bai ta6a jiyar da ita, a ranar Heenad ta amince da Khalil a matsayin mijin aurenta!
Maryam S belloπ
No comments:
Post a Comment