ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
maryamsbellowo.wordpress.com
*πTagwaye ne? π*
44
Fuuu tayi dakinsu tana ta kumbure kumbure, Goggo tayi murmushi ta dauko kwandon da ta kai ma Heenad abinci ta hade da wanda ta juye sannan da dibar ma Khalil cikin dan karamin flask ta dibar masa kosan ta kai falonsu. Dama tasan yana gab da shigowa gaishe ta domin qa'idarsa ce idan ya dawo daga sallar asuba sai ya fara shigowa ta nan, yau dinma hakan ce ta kasance, tana shirin shiga daki ya doka sallama, ta fasa shiga ta dawo falon ta zauna a yayinda da Khalil ya zauna qasa kusa da ita, bayan ya gaisheta ta amsa da fara'a sai kuma tayi tsai tana kallon danta wanda take zaton da akwai matsala domin Khalil ma'abocin dariya ne da fara'a hade da zolaya ko barkwanci, kuma kullum ya shigo sashensu da wasa da dariya ake rabuwa amma yau sai ta ga akasin haka, ta numfasa ta jawo masa abincin da kanta ta zuba masa tace.
"Ci"
Ya girgiza kansa yace
"Na qoshi Goggo bana jin yunwa"
Ta kalleshi
"Bansanka da qarya ba Khalil kuma kar kace zakayi min kaci abincin nace"
Gudun 6aci ranta yasa ya fara ci, yana ci suna ta6a hira kadan"
Husna ta katse musu hirar tasu da sallama ta shigo tana ta mita, Khalil ya dago ya dube ta bayan ya kur6i kokon yace.
"Ke lafiya?"
Ta zaune saman kujera ta soma magana
"A gaskiya yaya matarka batada hali ko kadan..."
Goggo ta bige mata baki.
"Kar na kuma jin kin ce mata batada hali, ba matar yayanki bace? Iye na sake jin magana makamancin wannan sai na 6ata miki rai"
Husna ta fashe da kuka, tana qara jin tsanar Heenad cikin ranta.
Khalil ya dago da mamaki yace
"Goggo wai me tayi mata haka ne?"
Goggo tana murmushi tace
"Can tsakaninsu taje taja amarya fada nasan tayi mata fada shine tun dazu take wannan mitar"
Khalil ya kammala cin abincin ya miqe yana duba agogo.
"Goggo bari naje nayi wanka kar na makara wurin aiki"
Tasa masa albarka da haka ya fice yana saqa da warwarewa cikin ransa.
Bayan fitarsa ne Goggo ta kalli Husna cikin muryar lallashi tace
"Ke Husna ba'a haka kinji ko? Haquri akeyi da rayuwa ni na tabbatar nan gaba ko ance tayi haka bazatayi ba"
Husna ta dago tare da gyada tace tace
"To"
Goggo tayi murmushi
"Yauwa yar albarka tashi kije ki gyara kayan miya a markada"
Da haka ta miqe tayi kicin tana share hawaye.
* * *
Da shigarsa ya taradda ita kan dinning tana karyawa, ya qaraso yana dan murmushi yace
"Amarya bakya laifi koda kin kashe dan masu gida"
Ko kallonshi batayi ba ta cigaba da cin abincinta.
Ya jawo kujera ya zauna yana fuskantarta yace
"Amarya ina nawa abincin?"
Ta yi banza dashi
Ya kuma maimatawa
"Ke kadai kika girka ma kanki?"
Bata tanka ba kuma sai ma miqewa da tayi ta bar masa wurin, daki ta koma ta fada toilet don yin wanka.
Minti biyu yayi zaune yana nazari, sai kuma ya miqe ya nufi dakinsa shima wankan ya shiga ya fito ya hade cikin baqin yadi mai taushi, baqar hular yasa da takalmi baqi, farar fatarsa sai ta hau da kayan da ya sanya.
Dakinta ya nufa tana kan gado ta baje tana latsa waya, yayi murmushi ya karaso inda take yace
"Cutie zan fita akwai abinda kike buqata?"
Bata ko kalle shi ba tace
"A'a"
Yayi murmushi ya fiddo dubu biyu yan dari biyar ya aje kusa da ita yace
"Sai na dawo ki kular min da kanki"
Bayan fitarsa taja dan guntun tsaki ta dauko kudin ta wurgar ta cigaba da abinda take.
Heenad na nan har qarfe sha biyun rana ta kasa tashi ta ta6uka komai, kanshi gadon da take kwance bai samu gyara ba bare kuma kicin da sauransu.
Ta gaji da latsa waya ta miqe tana tsaki, ita kam wannan rashin wuta ya ishe ta, ita bata saba da rashin wuta ba, ga wayarta tana neman mutuwa ma. Ta miqe a dalilin zafin da ta taji ta rage kayan jikinta.
Mami ta kira suka gaisa sannan ta kira Khadija itama sun dade suna hira daga bisani sukayi sallama.
* * *
Khadija na tsaye gaban madubi tana sanye da baqar doguwar riga marar hannu, gashin kanta take gyarawa, Adnan ya shigo dakin daga baqin qofa yaja ya tsaya yana kallonta cikin shauqin so kamar ya hadiye ta ya yakeji.! Sai data kusa kammalawa taji an rungumo ta ta baya ana kissn kanta. Ya juyota a hankali yana kallonta, zuwa yanzu Khadija ta dan rage jin kunya amma ba duka ba.
Yayi murmushi ya jawo ta zuwa kan gado ya zaunar da ita tare da kamo hannayenta duka biyu cikin nasa. Tayi murmushi kanta na qasa, kamo ta yayi gaba daya ya rungume yana shaqar qamshinta. Sakinta yayi ya miqe yana maida numfashi yana toshe hanci, a razane ta dago taga yaja baya toshe da hanci. Cikin sarqaewar murya tace
"La...fiya dai?"
Ya daure yana jin tuqar amai yace
"Khadija don Allah kije ki chanza turare wanann baida dadi"
Ta miqe jiki babu qwari ta shiga bayi ta cire kayan gaba daya ta sauya wasu ta fito daga bayin. Kafin ta iso gareshi ya miqe yana yunqurin yin amai, da gudu ya fita daga dakin yana haki, da sauri Khadija ta bishi daga bakin dakinsa ta fara jiyo kakarin amai, ta shigo tare da leqawa, hango ta yayi yace.
"Dan Allah ki fita kar ki qaraso"
Ya fada da qarfi cikin daga murya.
Da gudu ta fita tayi dakinta ta sunsuna kanta taji bataji komai ba, ta fashe da kuka ita kam ta rasa meyake ji ajikinta.
Dakinsa ya zauna yana tunani, 6angare daya ga son Khadija yanayi, amma sai yakeji baya qaunar ta matso kusa da shi....
Yafi minti talatin zaune dafe da kai, daga qarshe ya miqe ya fita, sheshekar kukanta yaji, ya nufi dakinta da sauri, sai dai yana shiga daga bakin qofa ya fito da sauri toshe da hanci.
Maryam S belloπ
No comments:
Post a Comment