๐๐๐๐❤
๐๐๐๐
๐๐
๐
MSB๐
maryamsbellowo.wordpress.com
®TALENTED WRITER'S GROUP (TWG)✍๐ป
*๐Tagwaye ne? ๐*
LAST PAGE✂️๐
55
Bayan sunyi arba'in ko wace aka maida ta gidanta.
A lokacin kuma suka soma registration ta sabuwar shekara. Cikin hukuncin Allah karatunsu yana tafiya daidai basuda wata matsala, domin ko wace ta maida hankali ba kadan ba tana karatu.
Wata rana Heenad na shayar da Adeel Abida ta shigo da sallama fuskarta a daure alamun fushi takeyi da Heenad. Abida ta zauna ta bude jakanta ta miqo mata kati tana fadin.
"In kinga dama kizo bikina next week ne"
Har ta miqe zata fita da azama Heenad ta jawo hannunta.
"Haba kawata don Allah kiyi hakuri, nasan ban kyauta miki ba, amma ba don ni ba don Allah ki yafe min"
Abida ta qara tsuke fuska
"Yanzu yadda muke dake har ki haihu bansani ba, Heenad yanzu kin kyauta kenan?"
Heenad ta kamo hannunta
"Nasani Abida kiyi hakuri please"
Abida tayi ajiyar zuciya
"Shikenan na yafe miki amma kar ki qara irin haka kinji?"
Heenad tace "insha Allah"
Abida tasa hannu ta amshi Adeel tana masa wasa a yayinda ta miqe zuwa kitchen ta samo mata abin motsa baki.
Can ta dawo ta zauna ta soma bude kwalbar pepsi ta tsiyaya mata ta miqa mata tana murmushi.
Abida na sha suna hira irin ta kawaye, can Heenad tace "amarya, Allah ya kaimu lokacin"
Abida ta amsa da amin tana cigaba dayi ma Adeel wasa cike da nishadi.
* * *
BAYAN SHEKARA UKU (THREE YEARS LATER)
Heenad da Khadija na hanga sun cika da murna domin a yau dinnan shine ranar da ake yaye daliban Turkish Nile da suka kammala karatunsu lafiya, yan uwa da abokan arziki sun halarci taron, bayan taron ya watse su Khadija suka fito hannunta riqe da Haifah yarinya kyakyawa yar kimanin shekara uku tana ta zuba surutu, a yayinda Adnan ke tsaye waje daya shida Khalil suna tattaunawa hannunsa yana dauke da Afra tana masa wasa da dogon hancinsa lol.
Gefe guda Heenad ce da kawayenta suna maida yadda akayi sannan gata dauke da tsohon ciki wanda da qyar take tsayuwa tsabar nauyi.
Cikin nishadi aka kammala daga nan wani restaurant suka nufi gaba dayansu mai kyau da tsada, abinci suka ci suna ci ana raha gwanin sha'awa, duk dai mazajensu sunyi hakan ne domin taya su murnar kammala karatunsu lafiya.
Bayan kwana biyu Heenad ta haifi yan biyunta wannan karon mata ne farare tas, masu kama da baban kamar an tsaga kara an karya. Ranar suna yaran sunci sunan mahaifiyar Khalil (Nafisa) ana kiranta da Basma, sai dayar taci sunan Mami ana kiranta da Ihsan.
* * *
Da sallama suka shigo Mami na kwance saman doguwar kujera tana hutawa, dukkansu suka shigo da sallama, Mami ta miqe zaune da fara'arta ganin jikokinta guda biyar sun shigo da gudu, Basma ce gaba sai Ihsan suka dale cinyarta suna 6a66aka dariya, can sai ga Adeel da Afra da Haifah da suke da kimanin shekara biyar suma suka zauna kusa da ita. Tana dariyar jin dadi tace
"Daga ina kuke haka ina iyayenaku?"
Sukayi dariya, Basma uwar surutu ce tace
"Cuna gida mu kalai muka zo"
Aka kwashe da dariya, Mami tace
"Ni dadina dake Basma tsamin baki kinga Ihsan nan har tafi ki iya magana"
Ta juya alamun fushi tace
"Da na shiyo miki shweet amma na fasha tunda kina shokanata" ta karasa tana nuna mata sweet din.
Gaba daya aka qara kwashewa da dariya, banda Mami da tace
"Kai ku dena yi mata dariya mana, yi hakuri kinji yar jikalle ta"
Sai a nan ta saki murmushin da tsantsan kamarta dasu Heenad ta bayyana.
Mami ji take kamar ta hadiye su don so, ba'a juma ba Daddy ya dawo ganin jikokinsa yasa ya saki murmushi. Ko hutawa baiyi ba ya kwashe su suka tafi siyen ice cream da kayan lashe lashe da tande tande na yara.
Sai dare Adnan yazo daukarsu.
* * *
Adnan ne zaune shida Khalil a falo suna kallon ball, can Adnan ya kalli Khalil yace
"Wai nikam me su Khadija keyi a daki ne har yanzu basu fito ba?"
Khalil yayi murmushi
"Kasan mata da..."
Kafin ya karasa sun fito cikin shiga iri daya, sun kara yar kiba, suka karaso suna murmushi suka tsaya gabansu Adnan.
Heenad ce ta soma magana.
"Ga wasa kwalwa nan muna so kowa ya nuna matarsa a cikinmu"
Tabbas yadda sukayi shigar bamai ganesu, don kuwa sanye suke cikin baqar after dress iri daya sai suka dora abaya yar karama daidai kafada kalar toka.
Adnan da Khalil suka miqe suna dariya
"Kaji min wadannan matan wai ace mu kasa gane matanmu, bari kaga"
Ya ja daya Khalil ya ja dayar, suna murmushi suka ce mun gama zaba idan kun isa kuce bamuyi daidai ba.
Khadija ta kwashe da dariya tana kallon Adnan tace
"Subhanalillah Heenad ce kaja fa ba Khadija ba"
Ya sake ta da sauri yana kallonta da kyau can yace
"Wallahi Khadija ce ba Heenad ba"
Kafin ta kara cewa wani abu ya ja ta daki yana fadin.
"Tunda na canko ki na biki bashin yaya goma tagwaye kuma kamar ki"
Ta zaro ido tana fadin
"Rufa man asiri wallahi bazan iya ba"
Yayi dariya
"Au haka kika ce bari kigani kuwa"
Ya biyo ta zai kamota ta zille, ta fara zagaye dakin yana binta, daga karshe yayi nasara ya chafko ta yana dariya, kan gadon suka zube suna maida numfashi, sannan kuma ya miqe ya kamota ya rungume ta sosai yana fadin"
"Khadija Allah yayi miki albarka, hakika samun mace da gari kamar ki sai an tona, ina alfahari da ke sannan kuma yau naga ribar biyayya ga iyaye, Alhamdulillah, yaranmu suna samun ilimin addini duk a sanadiyyar uwa ta gari da suka samu sam baki wasa ta fannin addininsu naji
dadi sosai"
Ta rungumo shi sosai tace
"Haba Abban Afra da Haifah ai kaima ka bada taka guddumar wajen ganin sun nemi ilimin, don haka bani kadai na chanchanci yabo ba hadda kai"
Ya kara matseta jikinsa
"Haka ne i love you so much Baby Allah ya hada mu a aljanna"
Tace "i love you too, Allah ya barmu tare ya kare mu daga sharrin mutum da aljan, Allah ka dauwwamar mana da farin ciki na har abada,"
Ya ce "Amin ya Rabbi bana fatan Allah ya nuna min ranar rabuwar mu"
Tace "nima haka mutuwa ce zata rabu insha Allah"
ALHAMDULILLAH!!!
Godiya ta tabbata ga Allah (SWT), Allah na gode maka da ka nuna min karshe littafina ma suna TAGWAYE NE? lafiya, kuskuren da nayi Allah ya yafe min, wanda na bata ma rai ya yafe min Allah ya yafe mana gaba daya.
GODIYA TA MUSAMMAN GARE KU SISTERS
Ayusha
My sister Bilkisu Ammani
Ashkd
Kdey
Fatima Muhamad Mansur
Zainab Bapullo (zee bee)
Faty ladan
Maryam Gafai
Asma'u Ammani
Hauwee Bash
Maman Khaleel
Fiddausi Abubakar
Meesha luv
Rash kardam
Asma'u Isa
Maman Nabeel
First lady
Hafsat Bashir
Jigama
Halima garko
Summaya gerei
Fatima muhammad bashir
OMG AND SO MUCH, bazan iya karasa lissafa masoyan book dinnan ba saboda kunada yawa Allah yasaka muku da alkhairi duk ina sonku๐
Dole na gode muku all members na
Rash kardam novels
Dandalin meesha lurv
Lovely fans
Talented writer's group
Hausa novels
Hausa novels na Faty muhammad
Hausa novels na chuchu
Khaleesat haydar novels
Mu sha karatu
Kiddies frnds forever
Ina mika godiyata ga duk wanda ya karanta Tagwaye ne nagode nagode! Duk wanda na kira da wanda ban kira ba duk ban manta da ku ba ina sonku duka❤️
My Books
KOMIN NISAN DARE
HAIFAH
TAGWAYE NE?
Sabon yana nan tafe insha Allah.
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
No comments:
Post a Comment