ππππ❤
ππππ
ππ
π
MSBπ
maryamsbellowo.wordpress.com
*πTagwaye ne? π*
50
Basu suka iso ba sai qarfe biyar na yamma, suka ajiye su Heenad gida, bakery ya biya ya yi musu ordering pizza.
Bayan sallar isha'i Khadija na tsakar ciren kayan jikinta zata shiga wanka Adnan ya shigo da sallama, yana sanye da jallabiya kalar ruwan toka, cike da kunya tayi saurin rufe jikinta. Ya karaso yana kallonta yace.
"Baby kunya kuma? Lallai ashe ban gama cire kunyar nan gaba daya ba kenan?"
Ta zaro ido waje tace
"A'a fa"
Yayi murmushi yace
"Wai ni har yanzu banji kin kira sunana ba? Kullum sai kiyi ta 6oyewa ko?"
Tayi murmushi cike da kunya tasan gaskiya ya fada.
Ya kuma kallonta
"To gaskiya a yau dinnan sai naji sunana a bakinki idan kuwa ba haka ba nine zan miki wanka yau"
Ta zaro idanu waje tana fadin
"A'ah..."
Yace "oya ke nake sauraro"
Ta juya masa baya tace.
"Ya Adnan"
Ya lumshe idanu sai yakeji kamar duk duniya ita kadai ta iya kiran sunansa, yayi dariya mai bayyana haqora.
Cikin shagwa6a yace
"Ni gaskiya sunan nan bai mini ba a chanza"
Ta soma kukan shagwa6a don ita kam in banda wannan sunan batajin zata iya kiransa da wani.
Ya daure fuska
"Aikuwa yau ni zan miki wanka idan baki kira ba"
Ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana murmushi ciki ciki.
Yace "ina jiranki fa"
Tace "to 'yalla6ai fa?"
Ya kyalkyale da dariya harda buga cinyarsa da hannunsa, sai da yayi mai isarsa sannan ya dago yana dubanta da tuni idanunta sun kawo ruwa. Ya miqe da sauri tare da dafo kafadunta.
"Haba My angel, daga wasa sai kuma kuka?"
Sai tayi dariya mai hade da kuka tana 6oye fuskarta a cikin qirjinsa.
Yayi murmushi hade rungumo ta.
"I am sorry ok? Wasa nake miki basai kin kirani da wani suna ba duk wanda yayi miki ki kirani da shi kinji?"
Bata san lokacin da tace
"Hubby ya maka?"
Ya lumshe idanu yana kallonta yace
"Yayi my Baby jekiyi wankanki, amma na biki bashin wankan"
Ta shige da sauri hade da rufe kofar da lock, tana murmushi.
Bayan ta fito ta sanya kayan baccinta kalar ruwan qasa, ta dora hijibi, sallamarsa ta kuma ji, ta jiyo suka hada ido ya sakar mata murmushi. Itama ta maida masa, baice komai ba, illa hannunta kawai yaja suka fito, dakinsa taga ya nufa ya zaunar da ita kan gado, wardrobe dinsa ta jikin bango taga ya bude, sai kuma taga ya shiga jawo akwatina masu kyau set hudu da dan kit, ta kalle shi cikin rashin fahimta tace.
"Wannan fa?"
Yayi murmushi
"Kayan dannar kirji ne kishiya zan miki"
Ta 6ata rai tare da juyar da kanta ta bashi baya, yayi dariya kasa kasa, ya zauna hade da rungumo ta, ta fizge jikinta, ya kamo hannunta ta kuma fizgewa, qarshe ma tashi tayi zata bar dakin ya fizgota ta fada jikinsa. Hawaye ya gani a fuskarta, ya shiga goge mata.
Ya juyo da fuskarta ya soma magana.
"Kwantar da hankalinki Baby, ai ke kadai ce a zuciyar Adnan you are my one and only insha Allah, ba zancen kishiya tunda naga kina tsoronta" ya karasa cike da zolaya
Kunya ya kama Khadija, kamar qasa ta bude ta shige ta ke ji, ya kamo ta yana dariya sosai.
"Ashe dai ana sona?"
Ta fara sunna kai, hannunta ya kamo yace
"Wannan naki ne na siyo miki dama ba'ayi miki lefe ba, to wannan shine tukuicin qaunata a gare ki"
Da kansa ya bubbude mata kayan, su atamfofi ne da leshi su material, da English wears nan da suka fi yawa, kayan kwalliya, cosmetics da costumes, da takalma da jukkuna kala kala, kasa magana tayi nan ta rungume shi tana hawayen farin ciki.
* * *
BAYAN SATI BIYU
To haka dai rayuwar ke gudana cikin hukuncin ubangiji, da rana Khadija na kicin tana girki wayarta ta fara ruri, ganin mai kiran yasa ta dauka tana murmushi.
Cikin muryar farin ciki Heenad tace
"Khadija na samu admission a Turkish Nile Pol Science na samu kefa?"
Cikin murna hade da mamaki Khadija tace
"Haba? Aikuwa ban duba ba bara idan na duba zan kiraki"
Daga haka sukayi sallama.
Ko minti sha biyar ba'a cika ba Adnan ya shigo, kicin din ya same ta tana zuba abinci a kula, bakin kofa ya tsaya ya hade hannuwansa wuri daya yana murmushi, kamshin turarensa taji ta juyo cike da mamaki tace.
"Har ka dawo?"
Yayi murmushi yace
"Albishirinki!"
Ta kalle shi da alamar tambaya tace
"Goro"
Yace "ki chanka mana"
Tayi shiru tana tunani, amma bata dago komai ba.
Yayi dariya
"Karanta wannan"
Ta kar6a jikinta na rawa. Bata san sadda tayi ihun murna ba hade da maqalqale shi tana dariya.
Sai kuma can ta sake shi cike da kunya tana kallon qasa. Yayi dariya
"Congrats Baby Allah ya baki sa'a yadda kika fara karatunan Allah yasa ki gama lafiya"
Cike da murna tace "amin"
Da sauri ta karasa girkin, wayarta ta dauko ta kira Heenad bugu biyu ta dauka.
Tana dauka kuwa ta sanar da ita, nan suka hau murna ta cikin waya.
Heenad ta tsagaita tace
"Me suka baki?"
Tayi dariya "Computer Science"
Heenad ta cika Khadija da ihu har sai da ta toshe kunnenta tana dariya.
Bayan sunyi sallama Khadija tsai tayi tana nazari can kuma ta furta a fili
"Wai yau nice zan je jami'a ikon Allah kenan, ashe inada rabo?"
Ba zato taji an rungumo ta ta baya
"Kina ja da ikon Allah ne?"
Ta girgiza kanta da sauri
Yayi murmushi ya jawo hannunta, dinning suka nufa, da kanshi ya zuba mata abincin ya soma bata a baki....!
Maryam S belloπ
No comments:
Post a Comment