YAR AGADEZ
{Page 02}
Kallon Abba tayi tana cigaba da kuka tare da dukewa kasa, Ashraf ne ya tako daf da Abba yace still in shock of the slap, "Abba ka mareni akan wannan? Abba ka tuna cewa fa ni danka ne koba komai kai kanin mahaifina ne wanda ya rasu shekarun baya da suka wuce, banida kowa sai ku sai Allah mahaifiyata ta rasu bayan mahaifina ya rasu, kuma kafin ya rasu shine ya fara taka wannan matsayin da kake takama dashi a yanzu, Abba ka zauna kayi tunani kar ka cutar da yarka kwara daya tak da Allah ya baka ka bari ta zabi wanda takeso kar kuyi mata auren dole tana da wanda takeso..." Abba ya daga masa hannu "Meyasa kake tunatar dani abinda na riga da nasani tun tuni? Nasan matsayinka a gareni saidai tunda Umma ta riga tayi maganar nan babu yadda zamuyi... kuma da kake maganar tana son wani waye shi? A iya zamana da Hoodah ban taba ganin tana soyayya dawani ba..." Ashraf yayi murmushi mai ciwo "Hakane Abba bakasani ba saboda baka damu da yarka ba ko? Bakasan me take ciki ba baka bata kyakkyawar kulawar da mahaifi ya kamata ya baiwa yarsa..." Umma ta daka masa tsawa "kaga Ashraf ka rufewa mutane baki a nan idan manya na magana yara basa saka masu baki wannan wace irin rashin tarbiyya ce da rashin sanin ya kamata?" Ashraf ya kalleta da idanunsa suka sauya kala sannan ya kalli Abba ya kamo hannunsa yace "Abba mun kasance mun shaku da juna nida kanwata Hoodah, a sanadiyar haka zukatanmu suka kamu da soyayyar junansu Abba a yanzu haka dama mun yanke shawarar sanar dakai halin da ake ciki....." Umma tace "A gidan ubanwa zaka auri Hoodah? Toh bari kaji in gaya maka ko kaine Romeo na duniya bazaka auri Hoodah ba..." abba yace "Kaga Ashraf tunda kaga Umma bata amince ba kawai a bar maganar nan banason tashin hankali..." Umma tayi shewa "Kadai ji da bakinka yanzu? Don haka tun wuri ka fitar da ita daga ranka tun kafin wanki hula ya kaika dare." A hankali ta kewaye jan idonta daya kumbura ta yunkura ta mike da kyar tana duban Abbanta daya dukar da kansa zuwa kasa yana kallon carpet tace "Kana jinta Abba? Auren dole fa Abba. Abba please kasa baki Abba kar ka bari a mun auren dole yaya Ashraf nake so please help me Abba." Aunty Rahanatu ta soma janta da karfi tana tirjewa amma rikon da ta mata ji take kamar zata balla mata hannu nan ta hakura da tirjiyar sannan tabi bayan Aunty Rahanatu dake janta da hannu. "Ku bamu waje..." aunty Rahanatu ta fadawa bayin dake binsu har daki take suka fita suka kulle kofa, suna zuwa Hoodah ta zube kasa ta kara fashewa da matsananci kuka mai ban tausayi jikinta har wani rawa yakeyi, hugging dinta Aunty Rahanatu tayi tana fadin "Shhh... everything is going to be okay InshaAllah." Cikin sheshekar kuka tace "No it's not! It's not going to be okay, kina ganin abinda ake shirin aikata mun? Za'a cuci rayuwata a mun auren dole abunda aka daina yi tun zamanin iyaye da kakkani shine ni za'ayi mun why me? Ta dasawa mahaifiyata bakin ciki kala kala kafin ta bar duniya bata gamsu ba shine ni zata dawo kaina? Ita ba Allah bace ba zata zo tayi deciding abinda zai faru da mutum ba she can't! Kaddarata ba'a hannunta take ba bazata zo kawai ta aurar da ni da dan sarkin Niamey ba, banma sansa ba, bansan halinsa ba, ba'ayi min adalci ba..." ta fada muryarta na kakakarwa hawayenta na tabo lips nata. "Hoodah..." ta fada cikin sigar rarrashi, "Akwai abubuwa da yawa da zasu iya faruwa da rayuwarmu Allah zaki ba zabi ba zabin ranki ba, idan wannan auren alkhairi ne ki karba hannu bibbiyu sai kiga wanda kikeso din ba alkhairi bane a gareki na tabbatar maki Allah zai sa maki albarka a ciki..." ta dago da jajayen idanunta tana kallon Aunty Rahanatu "Kema side din su Umma kike?" Aunty Rahanatu tace "Ko kusa ba side kowa nake ba, kawai ina tunatar dake zabin Allah ba naki ba, bakisani ba ko Ashraf ne alkhairi ko kuwa yariman Niamey, just have faith in Allah ki bar komai a hannunsa InshaAllah komai zaizo cikin sauki InshaAllah..." girgiza kanta ta shiga yi, "Bazan iya bari hakan ya faru ba, ya kamata kuyi wani abu a kai bazata iya making decisions ba anyhow akan mutum ba..." ta tura kanta cikin cinyarta tana cigaba da kuka "Babu abinda zamu iya yi a kai ke kinsan halin matar nan sarai yayah Jalal ma bai iyawa da ita balle kuma mu a suwa? Kedai kawai ki mika lamarinki ga Allah shine zai share maki hawayenki InshaAllah khairan ne..." Hoodah tace "Idan ba shi bane bafa?" Ta sakar ma Hoodah da murmushi "Bazai faru ba trust me, idan har kikasa Allah a ranki InshaAllah komai zaizo da sauki..." shiru dukansu sukayi still tayi hugging din Hoodah na cigaba da kuka a hankali, bayan ta gaji da kukan nata tayi shiru. "kina bukatar hutu Gimbiya, ya kamata kije ki kwanta kada kanki ya fara ciwo..." Hoodah tace "Naji amma shi yaya Ashraf waye zai rarrashe shi kamar yadda kika rarrashe ni?" Aunty Rahanatu tayi murmushi tace "Karki damu zanje na same shi kedai ki tafi kiyi wanka ki huta kinji?" Ta gyada kai ta yunkura da kyar tana hade hanya ta fita daga dakin, Har yanzu Umma na nan parlor tana magana kasa kasa da jakadiya, Abba da kaka basu nan yanzu, ko kallon inda suke batayi ba ta wuce dakinta da sauri tasa ma kofar lock, bathroom ta fada tayi wanka ta dade ciki ta dauro alwala ta fito ta gama shafe shafenta ta saka loose gown ta lace tayi kyau, sallaya ta shimfida ta saka hijab dinta ta fara sallarta a natse har yanzu zuciyarta bata mata dadi, cikin sojood takai kukanta ga Allah mai kowa mai komai har saida taji idanunta suna neman kafewa, zuciyanta wani irin zafi take mata da radadi, bayan ta idar ta mike a hankali nan taga wayarta na haske Ashraf tagani yana kiranta gefen gadonta ta zauna ta saita kanta ta dauka "Yaya Ashraf..." ya saki ajiyar zuciya "Ina fatan Gimbiyar tawa ta bar kuka?" Duk da tana cikin yanayi saida ta saki murmushi tace "Na daina...." yace "Yawwa, kinga yadda al'amarin ya juye ko? Abinda nakeso dake karki sa damuwa a ranki mu bar wa Allah kar mu tursasa, zabin Allah shine zabin mu..." tace "Nasani nagode da kaunarka gareni yaya Ashraf bazan taba daina sonka ba har karshen ruyuwata ba..." kwalla suka cika masa idanu ya hadiye abu da kyar yace "Nima haka Gimbiyata kece zabina idan har inada iko, saidai dole muyi biyayya ga Abba sannan kuma mu barwa Allah zabi..." ta lumshe idanu, shiru ya biyo baya Ashraf yace "Kizo na kaiki favorite place dinki..." tayi murmushi mai sauti "Gani nan zuwa...."
Ta gaban Jakadiya suka gifta itada Ashraf wadanda suke hira a natse daga gani kasan suna tafe cikin nishadi sai kace wani abu bai taba faruwa ba dazu, rike baki tayi cike da mamaki tuna maganar da sukayi da sarauniya cewar tasa ido idan har taga Gimbiya tare da Ashraf toh tayi gaggawar sanar da ita, cikin hanzari tayi cikin harabar Sarauniya tana zaune bayi biyu ko wace tana mata tausa a kafa daya daya, jakadiya ta shigo kamar an aiko ta, Sarauniya ta daka mata tsawa "Lafiya zaki fado man a kai haka?" Jakadiya ta zube kasa gwiwwa biyu biyu tana bada gaisuwar ban girma "Ranki shi dade ayi man aikin gafara amma yanzun nan naga Gimbiya da Ashraf suna tafe zasu fita tare..." hankade bayin nata tayi dake ta faman yi mata tausa har saida suka fadi tim sannan ta mike tsaye tace "Kika ce mey? Maimaita naji!" Tace "Ranki shi dade nace yanzu naga Gimbiya da Ashraf suna tafe zasu fita ta..." bata karasa magana ba kawai Sarauniya ta fita da sauri hakan bai hana Jakadiya da bayinta binta ba da hanzari, mai martaba yana tattauna da waziri da sauran mutanensa kawai ta fado masu babu ko sallama, hakan yasa kowa na wurin ya dago yana dubanta, ba tare data kallesu ba tace "Privacy! Zanyi magana da mijina..." a take kowa ya fita sannan ta kalli mai martaba tace "Idan har na isa ga Hoodah kuma idan har ana daukata da mahimmanci toh inaso kazo muje ka tsaida Gimbiya da Ashraf kayi masu kashedi kar na sake ganinsu tare tunda yanzu tasan cewa bada ita za'ayi!" Ya mike da hanzari har yana neman tuntube yace "Ina suka tafi?" Tace "Kaima kasan inda zasuje...." yace "Muje...." tare da bayi biyu suka tafi sai sauri take zubawa kamar zata tashi sama. Zaune suke bakin ruwa sun zuba kafafuwansu cikin ruwan itada Ashraf suna hirar soyayya, Ashraf ne yace "Yawwa Gimbiyata wallahi naji dadin yadda kika yi saurin sakin jikinki baki ji yadda nakejin dadi ba..." tayi murmushi "Toh ay idan ina tare da kai bana jin wani bacin rai a tare dani." Yace "Nasani Gimbiyata nima ay hakane a wuri na." Tayi dariya ba zato taji an fizgo ta da karfi cikin tsoro ta juyo kawai suka hada ido da Sarauniya sai suka mike da sauri Ashraf yace "Lafiya?" Wani wawan mari Abba ya dauke Gimbiya dashi har sai data daina ji na minti biyu, zai kara kai na biyu Ashraf yayi sauri yasha gabanta hakan ya dakatar da Abba sannan yana huci yace yana nuna su da yatsa "Daga yau na sake ganinku tare sai na dauki mataki akan haka, kinsan aure za'ayi maki meyasa zaki tsaya dawani?" Ta dago tana kallon Abba tace "Abba meyasa kake bari matar nan tana cin galaba a kanka? Tana so ta watsa maka family dinka kai baka gane ba Abba please ka zauna kayi tunanin abinda kake shirin aikatawa...." ya daga mata hannu "Ba abinda zan zauna nayi tunani a kai nadai fada maku daga yau kar na sake ganinku tare!" Sarauniya tayi dariya "Toh kun dai, wai shin soyayyar dole ce? Ku hakura da junanku mana, idan kunne yaji?" Abba yace "Jiki ya tsira." Sarauniya ta jawo Gimbiya da karfi wadda ta kafe da kyar take janta tana tirjewa, Abba ya kalli Ashraf kaima muje..."
BAYAN KWANA BIYU.
Tana dakin Kaka da yamma, Kaka ta kalli Hoodah tace "Abincin ya maki dadi?" Hoodah ta kalli plate din ko ci batayi ba tayi yake tace "Eh." Kaka tace "Nasani, ba'ayi maki adalci ba ko kadan, amma kar ki sake kiyi wasa da cikinki Gimbiya kar ciwon yunwa ya kamaki..." ta kakalo murmushi "Abba ya daina sona kaka laifi na yake gani saboda nace bazan yarda ayi mun auren dole ba kuma kinsan ba laifi na bane sai na waccan evil matar, tunda ta shigo gidannan rayuwarmu ta juya daga farin ciki zuwa bakin ciki, na tabbatar da Abbana bai aure ta ba da yanzu ba haka rayuwarmu take ba, Amma Allah ya kadarta hakan sai ta faru babu yadda muka iya...". Kaka ta numfasa cike da alhini "Nasani Gimbiya, saidai duk da haka mahaifinki ne, ki daina fadin haka ba'a ja da hukuncin ubangiji..."
Hoodah tace "Kaka kinfi kowa sanin yadda ya koma yanzu, da Abbana mutum ne shi wanda ko wace y'a take burin samu a matsayin mahaifinta, saidai kash banda yanzu bond din da mukayi sharing da Abbana yanzu babu shi he only care about that monster of a wife..." Kaka ta dafata "Addu'a kadai itace mafita, ki daina tuna baya..." Hoodah tace "Ta ya zan daina tuna baya karki manta a sanadiyarta Ammina ta rasa ranta saboda mugun halinta, wani tabo ne da bazai taba gogewa ba a cikin raina ya riga ya zama permanent scar, lokacin ban wuce shekara shiga naga kisan mahaifiyata da idona cikin dare da misalin karfe sha daya na dare, muna kwance daki sai mahaifiyata ta tashi da niyyar shiga bayi, toh naji motsinta nima sai na farka sai na tashi na daga labule me zan gani? Kawai naga Umma da katon dutse ta bayan katanga saida ta saita daidai inda Ammina take kawai ta jefa mata shi gaban idona Ammi ta zube jini yana fita ta hanci ta baki ta kai, hannunta da kafarta duk ya kurje, kaka girman dutsen nan zai kai katon block na fasa ihu ashe ita kuma ta gudu ba wanda ya ganta nan nayi kan Ammi ashe ta tafi... kamar ta rufewa kowa baki ba wanda yayi yunkurin daukar wani mataki akai...." Kaka tace "Kwarai kuwa duk nasan da haka abinda ta aikata zata jira sakamonta tun a nan duniya, ay matar nan saidai mu bita da addu'a don ta riga ta gama da Jalal..." Hoodah tace "Yanzu yana ji yana gani zai bi umarninta? A aurar dani?" Kaka tace "InshaAllah komai zaizo da sauki maganar auren nan idan har ba alkhairi saikiga baza'ayi shi ba, Allah yayi maki albarka, ya kareki daga dukkan sharri..." tace "Ameen." A hankali ta kwanta bisa cinyar kaka ta lumshe idanu...
*****
"Assalam Alailkum..." ya fada yana sa kansa cikin harabar gidan nasu, "Wa'alaikumusalam." Abbi ya mike yana fadin "Sultan...!" Yace yana murmushi sosai "Nine Abbi..." Abbi ya jawo shi yayi huggin dinshi yana faadin "MashaAllah ka samu sako na kenan? Na cewar ka dawo ina nemanka...." Sultan yace cikin hausarsa mai kama da larabci yace "Na samu Abbi sheyasa na dawo da gaggawa." "MashaAllah toh ya hanya?" Yace "Alhamdulillah Abbi na same ku lafiya?" Abbi yace "Alhamdullah ya Madinah? Wato kafi son zama can daga tafiya karatu kuma shikenan tunda ka gama sai kaki dawowa? Bakaso kazo ka tayani mulki ko?" Ya saki murmushi da ya bayyanar da ainahin kyawunsa "Ba haka bane Abbi wani abu ne ya rike ni acan din..." Abbi yace "That's alright mu tafi wurin Umminka ka gaishe ta..." Tare suka shiga harabar mahafiyar tasa Hajiya Batula wacce ke zaune tare da bayinta suna gadinta tana ganin Sultan ta mike da sauri cike da murnar ganinsa sukayi huggin juna "Barka da dawowa Yariman Niamey, ka chanza ka kara kyau, tsawo ka kara girma my son..." ta fada tana taba masa sajensa da ya kwanta luff yana kyalli, "Kai Ummi ban wani chanza ba shekaru biyu ne kawai rabona da gida." Ta dan make shi da wasa "Shekara biyu ba kwana biyu bane..." kowa ya kyalkyale da dariya, dukawa sosai yayi ya gaishe da mahaifan nasa suka amsa da fara'a, daga nan dakinsa ya tafi yayi wanka ya watsa ruwa ya fito ya ci Abinci. Kwanansa biyu da dawowa ya huta sosai kullum yana hawan doki, farauta ko fishing.
Yau kwanansa uku ya shirya tafi gidan abin. kaunarsa Khairi tunda ya dawo bai nemeta ba don haka yaga rashin kyautawarsa kwarai. Bayan ya isa gidansu Khairy yasa aka kirata tana fitowa ta gansa sai ta hade rai ta juya masa keya, dogarawansa yayi ma alamar da su bashi waje take suka tafi, yayi murmushi "Khairy naga kamar bakiyi murnar gani na ba ko?" Ta zumburo baki tace "Eh ay kwananka nawa sai yau zakazo??" Yace "Afuwan wani abu ne ya rike ni amma kiyi hakuri..." tace "Babu komai toh na yafe maka, ka shigo daga ciki Mama ta aje maka abinci da fura..."l gyada kai yayi ya bita ciki yana murmushi.
WASHE GARI
Yana dakinsa aka aiko masa da kiran mai martaba yanzu, mikewa yayi ya fito ya nufi harabar mahaifinsa nan ya iske Ummi itama a nan, ya zube ya gaishe su suka amsa da fara'a Abba ne ya soma magana "Dama dalilin daya sa nace ka baro madina kazo ina nemanka shine... munyi magana mun tattauna da sarkin Agadez shine muka yanke shawarar hada ka aure da yarsa Gimbiya Hoodah....!" A razane ya dago bashi ba harta Ummi saida ta razana jin abinda Abbi yace da sauri tace "Aure kuma mai martaba? Dalili da mey zakayi mashi aure da rivals dinmu? Meye dalili?" Abbi yayi shiru na yan dakikai can yace "Rivals nada ba? Ay yanzu komai ya rigada ya wuce? Nidai sun aiko man da sako cewar ga bukatarsu kuma na amince da hakan!" Ummi tace "Toh da ka amince ita Khairy yayi yaya da ita? Duk garin nan waye baisan yarima da Khairy ba? Anya kayiwa danka adalci kuwa mai martaba?" Ya numfasa "A matsayina na mahaifin Sultan bazan yarda na cutar da dana ba don haka kuyi addu'a idan akwai alkhairi a ciki...." Sultan ya dago da kansa ke duke ya kalli Abbinsa da shock cikin idonsa ya girgiza kai "Abbi why? Meyasa zakayi man haka? Khairy nakeso kowa yasani meyasa za'ayi mun auren dole?" Abbi yace "My decision is final!" Daga haka ya mike ya bar harabar ya nufi waje inda Ummi tace a zuciye "Shikenan tunda haka ya xaba mu zuba nida shi ko wacece ta shigo wallahi sai ta gudu da kafarta don haka ka kwantar da hankalinka indai ina raye bawanda ya isa yasa ka zauna da wacce bakaso....."
1 comment:
Ohh ikon Allah,hoodah ko Ina bbu Dadi kenan.
Allah yasa dai ammi ta canja a kudurinta.
Post a Comment