YAR AGADEZ
{Page 26}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
A gigice sukayi kanta babu abinda Mama keyi in banda rusar kuka, don dole aka bata gado aka sa mata drip nan Mama ta kira Baba ta sanar masa an kwantar da Khairy idan yazo zatayi masa bayanin komai, nan Mama ta zauna gefen gadon tana share hawaye, tashi tayi jin ana kiraye kirayen sallar magrib ta nufi bathroom ta dauro alwala ta gabatar da sallah, tana zaune nan har akayi sallar isha'i ta tashi tayi tayi sallah, tana gamawa ta zauna a nan ta cigaba da azkhar dinta, tana nan a haka aka tura kofar aka shigo da sallama Baba ne yana dauke da ledoji Mama ta amsa sallamarsa ya aje ledojin a gefe ya nufi gadon Khairy har yanzu bata farka ba, ya dan dade a haka yana kallonta kafin ya kalli Mama yace "Ya jikin nata?" Mama tace "Da sauki bata farka ba har yanzu." Yace ok ya dawo gefen Mama bisa kujera ya zauna yace "Nasan kina tare da yunwa ga abincin nan na kawo maki..." Girgiza kai tayi take ta fashe da matsanancin kuka harda shesheka yayi shiru yana kallonta can ya numfasa "Komai kikaga ya samu bawa mukkadari ne daga Allah Turai, yanzu ba lokacin kuka bane ba, yanzu meye akace yana damunta har ta fadi haka?" Ta samu da kyar ta tsaida kukan nata tace "Malam tun ba yau ba nake fadan yawon Khairy amma bataji dama hausawa sunce ka haifi yaro ne amma baka haifi halinsa ba, Malam Khairy harda kanjamau ta kwaso ma kanta..." ta fada cikin gunjin kuka, salati Baba yayi cike da tashin hankali yace "Innalillah wa inna ilahir rajioon Allahumma-jurni fi musibati, wa akhlif li khairan minha, Allahumma Indaka Ahtasibu Musibati Fa’jirni Fiha Wa Abdil li Khairan Minha, Allah kayi mana maganin abinda yafi karfinmu, kiyi hakuri nasan da ciwo amma babu dadi amma haka Allah ya kaddara mana babu makawa sai ya faru, babu yadda muka iya saidai mu rungumi kaddara hannu biyu, kisani wannan jarabta ce..." bai karasa rufe baki ba sukaji mutsu mutsun Khairy da sauri suka nufi bakin gadon suna kallonta, idonta a rufe take fadin "Ni keda kanjamau? Ni nasan boka ne yasa man ba kowa ba, in bashi bane toh wadannan ne da sukayi man fyade! Mama da Baba ku yafe mun wallahi sharrin shaidan ne duk dan in raba Yarima da matarsa garin yin hakan naje na jawo kaina, naja maku abin kunya abun fadi, na kuma goga maku bakin fenti akan wata soyayyar da bata amfeni ba saima ta jefa ni cikin masifa... boka naje na sallamawa kaina yanzu ga irinta nan, na cuci kaina na jawa kaina..." sai kuma ta fashe da kuka, duk mutuwar tsaye su Baba suka yi, kasa tsayuwa Mama tayi nan tayi taga taga zata fadi Baba ya taro, kuka ta fashe da shi wane ranta zan fita "Abinda Khairy take fada gaskiya ne ko dai sambatu takeyi? Kuce man ba gaskiya bane!" Ta kara fashewa da kuka, farkawa Khairy tayi ta bude ido tangaram tana farkawa ta fara kokarin mikewa daga kan gadon, saida tayi tozali dasu Mama sannan ta ja baya ta jingina da bango ta rakube Mama tace "Khairy abinda kika fada gaskiya ne ko ba gaskiya bane? Wai wurin Boka kika je harda sallama masa kanki?" Baba yace "Kiyi hakuri Turai yanzu ba lokacin da ya kamata ki fara mata wadannan tambayoyin bane, ki danne zuciyarki har muje gidan sannan." Kuka Mama ta cigaba da yi zuciyarta na tafasa, ita kuwa Khairy tsit tayi tama kasa koda kallonsu. Sai can wajen karfe goma Doctor ya shigo nurse na biye dashi a baya, "MashaAllah patient namu ta farka, how are you feeling now?" A hankali tace "Alhamdulillah." Bude file dinta yayi yana rubuce rubuce "Kamar yadda na fada maku a baya ku gaggauta sanar da mijinta yazo yayi gwajin nan don a gani ko bai dauke da wannan cuta," ya kuma kalli Mama dake share hawaye yace "Hajiya kiyi hakuri wannan cuta ana shan magani kuma kiga mutum yana living normal life dinsa, ita dai kawai sai an daure an dinga zuwa karbar magani, kuma sai ta dinga kula da kanta...." Baba yace "Toh Doctor abinda nake so in tambaya shine shi yaron dake cikinta zai kamu da wannan cuta?" Yace "Ba lallai bane, saidai idan an haife shi za'a iya gwada shi agani, sannan kuma kanku sai kunyi taka tsantsan kunsan fa ba dole sai ta hanyar jima'i ake dauka ba, yanzu misali idan ta yanke akaifa da reza sai ta yanke jini ya fito wani daga cikinku ya dauka a haka yayi amfani dashi toh zaku iya dauka, sannan amfani da allura daya wajen daukar jini ma yana sawa kamuwa da wannan cuta, abubuwan dai gasu nan zan maku karin bayani InshaAllah, sannan zata fara shan magani babu bata lokaci sannan zata dinga zuwa ganin likita don kula da ita kanta lafiyar tata tare da abinda ke cikinta, da fatan kun fahimta?" Suka gyada kai, yace "Da safe zan sallame ku don naga ta farka kawai za'a ajeta for observation, duk zan rubuta mata maganin da zata dinga amfani dasu sannan don Allah kar a manta a kawo mijinta a gwada sa." A sanyaye suka amsa sannan ya bata medication ya fita, nan sukayi jugum jugum babu wanda ya iya koda kwakkwaran motsi.
Haka kuwa akayi sai da safe wajen karfe sha daya na safe aka sallameta, Doctor din ya masu kwakwaran bayani da kuma magungunan da zata dinga sha, a haka suka tafi gida, a sanyaye kowa yayi jugum suka shiga cikin gida, nan Mama ta sa tayi wanka ta bata abinci da magani, kafin Khairy ta basu labari kaf abinda ta aikata, tana magana tana kuka Baba ya numfasa "Hausawa sunyi gaskiya Ummalkhairy da sukace in zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere in ba haka ba kaine zaka fada ciki, yanzu ina so ki fada man wace riba kika samu a duk abinda kika aikata? Nothing right? Babu abinda kika samu sai tarin wahala da bakin ciki da dana sani, yanzu ke akan namiji kika aikata duk wannan abun? Kece kulla mata sharri, kece bin boka, kece this kece that, wannan wace irin rayuwace kika daukar ma kanki? Yanzu wa gari ya waya? Yanzu ita Gimbiya da kikayi ma haka tana nan gidan mijinta bai rabu da ita ba tana nan daram, ke har kin isa ki wucewa hukuncin Allah? Allah ya kaddara bazaki aure shi ba amma kika kafe yanzu gashi nan, inda ace ke ta kirki ce Ummalkhairy da tun lokacin hakuri kikayi sai kiga kina zamanki Allah ya kawo maki chanji mafi alkhairi wanda zaki ji dadinshi, amma duk bakiyi ba, Nidai yanzu ina maki fatan wannan ya xama izina a gareki da duk masu aikata hali irin naki, kisani Boka ko Malami basu isa su baki abinda kikeso ba, babu wanda zai baki Allah kadai xaki roka ya baki ba wani boka ba ko malami, kinsan hukuncin wanda yayi shirka? Kin cuci kanki, kin kuma cuce mu Khairy amma ni bazan tsine maki ba addua zan maki yasa wannan shine sanadin shiryuwarki ya yafe maki kuskurenki, ki daure ki koma islamiyya inda ace kinada ilimin addini sosai da wani abun ma bazaki fara aikata shi ba, rayuwa da duk abinda ke cikinta a hannun Allah take don haka ki cigaba da istigifari sannan ya zama dole ki nemi gafarar wanda kika cuta, ki natsu Khairy ki daidaita rayuwarki kisan annabi ya faku, wallahi duk abinda ka shuka zai dawo maka ko alkhairi ko kuma sharri, da fatan kinji abinda na fada maki? Allah ya shiryeki ya saukeki lafiya ya baki miji na gari, inaso ki fita rayuwar su Yarima ki ji da taki rayuwar ki kyalesu suyi rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da natsuwa, Allah shi kyauta..." Mama tace 'Amin, ina fatan kinji duk abinda mahaifinki ya fada maki? Wannan ya zama izina a gareki ya zamo shine sanadin shiriyarki." Tace "Amin." Bayan sun gama mata nasiha mai ratsa zuciya ta tashi da gudu ta nufi dakinta ta fada kan gado ta dinga rizgar kuka, kukan bakin ciki, kukan takaici da kunci, kukan dana sani, kukan nadama ji take inama a maida hannun agogo baya ta farka taga duk mafarki ne? Inama zata ga duk wannan abubuwan basu faru da ita ba? Inama zata koma baya ta gyara kuskurenta? Inama? Inama?....!
*********
Kafin asuba ya farka duk da yayi bacci late amma ya tashi da wuri, bathroom ya shiga ya dauro alwala ya fito ya gabatar da nafila yana tsakar karatun qurani Yasir ya farka nan bayan yayi alwalla sai suka tafi masallaci don yin sallah. Haka suka dawo suka kwanta bayan sun gama sallah shidai tunaninsa shin Zarah na sonsa? Batada wanda takeso? Nan ya kuduri a ransa zai gane indai bata sonsa toh sai ya san yadda aka dakatar da auren, in kuma tana sonsa zai kwantar da kai bori ya hau watakon ya kuduri zai sallama mata zuciyarsa da kuma ruhinsa! Dafa shi akayi Yasir yace "What's wrong??" Ya juyo ya kakalo Murmushi "Bakomai me kagani?" Yasir yace "Naga tun dazu ka zurfafa a cikin kogin tunani, kar dai tunanin Hoodah ne ke dawainiya dakai?" Zaune Yasir ya mike "Look Ashraf, Hoodah yanzu matar wani ce dole zakayi hakuri ka manta da ita, kasani bai kamata kana tunanin matar wani ba...." zaune Ashraf ya tashi shima yace "Ko kusa ba tunanin Hoodah nakeyi ba, ina tunani ne akan Zarah...." Yasir yace "Have you fallen in love with her?" Ashraf yayi dariya da son kawar da zancen ayace "Ka tabbatar Zarah na sona? Zata zauna dani? Batada wanda takeso?" Yasir yayi murmushi hade da dafe kafadun Ashraf "Kamar yadda na fada maka Zarah is the most simplest girl you'll ever meet, wadda bana maka fatan ka hadu da ita shine kanwar mu wato Khadija, ita kwatakwata halinta yasha bambam dana Zarah, she's kind though but she got nerves...." Ashraf yayi murmushi "Allah sarki kasan sai kaga a gida daya kowa da halinsa, wai nikam tana ina Khadija? Kullum sai dai na dinga jin labarinta gun Zarah amma ban taba ganinta ba?" Yasir yace "Kar ka damu zaka ganta ay, ita Khadija karatu take tana 300 level tana UK, amma munyi waya tace mun tana nan zuwa very soon, zuwa jibi ma maybe..." Yasir ya kuma cewa "Kusan tsarararaki ne itada Zarah shekara daya ke tsakaninsu, amma fa suna mugun kama, saidai fa Khadija yar lele ce gaba daya Mummy ji take da ita, karfa kace ba'a ji da matarka amma dai tafi ji da Khadija." Ashraf yace "Allah sarki, toh wai ita Zarah ta gama karatunta ne?" Yasir yace "Ta gama kasan ita Khadija ta tsaya wasa da rawar kai sheyasa har Zarah ta kammala ita tana nan, saidai sa'ar ta daya Khadija dai yanzu ta kusa kammalawa don semester daya yarage ta shiga 400 lvl yanzu haka exams sukeyi." Ashraf yace "Ok, Allah toh ya dawo mana da ita lafiya." Yace "Ameen."
Washe gari karfe tara da kusan rabi Zarah ta shigo da sallama dauke da tray din abinci, nan ta gaishe da Ashraf dake shanya towel din da yayi wanka ya amsa da murmushi saman fuskarsa, yace "Zarah nagode da dawaniyar da kike yi fa, nace maki ki dinga bar man a bisa dining zan dinga ci a can." Tayi murmushi zuciyarta na harbawa, binshi da wani asirtaccen kallo tayi tace "Ba dawiniya bace yaya Ashraf karka damu, yanzu dai ina kwana?" Yayi murmushi "Lafiya lau Alhamdulillah ya kike?" Tace "Alhamdulillah, ga breakfast nan kaci, idan kagama zan dawo in dauke." Yace "A'ah karki damu zan kai da kaina ma." Tayi murmushi ta mike tsaye "A'a zan dawo in dauke kawai ka kirani." Tana gama fadan haka ta mike ta fita daga dakin tana murmushi.
5 days later....
Tun safe ake shirye shiryen tarbar Khadija, rabonta da gida ya kai shekara daya da wani abu a cewarta ita bata cika son xama Nigeria ba it's suffocating her, karfe 12 na rana jirginsu zai sauka don haka Mummy ta umarce Ashraf da Yasir da suje su daukota, nan suka tafi lokacin karfe sha daya da minti kusan talatin, a mota ne Ashraf yace da Yasir "Lallai yau na gasgata zancenka Yasir wato dai Khadija yar lele ce haka?" Yasir yayi murmushi yana concentrating a titi yace "Ay bakaga komai bama." Karfe 12 da minti sha biyar suka isa, bayan sunyi parking ko fitowa daga motar basuyi ba sai ga jirginsu ya sauka, cikin farin ciki Yasir "MashaAllah sun iso, nasan nan da minti goma zata fito." Nan sukayi tsaye suna jiranta bayan minti kusan sha biyar Yasir ya hangota ta fito tana jan akwatinta, nan Yasir cikin farin ciki yace da Ashraf "Kaganta can tana sanye da kananan kaya." Daga ido yayi yana kare mata kallo, sanye take da bakin wando sai yar ciki da leather jacket, tana sanye da hula black color ta riko hand bag dinta da wayarta, tafe take cike da yanga da kaisaita kai kace diyar wani shugaban kasa ce ko gwamna, bakinta kuwa chewing gum ne take tauna in style, fuskarta na manne da bakin glass wanda ya rufe mata kusan rabin fuskarta, tun kafin ta karaso turarenta yabi ya cika masu hanci Yasir ya nufi inda take da sauri tana ganinsa ta saki akwatinta ta rugo da gudu ta rungume shi tana ihun murna, bayan sun gama hugs din ta sake shi ya dauko mata akwatinta suka soma takowa wurin motan, suna zuwa daidai nan ta bude mota zata shiga taji ance "You're welcome Khadija..." ta dago idanunta tana kare masa kallo, tana duban Yasir daya bude booth yana kokarin sanya mata akwatinta ciki tace "Bros who's he?" Yayi murmushi "That's my friend Ashraf, remember him lokacin muna school?" Ta dan yamutsa fuska "I can't remember...." Yasir yace "It's ok then, ki gaishe shi ko?" Ta kalli Yasir tana kokarin bude mota "But you know I don't talk to strangers..." ta fada tana kokarin bude kofar motan, Yasir yayi karaf ya rike mata hannu "Ashraf is not a stranger, mind you he's family now ki gaishe shi in ba so kike mu kwana a nan ba." Takowa tayi gabanshi ta tsaya dab dashi ta cire glass din idanunta tana kallonsa from head to toe sannan tace "Sannu."
1 comment:
Deposit Bonus Casino Rollout Guide - $1600 Bonus
Looking for 넷마블 포커 the best $1600 casino rollover on our list? We've gathered a list 랜덤 룰렛 of 온라인바카라사이트 10 of the best bet365es no deposit bonuses for December 2021. Rating: 4.3 · Review by 스포츠 토토 사이트 CasinoRollover
Post a Comment