Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 29




*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
      P.M.L

*we dont just entertain and educate,we touch d hearts of readers*

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNART Lameed'o*
*RUFAIDA YUSUF*

*Page 29*
      *By*
*ʍʀs Κ„aΥ‘Υ‘aʐ*

     Ba a fi 10 mins da yi mishi waya ba ya sake kiranta yace ta fito su tafi

      Haka suka dinga fito da kayan bakin hostel shi Kuma yana kaiwa mota har suka gama sai ta ce ya raka ta su karb'i phone d'inta a wajen Masu chaji Da yake a wayar Halima suka dinga communicating, ba musu suka tafi karb'i waya suna tafe suna hira abin su gwanin ban sha'awa

      Suna tafiya su Untouchables suka fito daga mab'oyar su don duka abinda ya faru akan idon su ne,suna zuwa suka yi raga-raga da glasses d'in motar gaba d'aya sannan suka sace masa tayoyi duka,suka d'ebo Datti mai yawa suka tura a cikin motar, sai kuma kit d'in Zulaiha suka FASA shi shima suka zazzage kayan da ke ciki,akwai wata jakar undies d'inta itama haka suka zazzage ta a wajen suka yi mata baja-baja da kaya,suka kuma tsaya a wajen suna jiran suga ta inda za a bi a fitar da ita daga school d'in

      Suna nan tsaye Big boy da Katon kulki a hannun sa inda k.b ke rik'e da katakon hockey sai kuma Eeshat da ke gefe tana tauna chewing gum kowanne daga cikin su ya rufe ido da bak'in Google.

      Tunda su Zulaihat suka doso wajen taga abinda ya faru zuciyar ta ta fara bugawa da k'arfi, tsoro ne sosai ya shige ta don ta San wannan tsayuwar tasu ba ta alkhairi bace.

     Shiko Dr ganin hakan da yayi ba k'aramin b'acin rai ya shiga ba,domin kuwa wannan B'arnar da suka yi masa ba k'aramin kud'i zai jaa ba,gashi kuma shima yana tsoron tunkarar su.

     Juyawa yayi yaga yanda zulaihat gaba d'aya ta gama tsorata jikinta sai rasa yake yi. tsoron ta d'aya kada su tab'a lafiyar masoyinta

     Kallon ta yayi suka had'a ido ya mata alama da ido na "be strong" sai dai hakan da yayi maimakon ya bata k'warin guiwa sai ka karya mata zuciya sai ta fashe da wani sabon kukan

     Ganin haka ya sa ya ce mata tayi hak'uri su koma clinic ya karb'i key D'in motar Dr khaleed sai ya kaisu da ita

      Shi kuma ya juya ya nufi wajen motar zuciyar shi na matuk'ar bugawa don bai San me zasu yi masa ba,sai dai bai bari hakan ya nuna a face d'in shi ba

     Yana zuwa ko kallon inda suke bai yi ba ya sunkuya ya kwashe kayan zulaihat d'in da suka watsar,su kuwa suka dinga mishi dariya suna tsokanar shi Wanda hakan ba k'aramin bata masa rai yayi ba

      Ya gama had'e kayan tsaf ya juya zai tafi sai kawai ji yayi an jefe shi wani abu mai matuk'ar wari ta bayan shi

      Cak ya tsaya yana tunanin menene Wannan suka jefa masa? Sai dai bai juya ya tanka su ba ya ci gaba da tafiya,Ai kamar daga sama sai ji yayi ana ta jefa masa wannan abun mai warin masifa har ji yake tamkar zai yi amai

      Cike da zafin zuciya ya waiga idanun sa sun jawur kamar gauta ya yi wani kukan kura ya kauwa big boy raruma Wanda shi bai expecting haka ba. Kafin kace meye wannan ya had'a masa jini da majina Domin idon Shi a rufe yake ko ganin abin yake baya yi,daga baya yaji an cafko shi ana k'ok'arin daga shi sai ya kuma cakumar Wanda ke rik'o shi ta bayan ya kwantar da shi a kasa ya d'auki wani dutse a gefen shi ya buga masa akai,dai-dai nan kuma Zulaihat ta k'araso wajen don ganin abinda ke faruwa ga mutane sun taru mak'il a wajen ana kallo an rasa mai shiga tsakani

      Da yawa mutanen Wajen Allah shi kara suke yI wa untouchables ana cewa yau sun tab'o Wanda ya fisu masifa, Eeshat kuwa ganin ana dukan su big boy ai tuni ta sampe daga wajen ta karawa wabdon ta iska, bata tsaya koina ba sai d'akin da Ruky ke jinya ta labarta mata abin da ya faru

     Zulaihat kuwa ganin Dr na Neman yin kisa ya sa ta taho da gudu ta na rik'e shi amma ina bai ma saurate ba ba ya hankad'a ta ta fad'i gefe guda, duk da haka bata hak'ura ba ta sake zuwa ta rik'e shi tana janshi,sai a sannan ya gane meke faruwa ya tashi suka bar wajen inda aka bar su k.b a wahale kowa ya Watse Ana musu Allah shi k'ara

UntouchablesπŸƒπŸ»‍♀

1 comment:

Unknown said...

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ Su KB anji maza