Friday 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 09

πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’


Written by MSB✍🏻 
Story by Maryam Sb (MSB) 😘 πŸ’• 




πŸ‘„πŸ’‹




Page 09



“Mom please” tace tana riko hannuwan mom.

“Wai idan kuka tafi nida wa zaku bari?” Mom ta fada tana latsa wayarta da alama wata number take nema zata kira.


“Mom kwana 2 kawai zamuyi fa kawai” cewar Amal.


“Don Allah mom” Samha ta fada tana zama kasa gefen mom. 

“Ok kuje amma make sure kun fada ma babanku”


Yau kwana 1 kenan da tafiyar Fawzan, tunda ya tafi wayansa ke kashe tana ta kira, amma sai kawai tayi tunanin tasan baiyi settling ba kuma maybe aiki ne ya rike sa, amma tace zata kuma gwadawa gobe. 

Kadaici ne ya ishe ta shine ta tuna da kakarsu ta side din babansu, ita kadai ke sata dariya tana debe mata kewa.


Dad suka tambaya ya amince, cike da murna suka ruga upstairs itada Amal, da yake Amal ta dawo dakinsu Samha gadon Hilwa. Kayansu suka shiga harhadawa a jaka da duk wani abu da zasu bukata. 
Bankwana suka ma su mom Salisu ya tafi kaisu Gwarumpa. 



_______




Da gudu suka shiga gidan.

“Hi kakale!”
Suka fada suna fadawa jikinta. 

“Ke Dije haka akeyi zaku fado ma yar tsohuwa salon ku karya ta” tace tana kwance kullin goronta a leather.


Samha ta tsani sunan wai Dije, asalin sunanta Khadija sunan kakarta ne ta wurin mom.


“Tabdi! Hajiya, Dije kuma?” Tace tana daga gira daya, dariya tayi ta make mata cinya cikin wasa.

“Yar tsohuwa ina wuni?” Cewar Amal tana dora kanta bisa cinyarta

“Lafiya takwara Hassatuwalle” murtuke fuska tayi 

“Hafsat dai”

“Ke kika san wani Hafsa mu Hassatu muka sani”

“Bawani nan”

“Eh mana, wai tukunna ma wata nawa zakuyi nan?” Ta fada tana ballar goro tana kaiwa baki


“Ahh! Easy yar tsohuwa meya kawo na wata kuma kwana biyu kawai zamuyi”cewar Samha. 


“Ja’ira” tace tana kyalkyatar dariya


Suka sa dariya gaba daya. 


Daddare Tuwon semo miyan kuka da man shanu suka ci, bayan sun gama ne suna zaune dakin da suke sauka. Samha tace da Amal.

“Har yanzu Fawzan bai kirani da number din can ba” ta fada cike da damuwa

“Da gaske? That’s unlike him, kila aiki ya masa yawa ki dan kara jira kadan zai kira inshaAllah” 


“Allah dai yasa lafiya, na saba ne duk inda yaje yana sauka yake kira na...”


“Ya Samha ki kwantar da hankalinki zai kira”


“Okay Hakane kam”



*****


Washe gari yawo suka tafi mostly shopping, sannan suka siyo snacks sai da yamma suka dawo. 

Wanka Samha tayi nan taji saukin gajiyan dake damunta, dogon skirt ta saka baki da riga pink color, sai da sukayi sallar asr sannan suka baje sukaci suka sha duk da dai Samha din ba wani da yawa taci ba.

Tana gamawa Yasmin ta kirata, dauka tayi 

“Hey dear” cewar Yasmin.

“Ya kike?”

“Alhamdulillah ashe bakya gida nazo akace kina gidan Hajiya”


“Wallahi fa, jiya nazo amma gobe zan koma inshaAllah”


“Ton shikenan bari na tafi gida kawai...”

“Haba baki iya zuwa nan?”


“Zan iya mana, yamma tayi that’s why”

“Oh ok, ya labarin Fawzan?”


Ajiyar zuciya tayi
“Har yanzu bai kirani ba”

“Zai kira aiki ne ya rike sa nasan”

“Bai taba tafiya ba aiki ya hana sa kirana ba”

“Maybe this around is different kinsan dole akwai kwakwaran dalilin da yasa bai kira ba dai ko, ki masa uzuri”

“Nayi”

“Yawwa, toh bari na tafi bye, sai munyi magana”


“Thank you so much Yasmin insha Allah idan na dawo zanzo”


“Alright”




*****


The most annoying sound in the world woke her up, her stupid alerm. 

Da sauri tasa hannu ta kashe, karfe 4:30, a kasalance ta fada toilet, bayan ta fito ne ta soma da nafilfili, ana kiran Asuba Amal na tashi ta shiga toilet don yin alwalla.

Bayan Samha ta gama sallah ne ta bude qur’ani tana ta karantawa daga suratul fatiha, then her favorite surah wato Suratul mujadala har ta gama sannan ta karanta sauran litattafan addu’ointa bayan ta shafa.  

Karfe 6 ta tashi daga kan sallaya, ta ninke ta mayar da qur’ani mazauninsa.
Gado ta hau kafin wani lokaci bacci ya dauke ta.


______


“Ya Hilwa tashi! Tashi ya Hilwa” a hankali ta bude idonta inda ta sauke kan Amal dake tsaye kanta. 

“Lafiya zaki tashe ni ina bacci?”

Zama tayi gefenta ta rungumo ta, take ta fara sheshekar kuka. 

Cikin rashin fahimta ta janye ta daga jikinta tace
“Kuka Amal? Meyafaru?”

“Ya Hilwa kinsan dai kullu nafsin za’ikatul maut ko? Kinsan da haka ko?”

Gabanta ya fadi.
“Na...sani mana, wani abin ne ya faru”

“Ya Hilwa ki zamo daga cikin masu hakuri da tawwakali, ki zamto mai hakuri ya Hilwa”

A lokacin ne kuma gabanta ya tsananta bugu
“Amal ki sanar dani meya faru don Allah?”

Ba tare da tace komai ta jawo hannunta suka rinka shiga wasu kofofi kofa tafi goma har suka iso wata kofa mai hasken gaske, ja sukayi suka tsaya, iska ke kadawa ko ina ga wani irin haske mai haske idanu.

Amal ta shiga nuna kasa inda gawar ke kwance an lullu6e ta da farin linkafani.

“Bude ki gani ya Hilwa”

Hawaye ya shiga sakko mata
“Waye? Waya rasu?”
Ta tambayi wasu mutane dake tsaye cikin shigar kayan pilot. 


Ba wanda ya tanka ta, hakan yasa ta dinga takawa a hankali har ta isa inda gawar take, tafi minti 2 kafin a hankali ta zame kasa tana kallon gawar, hannunta ya shiga rawa inda tasa hannu ta fara yaye fuskar mutumin. 

Tana budewa ta mike tsaye a razane tana girgiza kai hawaye kuwa kamar ana ruwan sama, nuna gawar take still tana girgiza kai
“It can’t be! No!”

Razanniyar kasa ta saki...


“Hasbunallahu wa ni’imal wakil” zaune take kan gado amma ko wace ga6a ta jikinta rawa take kamar mazari, zufa kuwa ta jike jagab tsabar razana. 

“Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un”

Kawai take nawatawa tana tunanin wannan mummunar mafarki da tayi....

No comments: