Friday 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 73-74

๐Ÿ’„Fawzan ko Adeel?๐Ÿ’


  Written by MSB✍๐Ÿป
Story by Maryam Sb (MSB) ๐Ÿ˜˜๐Ÿ’•


    ๐Ÿ‘„๐Ÿ’‹


    Page 73-74  


   Yasmin ta doka mata harara “Ke kuma a suwa zaki wani shigo gidan mutane zaki fara musu masifa!...?” Samha tayi sauri ta ta6o Yasmin tana mata alamar tayi shiru da idanunta “Bari a kira shi” “Da kar ki kira shi mana, ashe bai mutu ba aka mana karyar ya mutu? Toh aje a fito mana dashi...”  Ciki Samha ta wuce ba tare data tanka ba, ta dan juma ta dawo tana gaba Adeel na biye da ita a baya. Aliyah na ganinshi ta wani yi jumping tayi hugging nashi “Ya Fawzan! Ashe baka mutu ba aka ce mana ka mutu... you have no idea how much I miss you...” Da sauri Adeel ya janye ta daga jikinshi tare da matsawa baya yana kallonta with a confused look, yace “Khadija, wannan kuma wacece? Don ni bansanta ba...” “Kai! Wato harda kawar masa da tunani kukayi don kar ya yarda da kowa sai ku ko? Toh ahir dinku aniyarku ta biku!” “Kiyi hakuri ba haka bane kawai dai lalura ce ta same shi...” “Ba wata lalura, kawai dai abinda kukayi masa ku kwance shi...” “Ke malama shiru shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne...”  Yasmin tace tana kallon Aliyah da ta cika tayi fam!  “Malama ba dake nake magana ba ki bari inyi da wadanda suka isa bake ba” “Ni banida lokacin biye ma haushin da kikeyi, kuma Fawzan gaki gashi nan mugani idan zai yarda ya biki aikin banza kawai mtss” tana fadin haka ta wuce ciki da sauri. Hannunshi Aliyah ta soma ja tana kokarin fitar dashi daga gidan, yayi tsaye cak gamida da fizge hannunsa da sauri “Nace miki bansanki ba, ban ta6a ganinki ba ni mutumin qauye ne ban ta6a zuwa birni ba sai wannan lokacin, don haka wanda kike nema wani ne daban bani ba”  “Haba Fawzan nice fa Aliyah? Remember? Your cousin fa, kar kace baka sanni ba please” “Wallahi bansanki ba, na roke ki ki rabu dani!” Da sauri ya shige ciki Aliyah na kwala masa kira amma ko juyowa baiyi ba A zuciye ta damqo wuyan Samha “Munafuka, daman tun tuni ya tsane ni saboda ke! To wallahi baki isa ba, wallahi mahaifiyarsa zan kawo maku ay bai isa yace ya mance da ita ba...” “Let me go...” Samha ta cire mata hannu daga rikon data mata. Sannan tayi dragging nata ta fitar da ita daga gidan. “It’s ok Aliyah calm down and leave please, goodbye!” Tace tare da rufe kofar da lock, tana jin tana ta bugawa ta wuce ciki ta barta har ta gaji ta tafi. Da mom taci karo zata haura sama “Samha hayaniyar me nake ji haka?” “Mom Aliyah ce tazo tana ta surutan banza” “Toh! Ya gane ta ne?” “Yace bai santa ba” “Allah ya kyauta, zan shiga ciki ne, kuje kuci abinci angama” “Toh mom” “Ya Samha...” Ta daure fuska “What’s wrong with you?” “Why don’t you asked yourself...” “Ya Samha...” “Why didn’t you tell me Yasmin is coming?” “Oops! Sorry it skipped my mind” Tayi rolling eyes nata ta jawo Yasmin suka shiga kitchen  “Samha I have served the chicken soup let’s go to the garden and eat it” Amna tace tana rike da cupcake hannunta  Tayi murmushi  “Sure let’s go” Serving kowa yayi suka zauna kan grass, katon streetlights ne a wurin suna haska idanunsu kasancewar duhu ya fara yi.  “Wa zaiyi playing Whot?” Yasir yace yana fiddo da cards din Zagaye kwayar idanunta tayi taga bataga Adeel ba, kallon kitchen tayi ta transparent glass din window, hango su tayi tsaye shida Shatu suna hira cikin nishadi, Shatu sai kyalkyala dariya takeyi daga gani wani labari sukeyi mai sasu nishadi. Wani abu ya tokare mata kirji kishi ya turnuke ta, ta hadiye miyau da kyar.  Gaba daya group din sun fara playing Whot din cikin nishadi.  Bata kaunar ganin Fawzan da wata mace, kuma tana sashi nishadi tana wani faranta masa rai har ya manta da ita Mikewa Yasmin tayi “Zanje nayi alwalla, zo ki rakani Samha Please” Yasmin tace tana mikewa tsaye, hannun Samha tayi dragging ta mikar da ita tsaye Tafiya suke suna rike da hannun juna har suka shiga cikin kitchen, bayan Adeel suke gani ya dan ranqwafa ya zauna kan marble island. Ya juyo yana kallonsu ya saki murmushi
“Samha tun dazu nake jiranki zamuyi magana, zan iya fada maki yanzu?” Ta girgiza kai alamar a’ah “Nop! Sorry zan raka Yasmin bathroom ne nima zanyi alwalla daga can” Harara Shatu ta watsa ma Samha tana wani kokarin janshi da hira don ta qular da Samha, wucewa sukayi suka fita daga kitchen din “What’s wrong with you babe?” “It’s nothing!” “Please tell me, it’s Adeel right?” “Fawzan...!”  “Sorry Fawzan, stop worrying yourself ok? Besides aurenta zaiyi kamar yadda zai aureki” “I know, I just don’t like their closeness at all” tace tana wasa da zobenta “Jealousy! Well kishi dole ne but hakuri ya zama dole, besides Samha you’re not even sure ko Fawzan ne...?” “Am ๐Ÿ’ฏsure it’s Fawzan...”  Bude kofar toilet Yasmin tayi ta saka slippers  “Well let’s wait and see, idan ya warke zamu san ko Fawzan ne” tana fadin haka ta shige.  Sallah sukayi bayan sun gama sukayi running downstairs. Garden suka koma babu kowa wurin, and wurin an rage fitilun ya danyi duhu Kamar daga sama Samha taji an wurga mata water balloons all over her body, ihu tayi ta fara kyarma saboda sanyi “What the...!?” Tace tana dragging rigar Areef kasancewar shine gaba gaba Tun daga kanta har kafarta ruwa ne ke diga har sabon takalminta ya jike jagab da ruwa.  “It’s water balloon fight, dauki bucket dinki!” Siddiqa tace tana mika mata bucket dinta “Thanks!” Ta kar6a ta dauki guda biyu a hannunta “Hey Samha look!” Ayman yace daga bayanta, juyowa tayi bata ankara ba taji ya wulla mata balloons da yawa a jikinta Ihu tasa cikin dariya itama ta wulla masa na hannunta amma kafin ta kai ga samunsa ya ruga a guje take ta bishi a guje itama tana wulla ma duk wanda ya tari gabanta, take ta jika kowa itama ba abinda ke tashi wurin sai ihu da dariya, gabanta ya dinga bugawa na excitement and joy. Matan suke ihu mazan kuma na dariya, nan ta gane dariyar Adeel amma ta rasa gane inda yake, ita tana tsaye a gefen pool. Can ta hango Yasmin wadda take squeezing gashinta dake digar ruwa ta kyalkyale da dariya, dagewa tayi iya karfinta ta wulla mata balloons din wanda suka sauka kan fuskarta, faduwa kasa Samha tayi ta dinga dariya, Yasmin ta tsaya tana kallonta da mamaki, da kyar Samha ta tsagaita da dariyar sannan ta mike tsaye da kyar tana cigaba da dariya, “Muguwa!” Yasmin tace tana dariyar itama, gwalo ta mata tana cigaba da dariyar mugunta. Hango shi tayi zaune suna hira da Areef suna ta dariya, taji dadin yadda yan gidansu suka jawo Adeel a jiki, dariya tayi kasa kasa ta dauko water balloon ta dage iya karfinta ta jefa masu Adeel ya sauka bisa kansa wanda yayi nasarar jika rigarsa, while Areef a saman fuskarsa ya sauka, dauka tayi zata wullawa Areef ya doka mata harara “Don’t you dare Samha...!” Ina bata saurare su ba ta cigaba da wulla masu tana kyalkyaltar dariya, tana gamawa ta juya ta kwasa a guje, tana gudu iska na kadata gashi dare ya soma yi sosai, sanyi na ratsa ko wane lungu na jikinta kyarma takeyi amma duk da haka bata tsaya da gudun ba.  “This means war!” Taji muryarshi a bayanta, daga kan footsteps din ta tabbatar bashi kadai bane, wuta ta kara tayi hanyar cikin gida amma ina too late jawota taji anyi, ta fasa ihu gaba daya attention ya dawo kansu. “Ya Areef am so...” shiru tayi ganin Adeel yana hucin gudu Areef na gefensa. Jawo ta Areef yayi ta kara ihu “Ya Areef ina zaka kaini?” Bai tanka ba ya cigaba da tafiya, wurin pool taga ya nufa ta fasa gigittacen ihu “Ya Areef plss no! Am sorry! Wallahi akwai sanyi!” But it was too late! Daga ta sama sukayi sukayi swinging dinta suka wulla ta cikin pool! Fadawa ciki tayi, splash kawai akeji na ruwa, gaba daya wurin aka dauki sowa da dariya, swimming tayi ta fito ta tarar da Adeel tsaye with a sorry face. Wuce shi tayi tana kyarma ya biyo ta, gudu tayi saboda yadda rigarta ke manne jikinta ga surar jikinta na bayyana, kakkarewa tayi ta ruga cikin gida a guje. “Khadija...!”  A daki Ta iske Amal da Yasmin sunyi wanka suna sanye da kayan bacci suna hira, da alama Hilwa ta tafi gida.  Wuce su tayi ta shiga toilet tana jin suna mata dariya, wanka tayi da ruwa masu zafi ta fito ta wuce gaban  mirror tana tsane gashinta da dryer. Gamawa tayi ta saka kayan baccinta tayi isha’i ta sauko downstairs don tasha ruwa. Gidan tsit sai mom dake kokarin kashe fitilu.  “Ah baki kwanta ba Samha?” “Yanzu xan kwanta ruwa zan dauka” “Ok, sai da safe to” “Sai da safe”  Mom ta wuce upstairs, fridge ta bude ta dauki ruwan ta kashe fitilan kitchen ta haura upstairs a gajiye tana hamma. Sadda ta shiga dakin ta tarar su Amal na bacci  Wayarta da Saudat ta bata dazu ne ta duba 2:30am tagani, ta ware ido. Wow ashe dare yayi haka? Kwanciya tayi tana addu’ar bacci da tunanin gobe yadda za’a kare a zaman kotu, ajiyar zuciya ta sauke tana cigaba da addu’a tana gamawa ba’a juma ba bacci yayi awon gaba da ita.          


God bless y’ll! ❤️

No comments: