Friday 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 75-76

๐Ÿ’„Fawzan ko Adeel?๐Ÿ’


  Written by MSB✍๐Ÿป
Story by Maryam Sb (MSB) ๐Ÿ˜˜๐Ÿ’•  


   ๐Ÿ‘„๐Ÿ’‹  


   Page 75-76


  Assalam, first of all we wanna thank each and every reader that took his/her precious time to read my  novel, I really really appreciate thanks alot May Allah (SWA) bless you all๐Ÿ™๐Ÿผ  And secondly ina baku hakuri akan rashin jina kwana 2 da kukayi, banida lfy ne๐Ÿ˜” but alhmdllh najii sauki insha Allah zaku cigaba da jina kamar da, one love all❤️ ina jin dadin yadda kuke nuna mun love ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป love you all from the bottom of my  heart ♥️♥️

Wannan Page din nakune Asmau Isa, Maman Humaira, and Xuxu ngd da yadda kuka damu da rashin jina shiru da kuka yi I really appreciate wallahi! MSB ta mallaka maku wannan page din kyauta kuyi yadda kuke so dashi! ❤️
 Ina kuke kawayen arziki Maman dana aka maman Nabeel, Zee Bee, Maryam Gafai, Fatima Zarah yar adami ina yinku irin sosai dinnan wallahi,  Nagode da yadda kuka damu dani ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป Allah ya bar mu tare! ❤️


   ********* the next morning

SAMHA’S POV ๐Ÿ˜‰  

Washe gari na tashi with a fresh and clear mind, idan na tuna yaune ranar da za’a qwatar mun yancina sai naji wani dadi ya rufe ni, qawataccen murmushi nayi da har sai da fararen hakorana suka bayyana, dadi naji a hankali na tashi zaune na duba lokaci 8:41am na gani, tuna tunda nayi sallar asuba na koma bacci sai yanzu na farka, gadon nagani wayam ba kowa da alamar su Yasmin har sun tashi kenan. Tashi nayi daga gadon na nufi  toilet, I did my business bayan na gama na fito daure da towel, gaban mirror na isa na kalli kaina har na danyi haske compared to ranar da na dawo daga qauye, idona baqin ya dan washe, na soma busar da gashina da dryer bayan na gama na gyara shi, na daure into a bun, sannan na shafa cream, wardrobe dina na bude ganin kayan Amal, yasa na tuna banfa da kaya ko daya nan gidan suna gidan azzalumi Haidar, raina har ya sosu dana tuna shi, kawar da tunanin nayi da sauri na fara laluben cikin kayan Amal duk da nasan bazan samu wadanda zasu mun ba, don nafi Amal tsawo, nafi minti biyu gwada wancan cire wancan, tsaki naja na tattara na maida mata kayanta inda na dauko, kiranta na soma yi da karfi “Amal!! Amal!!!” Da sauri ta shigo  “Ya Samha lafiya?” “Na rasa kayan da zansa, banida kaya ko daya nan gidan” Tayi dariya “Oh Ya Samha! Of course you do! Remember ranar bikinki kika hada wasu new kayanki da baki cika sawa ba kika ce asa miki akwati?” “Ohh! Na tuna suna ina?”  Can saman wardrobe ta jawo akwatin ta saukoshi ta dora kan gado ta bude. Nayi murmushi cike da jin dadi na fara duba wanda zansa, can idona suka sauka bisa wata dark green atamfa wata sallah na dinka ta, doguwar riga ce fitted gown, dauko ta nayi na kimtsa na fesa turare masu dadi a jikina, dakin na gyara sannan na sauka downstairs, suratai nakeji a dining na nufi can, gaba daya suna kan dining Fawzan na hango yana cin abinci, sanye yake cikin kayan da na siya masa, black tank shirt, anyi rubutu a jikinta da navy blue Italian style an rubuta You’re mine, nayi murmushi na sadda kaina kasa ganin kallon da yake mani, tahowa na cigaba da yi na samu wuri na zauna, Shatu nagani gefensa tana wani shisshige masa, danne kishina nayi na gaida mom ta amsa da fara’a. “Ina Yasmin?” Nace ina duddubawa Amna ce dake shan tea tace “Taje gida ta dauko kaya zata dawo yanzu” “Ok” kawai nace, pancakes ne da custard dadi naji how I missed custard, serving kaina nayi naci iya cina na tashi. Shiri kowa ya shiga yi can Yasmin ta dawo har tayi wankanta da kit hannunta.  Wurin 11:30 muka tafi kasancewar za’afara gudanar da shari’ar karfe 12:30.  ***** fewa minutes later   Kotun tsit, both lawyers and audience, mu family munyi rukuni wuri daya, alkalin ma bai iso ba har yanzu, na zagaye qwayar idona na ga an shigo da Haidar da yan sanda 2 ke masa jagora hannunsa sanye da handcuffs, dan murmushi nayi ina kallonsa can aka kaishi ya tsaye sannan police biyu suka tsaya gefe da gefensa, hango yan gidansu Haidar nayi zaune maama in banda harara ba abinda take watso mun, sharewa nayi nace ma Saudat “In camera dinnan?” “Mom taba lawyer din da ke kare ki tare da wayarki as evidence” Gyada kai kayi a sadda alkali ya shigo inda masu take masa baya suka rakashi har mazauninsa, sannan sauran lawyers din sun kai hudu kowa ya zauna.  Miqa mashi wasu takardu akayi ya sanya glass dinsa yana duddubawa, wani mutum ke tsaye gabansa ya fara magana  “A yau ranar litinin ashirin da hudu ga watan august, za’a gudanar da shari’ar inda ake karar Aliyu Haidar da aikata laifuka kamar haka: Kisan kai tare da amfani da sassan jikin dan adam yana amfani dashi, aure aure tare da horo mai tsanani da yake ma matansa wanda turawa ke kira domestic violence, na uku kotu ta kama shi dumu dumu yana kashe kashe da kona garin bayin Allah, that’s it for now, wannan shine”  Alkali ya gama rubuce rubuce ya nuna lawyers din dake zazzaune da hannu wata alama.  Tashi na farkon yayi yace “Sunana Barrister Sunusi Aliyu, nine lawyer da ke kare wanda ake qara wato Aliyu Haidar” zama yayi dayan ya mike “Sunana Barrister Sufyan Kamal nine lawyer din dake kare mai qara wato Khadija Ahmad” ya zauna Alkali yayi rubuce rubucensa ya dago da fuskarsa. “Aliyu kaji laifuka da kotu ke zarginka dashi ka amince?” Ya girgiza kansa da sauri “A’a ya mai girma mai shari’a wallahi sharri ake yi man ban aikata laifi ko daya a ciki ba” Alkali yayi rubuce rubucensa ya kalli lawyers din.  “Akwai mai magana a ciikinku” Barrister Sunusi ya mike ya isa inda Haidar yake ya fara magana cikin daga murya “Ya mai girma mai shari’ah! Ana zargin client dina wato Aliyu Haidar akan laifukan da bai ji ba bai kuma gani ba! Sharri ne akayi masa inaso a bani daman in yi presenting wasu yanzu” Alkali- (an baka)  Fita yayi ya shigo da wasu mutane sun kai biyar yace “Ya mai girma mai shari’ah wannan” ya nuna wani mutum  “Maqocinsa ne kuma zai baka kyakkawar shaida akansa, da halayensa na gari, ba’a ta6a kamasa yana koda fada da kowa ba ya mai girma mai shari’ah! Bai ta6a sa’insa da kowa ba balle fada ta fatar baki, Haidar kamilin mutum ne, a bashi daman ya fada maka da kansa” Alkali- (Bismillah) Mutumin ya haura aka masa tambaya yace  “Ya mai shariah tabbas ni maqocin Haidar ne akalla munyi shekara 20 cif tare dasu a unguwar, Haidar mutumin kirki ne mai yawan kyauta, ko fada bamu ta6a yi dashi ba” “Toh gashi ya mai girma mai shari’a haka ma sauran duk zasu bamu shaida akansa, Aliyu Haidar ko quda an masa shaidar bazai iya kashewa ba balle dan adam, yasan darajar dan adam, nakeso kotu tayi watsi da duk zancen su Khadija a wankesa daga zargin da ake masa, nagode ya mai girma mai shar’ah” ya koma ya zauna Alkali- (Barrister Sufyan kana da abin cewa?” Ya taso  “Eh ya mai girma mai shari’ah, inaso Khadija ta fito zan mata wasu yan tamaboyi” Alkali- “Khadija Ahmad muna son ganinki a gaban kotu” Gabana ya bada wani ras ras! Tashi nayi a hankali kamar wacce kwai ya fashewa na isa gaban alkali......          


God bless y’ll! ❤️

No comments: