Friday 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 19&20

πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’

Written by MSB✍🏻
Story by Maryam Sb (MSB) πŸ˜˜πŸ’•

πŸ‘„πŸ’‹

Page 19-20

2days later

“It will be fun I promise”

“Not to me”

“I promise you’ll enjoy it”

“No I won’t and I am not going” tace tana cigaba da saka kayayyakinta cikin akwati sounding annoyed

Yasmin ce keta kokari ganin Samha ta bita wurin bikin friend din cousin dinta data gayyace ta amma Samha taki yarda.

“Please mana Samha”

“Am not in the mood” tace tana cigaba da abinda takeyi

Tsaki Yasmin taja tare da grabbing jakarta da gyalenta ta soma takawa hanyar fita daga dakin wai ita a dole tayi fushi.

Da sauri Samha ta mike tasha gabanta.
“Ina kuma zakije?”

Ba tare data kalle ta ba tace
“Zanje na roki wata friend tawa ta raka ni since you refused” ta fada tana kokarin fita daga dakin

“No wait! Am sorry ok? Zan raka ki but promise bazamu dade ba”

Cike da jin dadi ta daka tsalle
“I promise”

Fita Samha tayi
“Bari na tambaya toh”

***

“No bazan saka wannan rigan ba” tace tana mayar da ita akwati

“Haba mana Samha wai nikam yaushe kika koyi gardama ne?”

“Ohon miki”

“Don Allah kisa, saboda ke fa na saka tawa nasan munada iri daya”

Shiru tayi kamar mai tunani can tace
“Please Yus”

“Don Allah don Allah ki saka na roke ki Gosh!”

“Naji”

“Yeey” tace kamar yaron da aka ma alkawarin chocolate.

Wanka tayi bayan ta gama shafe shafenta ta zura rigar maroon voile lace wanda yayi mugun amsarta, da kyar Yasmin tayi convincing dinta ta mata very very light makeup. Bayan ta kimtsa ne Yasmin tace

“Wow! Kinganki kuwa? Superb!”

Shiru tayi ba tare data tanka ba ta nema hanyar fita, Yasmin tabi bayanta tana dariya.

*

Wurin event din ya kawatu, more especially da yake dare ne sai kyalli yakeyi fitilu nata haska wurin.

Sadda sukaje an riga da an fara, wuri suka samu suka zauna, duk Samha is uncomfortable saboda bata kaunar crowd. Yasmin kuwa sai harkar gabanta takeyi sai kace bikin gidansu ne akeyi da alama dai tasan mutane wurin sosai.

Bayan wani lokaci aka umarci kowa yaje yayi serving kansa abinci, jawo hannunta ta shiga yi

“Tashi muje Samha”

Can ciki tace kanta kasa
“No! Na koshi Please jeki zuba kici mu tafi gida”

Ba tare data saurare ta ba ta ja hannunta ba shiri ta mike ta soma tafiya kanta kasa, serving suka shiga yi bayan sun gama suka shiga takowa back to their seats.

Tsaye yake can nesa shida wani da alama abokinsa ne suna magana daga ganin maganar nada mahimmanci, kamar ance dago kanka kawai ya hango ta tana serving abinci, kamar a mafarki haka yake gani, kallonta ya shiga yi bako kyaftawa har sai da abokinsa mai suna Umar ya tabo sa

“Lafiya?”

“Ba..bu, don Allah yi sauri mu karasa maganar akwai wani abu mai mahimmanci da zanyi yanzu”

“A event?”

“Yes” yace tare da juyowa ya kalli inda take amma sam bai ganta ba, ya dinga kewaye kwayar idonsa yana nemanta amma ina bai ga koda mai kama da ita ba.

“Are you really ok?”

“Y...yes cigaba but hurry up please”

Kwakwata hankalinsa baya kansa jinsa kawai yakeyi, daga karshe da yaga maganar bamai karewa bace yace
“Look mun karasa maganar nan some other time”

“Am..ma...”
Umar bai karasa maganarsa ba tuni ya nemi Haidar ya rasa.

Tsakurar abincin tayi
“Am done mu tafi gida” tace tana duba time a wayarta

“Ke kin gama ni kuma fa?”

“Kin fa gama Yasmin”

“Naji chaii” tace bayan sunje sun daddauki hoto da amarya wanda da kyar Samha ta amince. Tafiya sukayi waje inda Salisu yayi parking motar.

Haidar sai dube dube yakeyi cikin hall dinnan amma bai ganta ba duk hankalinsa a tashe. Sultan ne ya hango shi da sauri ya nufo shi

“Lafiya?”

“I have lost her again” yace yana dafe kansa

“Who?”

“Yarinyar dana baka labari yanzu na hango ta a can wallahi tana serving abinci, noo”

“Are you sure itace?”

“How can I forget the face? Never”

“Ka kara dubawa, maybe kuma ta tafi gida”

Tare suka shiga dube dube amma ina babu alamunta, gajiya Sultan yayi yace
“Sai dai hakuri fa I think she’s gone”

Cike da takaici Haidar ya bar hall din

“Where are you going?” Cewar Sultan

“Home”

“Tun yanzu?”

“Yes”

“Toh muje kayi dropping dina gida”

Bai tankasa ba illa gaba da yayi abinsa, yana fitowa ya hango motar ta fice daga gate din.

“Innalillahi kaga motar dana gani ta shiga rannan”
Yace kamar zaiyi kuka

“Sorry man, zamu sake ganinta insha Allah don’t worry”
Yace yana jawo sa mota.

“Bani da sa’a sam”

“Don’t say that”

“It’s the truth” yace yana shiga mota.

**********

Last akwati take zipping, Amal nata kallonta

“What?”

“Babu zanyi missing dinki ya Samha”

Yar dariya tayi tace
“Am not going forever, you can visit anytime you want, and I will be coming every weekend idan am free insha Allah”

Kamar zatayi kuka tace
“Insha Allah”

Bayan ta gama arranging manyan akwatinanta guda biyu ta dauki kit dinta ta saka sauran kayan makeup dinta da costumes nata. Amal ce ta shiga tayata fidda kayan waje cikin boot, bayan sun gama ta je ta samu mom and dad ta masu bankwana, addu’a suka shiga yi mata da nasiha.

Bayan ta shiga mota kiran Yasmin ya shigo

“Babe am on my way” tace bayan ta dauka

“Me too mu hadu school”

“Alright”

Can kusa da hostel din yayi parking, nan suka jira Yasmin ta karaso, ba’a jima ba motarsu ta karaso, drivers din suka shiga fiffido masu da akwatinansu, kayan abincinsu aka shiga saukewa ba abinda babu, bayan sunyi bankwana dasu suka shiga jan akwatin. Dole sai dai da daya daya idan suka kai su dawo.

“Wai ina zaki kai wadannan uban kayan?” Samha tace suna tafiya cikin hostel din.

Dariya Yasmin tayi
“Inda zaki kai naki”

Haka suka karasa room 7 shine nasu, ganinshi bude yasa suka shiga da sallama, yan mata biyu ke ciki ko wace kwance kan gadonta suna ta hira, ganin baki yasa suka mike zaune suna fara’a suna amsa sallamansu.

“Sannunku” su Yasmin suka ce suna karasawa gun 2 empty beds din da suke dakin. Akwatinsu kowa ya aje gefen gadon sannan suka sake fita dauko sauran kayansu. Kayan abincinsu suka shisshigo dasu suka samu gefe suka aje kafin suyi unparking su adana komai.

Suna dawowa yan mata suka mike suna masu sannu da zuwa, bayan sun amsa yan matan sukayi introducing kansu.

“Sunana Zainab Mustapha, but u can call me Zee Musty” wata doguwa baka tace

“Nice to meet you” suka fada a tare

Dayar fara ce mai tsaka tsakiyan tsawo tace
“Am Murjanatu Suleiman”

“Nice to meet you all”

“Thanks” sukace a tare

Yasmin ce tace
“Am Yasmin Sadiq and this is my childhood friend Khadija Ahmad but ana kiranta Samha”

 Samha tabi dakin da kallo gaskiya dakin nada kyau ya burgeta kamar ba hostel ba, yana dauke da medium size beds guda hudu ko wane da side drawer dinshi da wardrobe marar girma sosai a gefe, daga gefe kuwa kowa da study table dinsa, can gaba kadan yar kofa ce ashe dan kitchen ne karami, harda toilet ciki mai showers biyu da toilet seats biyu haka ma sink.

Unparking sukayi kowa ya shimfida bedsheets da bargonsa, suna gamawa aka kira magrib, sallah sukayi, sai da sukayi isha’i suka dafa macaroni da sauce sukaci.

Karfe tara tayi wanka bayan ta kimtsa ta haye gadonta, hira sama sama sukayi sannan Yasmin tace
“Gobe sai mu fara registration”

“Insha Allah” tace tana jawo bargo tare da rufe idanu

“Allah ya kaimu” inji Yasmin

“Amin” Samha tace tare da yin addu’oin bacci, kafin wani lokaci bacci mai nauyi ya dauke ta.....

*^*^*^*^*^*

No comments: