Friday 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 41-42

πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’  


Written by MSB✍🏻
Story by Maryam Sb (MSB) πŸ˜˜πŸ’•    

πŸ‘„πŸ’‹  

Dedicated to each and every reader, we really appreciate your love and support one love ❤️    

Page 41-42    

Ihu ta fasa tace “I beg you in the name of Allah please let me be! Banaso banaso! Wai ana dole ne?”  Bige mata baki yayi “Kul! Don’t mention Allah in this saboda na tabbatar yace don’t disobey one’s husband, kila har kin manta but ke matata ce yanzu, I can whatever I want to do with you! Got it?”  Hannu tasa ta rike wandonta iya karfinta, dariya yayi ta mugunta sannan yayi grabbing breast dinta da karfi ya dinga matse su, azaba taji take ta fara ihu tana kokarin cire masa hannu amma ina ta kasa, sai da ya gaji dan kansa sannan ya bari ya mirgina gefenta kan gadon ya dinga snoring kamar dabba.   Tana ganin haka ta mike ta leka waje taga gari ya fara haske lallai ko runtsawa batayi ba bare sallar asuba, jiri ta dinga jin yana dibarta ga duk illahirin jikinta ciwo yake, kanta kamar ana sara mata guduma, da kyar take tafiya tana bin bango tabi ta hanyar da aka shigo da ita, kofar ta gani a rufe gam gashi irin glass door dinnan ce, ta dinga kokarin budewa ta kasa, haka ta zagaye gidannan kaf bataga wata kofar ba, window ta bude taga duk karafuna jikinta bata iya fita.  A hankali ta juyo taga wata kofar daki ta shige ta danna key, dingishi takeyi ta isa gaban wani mirror data gani a dakin ta kalli kanta, jini duk ya bushe mata a fuska, jikinta duk shatin bugu ne, gefen bakinta ya kumbure, fuskar duk ciwo dai, breast dinta ji take kamar ba’a jikinta yake ba sai zogi suke mata.    Zamewa tayi kasa ta saka fuskarta cikin cinyoyinta sam ta nemi hawayen ta rasa, hannu tasa cikin gashin kanta tana yamutsawa, ganin zaman bazai mata ba ta mike ta duba taga wata kofar toilet ta shiga, ruwa masu mugun zafi ta kunna ta gasa jikinta sannan ta dauro alwalla, jinin ta wanke daya bata mata kaya, sallah tayi bayan ta gama ta dade tana addu’a Allah kawo mata mafita a gareta.   Kwanciya tayi kasa saboda baccin da takeji ga ciwon kai, nan ta kwanta bacci ya kwashe ta.  Karar buga kofar ya farkar da ita, da sauri ta tashi gabanta ya yanke ya fadi “Baiwar Allah ki fito ya dade da fita fa” Da sauri tace “Waye....?!”  “Ki fito in maki bayani”  Kin fitowa tayi don ita kam a tsorace take. “Na rantse da Allah bazan cutar da ke ba, taimaka miki zanyi”   Tashi tayi da sauri ta nufi kofar “Kin tabbatar?”  “Eh”  Bude kofar tayi da sauri tace  “Taimaka min...”  Bata karasa maganar ba taji wani abu saman kanta, a hankali ta waiga ta ganshi tsaye ya aza mata bindinga saman kai.  “If you move I’ll blow your head” kallon dayar yarinyar yayi da ke kyarma kamar mazari yace “Leave now!” Da gudu ta fice  Juyowa yayi yana kare mata kallo “Are you trying to play smart with me? Move!”  Jikinta ba inda bai rawa, janta yake har suka fita waje, suna zuwa ya kara danna mata kan bindigar yace “Take a look!”  Dagowa tayi da sauri ta dinga bin bindigar da ido yana nuna mata, gidan zagaye yake da katti majiya karfi ko wane rike da zureriyar bindiga, kallo daya zakayi masu ka fara kyarma.  “You see my men Samha? If you’re even thinking of running away better stop! Just one move they will shot you dead I guarantee you that! Because you’re not going anywhere har sai na cimma burina a kanki until am done with you! Kina jina?”  Ta gyada kai da sauri.  “John!” Ya kira daya daga cikinsu “Sir?” Yace daya karaso  “I hope you know your job here? Because John if you dare fail you’ll have to bear the consequences! Understood?”  “Yes sir!”  “Good leave! Ke kuma mu tafi!”  Cikin gida suka koma, suna zuwa ya baje kan kujera hade da kunna kallo. “Kawo mun breakfast!”  “Ina?”  “Ni kike tambaya!?” Ya daka mata tsawa  Da sauri ta tashi taga abinci kan dining, daukowa tayi gaba daya ta dire gabansa.   “Sai nace ki zuba? Dabba kawai!”  Zuba masa tayi ta mika masa, wani wawan kallo ya mata. “U mean da kaina zanci? Feed me or I will shoot!”  Bashi ta dinga yi kamar zatayi kuka, daya gama ma daka mata tsawa yayi yace ya gama. “Jeki dining kici naki”  Daman yunwa takeji, wani plate ta dauko ta zuba nata sannan ta zauna ci, tana gamawa tayi clearing wurin.  Kamshin turarensa taji, a kimtse ya fito cikin shigar shadda sky blue da hula kalar kayan, murtuke fuska yayi “Ina wayarki?”  “Tana daki”  “Jeki dauko!”  Daukowa tayi ta miko masa “Daga yau baki ba wayar nan, ba ruwanki da kowa sai ni, kinaji na?”  Idanunta cike da kwalla tace “What about my family?”  Arniyar dariya yayi “Am now your family!”  “Noo kar ka mun haka, zan iya jure komai zaka mun amma kar ka rabani da family na”  Kallonta yake tana kuka yace “Zancen kikeso! Ni kinga na fita, be ready for me kafin na dawo!”  Har ya tafi ya kuma dawowa “And by the way where is your passport?”  “What for?”  Bindiga ya nuna mata, take tayi shiru “Nace yana ina?”  Shiru tayi tana zare ido, shako mata baki  yayi da hannunsa “I said where is it?”  “Gidanmu!” Ta bashi amsa  “Zan kaiki ki kar6o shi and you have do as I say or I will kill you Samha! Understood!?”  “Y...yes!”  Yayi dariya  “Good girl” sannan ya fice bayan ya rufe kofar da key.   Zamewa tayi kasa tana tunanin makomar rayuwarta....   Dafata akayi, firgit ta mike  “Baiwar Allah tunani bashi bane mafita a gareki, addu’a zakiyi”
“Don Allah who are you?”  Jawo hannunta tayi “Zo mu zauna”  Binta tayi suka zauna kan kujera sannan ta soma magana. “Sunana Saudat Yusuf, kwata kwata ni ba yar garinnan bace in-fact banida dangi ko guda daya a nan”  “Toh meya kawo ki hannun Haidar?”  “Ni yar mutan Niger ce, lokacin mahaifina nada rai business partner ne da mahafin Haidar, wata rana na raka mahafina wani function na company dinsu ya hadu dani, a lokacin inada saurayi wanda nake mutuwar so, amma tunda ya ganni ya samu mahaifina yace masa yana sona, da da farko babana bai yarda ba saboda yasan akwai wani al’amari mai girma da ya faru tsakaninsu, in takaice maki labari dai Rivals ne. Yayi threatening dina da kashe duka family dina idan ban yarda ha, haka ina ji ina gani aka daura mana aure dashi, daren farko kamar yadda yayi maki haka ya nakada man duka nasha wahala sannan ya rabani da budurci na ta karfi, haka kullum yake mani har kusan sati sannan ya rabu dani, tunda lokacin ya daina kulani amma bai fasa dukana ba, abu kadan zanyi ba daidai ba ya dakeni.  Kuma kinsan abin tashin hankali bayan rasuwar mahaifinsa duk danginsa sunsa ya sakeni, bawanda yasan dani cikin gidannan ko waje ban isa na fita ba, wata rana na samu labarin mutuwar mahafina wanda na gano Haidar ya kashe shi, na razana na dinga kuka gashi banida waya ya kwace man waya...”  A razane Samha tace “Taya kikasan mutuwar mahafinki?”  “Shi da bakinsa ya fada man”  “Innalillahi wa inna ilahir rajiun”  “Don Allah ya sunanki?”  “Sunana Khadija amma ana kirana Samha”  “Toh Samha shawarar da zan baki shine duk rintsi duk wahala kar ki bari ya karbe maki budurcinki, in-fact koda wasa kar ki bari ya kusance ki har ya maki fyade”  “Nasani saboda saura kiris ya man fyaden ay, amma ya akayi kika bari ya taba ki ke?”  A lokacin da bansan sirrinsa bako”  Cikin inda inda tace “Wa...ne si...rri?”  “Siirikansa sunada yawa Samha, wallahi Samha idan zaku kwana kuna bincike bazaku taba ganowa ba”  “Don Allah ki fada man Saudat”  “Zan fada maki wani lokaci Samha ina gudun fadawarki wani hali”  “Bandamu ba kawai ki sanar dani don girman Allah”  Mikewa Saudat tayi tsaye tana share hawayenta tace “Tunda nike a rayuwata ban taba cin karo da azzalumin mutum ba, marar imani, macuci, azzalumi ba kamar Haidar, Haidar ya cuce ni ya cuci rayuwata... ya cuci yayan mutane ya salwantar da rayuwarsu Samha...!” Ta fada cikin kuka  “Me yayi maki? Me yayi ma yayan mutane? Ya fada man yace yana auren yarinya ya gama da ita ya saketa...”  “Samha Haidar zai iya dawowa a kowane lokaci ina gudun ya gammu tare, zai iya cutar dake, saboda yasan nasan sirrinsa, bazaiso ya ganmu tare ba”   “Don Allah ki fada man wane sirri ne wannan? Na shiga uku!”  Dafata Saudat tayi tana kallonta da kyau sannan ta fara magana.....

                 
Thanks for reading! πŸ˜‡

No comments: