Friday 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 69-70

๐Ÿ’„Fawzan ko Adeel?๐Ÿ’  

Written by MSB✍๐Ÿป
Story by Maryam Sb (MSB) ๐Ÿ˜˜๐Ÿ’•    

๐Ÿ‘„๐Ÿ’‹    


  Page 69-70  


   ******  

 Karfe 8:54 suka isa asibiti da mom da Amal da Adeel da Samha tace in ba’a zo dashi ba bazatazo ba, a cewarta shima sai yaga likita da kyar ya yarda ya biyo su. Reception suka tsaya suka fiddo card mom ta biya aka mika su ga wani Doctor Hamza dake on duty, wani Eye Doctor ne field dinsa kenan. A waiting area suka jira akwai patients uku kafin su, nan suka cigaba da jira har finally aka kira Samha, mom ta kamata suka shiga dakin, zaunar da ita mom tayi itama ta samu wuri ta zauna, file dinta ya bude tare da gyara biro.   An elderly man about 40 to 45 years, mai dan jiki chocolate skin color ne zaune kan kujera yana dauko file daga jikin sauran files din dake ajiye kan table, yace “Khadija Ahmad ko?” Ta gyada kai Yace “What’s the problem miss Khadija?” “Doctor I was hit” “With what?” “Uhmm... am not sure” “Why?” Yace cike da rashin fahimta “Well, I wasn’t aware of the surrounding, and I was hit” “I see” yace yana rubuce rubuce “Can you come and sit here please?” Tashi tayi mom ta taimaka mata ta zaunar da ita kan wani gado a dakin, a hankali ya shiga warware abin da aka nade mata idon dashi har ya warware gaba daya, idanun sun manne wurin yayi ja ya kumburo. Dubata yayi ya dago yana kallon mom cike da mamaki “Wace asibiti kuka kaita?” “Uhm ba asibiti bane” “No wonder, ma’am why? meyasa zakuyi mata magani a gida? Cuz I can clearly see da iliminki why?” Ta kama inda inda yace “It’s ok don’t worry” yana cigaba da dubata  Nunfasawa yayi ya dawo ya zauna mom tabi bayansa “You can clearly see she cannot open her eyes, I think we have to operate on her to open them for her” Yaga yadda ta zama shocked nan take ya saki murmushi yana gyara zaman siririnsa glass dinsa. “Don’t worry ma’am is just a minor operation, just 15 minutes angama, if you’re ready gobe da safe sai ayi” “We’re ready Doctor, indai za’a samu lafiya ay mu fatanmu kenan” “Alright tomorrow at 9:00am on dot zan  shigo, sign here please and proceed to pay for the operation at reception area” “Mungode Doctor zamu iya tafiya?” “Ah... no need I will just admit her here da safe ayi is that alright?” “Of course Doctor ba matsala” Rubutu ya cigaba dayi inda yayi admitting nata ya basu daki. Bayan ya gama ya mika ma mom file din.  “Here is your room, room7 collect the key nan wurin nurses, zasu zo su sa mata drip and the rest” “Thank you” “No problem Allah bata lafiya” “Ameen” mom tace gamida mikewa ta kamo hannun Samha Fitowa sukayi inda su Amal suke, mom tace “An kwantar da ita aiki za’ayi gobe da safe” “Innalillahi aiki?” Adeel yace a dan razane “Mom wane irin aiki?” Amal tace tana zare ido “Ku kwantar da hankalinku bawani major aiki bane is just minor, za’a bude idon ne cuz ya liqe she can’t open it herself” “Okay”  “Ku jira nan bari na fada ma nurse ta bude dakin ku shiga da ita nikuma I will make all the necessary payments” daga haka ta wuce kai tsaye reception, ba’a juma kwarai ba ta dawo itada nurse, sai da ta tabbatar an gyara masu dakin sannan ta wuce don biya kudaden. Sai da mom ta biya dukkan kudaden ta dawo ta kalli Amal “Amal zaki kwana ko na tsaya na kwana?” “Zan kwana mom” “Ok bari na bada a kawo maku abinci naga bakuyi dinner ba, da safe zan dawo insha Allah, me kuke bukata kuma?” “Mom brush dinmu da toothpaste, then cream and perfume, and sallaya da hijab, sai kayan da zamu sa gobe sai bargo, pillow and carpet, shikenan I think” “Okay” Nan mom suka dan zauna aka saka mata drip din da allurai, fira kadan sukayi wurin after 9 ta tashi ta kalli Adeel “Muje ko?” Ya mike yana kallon Samha “Allah ya kara sauki Khadija” “Ameen” tace sannan ya fita.  “Mom good night” Samha tace tana murmushi  “Good night Allah ya kara sauki, sai kunga saqon” “Tam” daga haka ta sa kai ta fita, sama sama sukayi hira wurin 11:25 aka doka knocking, Amal ta mike ta bude kofar ganin mai gadinsu ta gaishe shi yace “Ya mai jiki?” “Dasauki” “Ga kayan inji Hajiya” “Tam Mungode” tace tana kar6ar wasu daga hannunsa, kayan ya shigo dasu duka ya mika mata wasu ledoji guda uku.  Godiya ta masa sosai ya masu sai da safe ya fita. Ledojin ta bude, shawarma ce guda biyu da meatpie biyu, sai samosas, dayar ledar kuwa pack din abinci ne guda biyu, dayar ledar kuma drinks ne dana roba dana kwali sai ruwa, fridge Amal ta bude ta saka drinks din da ruwan sannan ta dawo suka fara cin abincin.  Suka ci iya cinsu Amal ta saka sauran fridge, shimifida carpet Amal tayi kasa ta rufe Samha da bargo daya tayi ta dauko dayan ta aje inda zata kwanta, rage masu wutar dakin tayi ta kwanta, dakin tsit Amal tace “Bacci kike ya Samha?” “Uhm uhm” “Ok” Shiru ya kara biyo baya Samha tace “Wai ina dad?” Gaban Amal ya yanke ya fadi, taso fada mata amma mom ta gargade ta da sai Samha ta nutsu ta kuma warke, don tasha wahalar rayuwa bai kamata a kuma tada mata hankali ba. “Baya nan ne” “Ina yaje?” “Baya kasar” “Why ba’a samun wayoyinsa?” Rasa Abinda zata ce tayi, can idea tazo mata “Oh ya kira mom da public cellphone wayoyinsa suka fadi a airport” “Ohh, when is he coming back?” “Nextweek” “Allah dawo dashi lafiya” “Ameen, ya Samha jibi ne za’a fara zaman court” “Eh, idan aka bude mun ido na ina so naje station to tell him my mind, I want to show him how happy I am da na ganshi a situation dinnan” Amal ta danyi dariya “Kai ya Samha” “Allah, he’s a monster mutumin, macuci kawai, mugu...” “Ya isa ya Samha, kar ki 6ata ranki a banza a wofi, let’s all focus on your health now that’s the most important thing to us yanzu, ki rabu dashi, hausawa na cewa ka gina ramin mugunta gajere, idan ka gina shi da fadi to tabbas kai zaka fada ciki tsundum”  “Tabbas hakane Amal, yanzu gashi nan ya fada ciki ay” “Allah dai ya kara rufa mana asiri ya kuma sa iyakar wahalar kenan” “Ameen ya Allah”  “Kiyi baccin ki kar ma kisa abin a rai kizo ki kasa bacci, and gobe kinsan aiki za’ayi maki, just relax and sleep ok?” “Ok” “That’s my sisi” Tayi murmushi  “I just missed you Amal” “Me too ya Samha” “Good night Amal” “Sweet dreams” “You too”



*****   Tun 7:30 mom da Hilwa da mijinta suka iso Shatu da Adeel na biye dasu, ba’a juma ba Areef yazo shida matarsa Sadiya. Nan suka fara jiran zuwan likita, shine baizo ba sai 9:30, shigowa yayi da dawo yana duba time “Am sorry kunganni sai yanzu, sorry for the delay” “Bakomai” mom tace Kayan theatre yabama mom ta saka ma Samha, shi kuma ya wuce don kimtsawa tare da wanda zai taimaka masa a aikin. Around 9:53 ya dawo tare da wheelchair aka dora Samha, nan kowa yayi mata addu’ar fatan dacewa suka shige....    Sune basu fito ba sai wurin 11:39, gurguro ta akayi saman gado kamar gawa, a dakinta aka kaita aka maida ita kan gadon dakin Doctor din ya kalli mom yana murmushi  “Zata farka nan bada dadewa ba, data farka zata bude idonta insha Allah” “Mungode” “I will come back and check on her later, Allah bata lafiya” “Ameen” Areef ya kalli mom “Mom bari naje na dawo, idan ta tashi just call me” “Okay a dawo lafiya” tare suka fita da mijin Hilwa da Adeel”   A hankali take motsawa, kusan second 15 sannan ta fara kokarin tashi zaune. Taimaka mata mom ta tashi tana kokarin bude idonta ta kasa, da kyar ta bude kadan taji wani irin haske tayi sauri ta rufe, sake budewa Tayi a hankali har ya bude gaba daya, biji biji take gani kafin ta fara gani tas! Idonta ya sauka kan su mom da suka jera layi kamar zasuyi assembly, wani irin murnar dadi tayi ta rufe bakinta da hannunta cike da jin dadi harda dan guntun qwalla tace “Mom...!” Tayi hugging nata sosai. Sun dau lokaci a haka suka saki juna Samha tayi dariya  “I can see! Amal! Ya Hilwa! Wow! Omg my eyes are finally back!” Tace tana hugging Amal da Hilwa a tare. “Yes you’re back Samha! You can see now” Hilwa tace tana murmushin jin dadi “Alhamdulillah ya Samha Allah kara maki lafiya”  Janyewa sukayi daga hugging din Samha ta kalli Sadiya “Who’s she?” “Oh that’s our inlaw, ya Areef’s wife” Ware ido Samha tayi cike da mamaki, kafin ta bude hannu nan Sadiya ta bata big hug. “Allah ya kara miki lafiya” “Ameen” Hannun Shatu mom ta kamo dake bakin kofa tsaye ta kawota gaban Samha “Ga Shatu”  Shiru sukayi dukkansu suna kallon juna, Shatu ji take kamar ta shako ta while Samha na kokarin danne nata kishin, cuz ba amfani anyway tare zasuyi zaman kishi suyi sharing miji daya.  Hannunta Samha ta kamo tana murmushi  “Shatu Nagode da kulawar da kuka bani, Allah saka da alkhairi” “Ameen” tace ta tafi ta nemi wuri ta zauna “Oya tashi kiyi wanka, nasan da Doctor yazo zamu tafi gida” cewar Hilwa Kalle kalle ta farayi “Ina Fawzan?” “Oh sun fita dasu Ya Areef, mom zata kirasu yanzu”  Wanka tayi ta shirya cikin dark blue atamfa dinkin riga da skirt, rigar peplum aka mata sai straight skirt, fesa turare tayi, tayi kyau don ma ta rame sosai tayi duhu, sai idanunta da suke a dan kumbure da baki baki wurin.  Tana gamawa Doctor Hamza ya shigo dashi da nurse  “Masha Allah, our patient is awake and back again” Tayi murmushi  “Sai gida ko?” Yace yana kar6ar file dinta daga hannun nurse Rubuce rubuce yayi bayan ya gama ya mika ma mom “Magaungun da zata nasha ne, akwai supplement a ciki naga tana bukatar su, sai cream za’a dinga shafa mata a saman idon wannan baqin zai washe a hankali” “Insha Allah” mom tace “You can go home now, Allah kara lafiya” “Ameen”  Yana fita Sadiya da Shatu suka fara tattara kayan, Hilwa kuwa in banda kwadayi ba abinda takeyi, mom ce ta fita zata siyo magungunan da kudin dakin da suka kwana zata biya. Yafa dan karamin gyale Samha tayi bisa kai tana tayasu tattara kayan, Hilwa ce ta hana ta “Basshi mun gode samu wuri ki zauna” Fita sukayi suna kai kayan mota Hilwa na taya su tana mita, zaune take kan kujerar dakin taji muryarsa ta daki dodon kunnenta, a hankali ta daga kai ta kalle shi take zuciyarta ta tsinki, tsayawa yayi yana kallonta itama haka, kafin a hankali ta tashi ta isa gabansa, fuskarsa take bi da kallo cike da al’ajabi tace “Fawzan? Daman na fada maka duk ranar da ido na suka bude zan tabbatar maka” Yayi murmushi  “Bazanyi gardama dake ba, yaya jikin?” “Alhamdulillah, gashi kana ganin ina kallonka” Yace “Kwarai kuwa naji dadin haka” “Baby sis!” Muryar Areef taji da gudu ta fita taje ta bashi big hug, komai ta tuna kuma tayi pulling back tana yamutsa fuska “What?” “Fushi nake dakai” “Da nayi me?” “Da kayi aure bana nan” “Ohh! Am soooo sorry baby sis, please forgive yaya Areef” yace yana kama kunnuwansa, hakan ya bata dariya ta sake hugging nasa “Forgiven” “That’s my sis” Adeel kuwa yana gefe yana murmushi “Oya kuzo mu tafi gida” mom tace tana karasowa inda suke.   A mota ne Samha tace “Don Allah muje polices station, I want to tell Haidar something” Hilwa tace “Haba mana gobe fa za’a je court, kar ki 6ata lokacinki a banza, kisa muyi 6arnar man mota kan wannan banzan” “Please” tace kamar wata mage “Okay” Areef yace bayan mom tasa baki akan a bari taje ay yanzu mijinta ne, amma five minutes zatayi Dadi taji yau Haidar zai raina kansa. Kwana Areef yayi ya dau hanyar police station din, da zuwansu ta shiga ciki inda ta samu aka hada ta da wata policewoman ta kaita cell din Haidar.  Tana shiga ta tsaya tana murmushin mugunta  “Aliyu Haidar!”  Yana ganinta ya taso ya dafa karfen ta ciki yana kallonta cike da mamaki. Matsowa tayi daf dashi tana clapping hannunta....      



Eid mubarak to all  muslim around the globe ๐Ÿ”›♥️

No comments: