Friday 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 43-44

๐Ÿ’„Fawzan ko Adeel?๐Ÿ’

  Written by Sa’adatu Sada✍๐Ÿป
Story by Maryam Sb (MSB) ๐Ÿ˜˜๐Ÿ’•    

๐Ÿ‘„๐Ÿ’‹  


   Page 43-44    


“Samha, Haidar yana dauke da cutar HIV, ya goga mun ya goga ma yayan mutane bila adadin, Samha Haidar dan fashi da makami ne wannan sana’ar tasa ba wanda ya sani hatta iyayensa da yan uwansa basu sani ba, a waje kallon mai kirki ake masa wanda sai kayi zaton ko kuda bazai kashe ba, amma Samha Haidar mugu ne na karshe baida digon imani a zuciyarsa, nidai yanzu tsoro nakeji kar yazo ya gammu nan, he can go to any length to get what he wants, Samha duk rintsi duk wahala kar ki bari ya kusance ki zai shafa maki kanjamau, nima daya shafa man kaddara ce data riga fata, amma ke Samha tunda kinsani kar ki yarda ki kwatar wa kanki yanci! Kar ki bari ya salwanta rayuwarki kinada sauran kuruciyarki.  Samha.  Haidar da dukiyar haram yake amfani, haram yake ci, wannan makeken shagon nasa gaba daya ba halal cikinsa, da haram yake ci yake sha yake tufafi”   “Hasbunallahu wani’imal wakeel... Insha Allah koda wasa bazan barsa ya kusance ni ba, Saudat nagode sosai da kika fada man wannan maganar”  Ta dafata “Kar ki damu alkawari ne na dauka duk wata mace da ya kawo zan sanar da ita halinsa kafin ya gama da rayuwarta”  “Nagode, amma kun dade tare ne?”   “Eh shekarar mu uku dashi”  “Subhanalillah amma shine kika kai wannan lokacin dashi? Bazaki nemi hanyar guduwa ba?”  Tayi murmushin takaici  “Samha duk yadda kike tunanin Haidar ya wuce nan, duk rintse idonsa na kanka bazai taba bari ka gudu ba”  “To wai a ina kike kwana?”  “Sashe na yana nan gaba kadan, amma sai kin fita daga nan sashen kwata kwata”  “Amma dazu ni kofa daya kadai nagani cikin gidan nan”  “Kofar boyayya ce bakowa ke ganewa ba”  “Ikon Allah, inda kinga kulawar da Haidar ke mani sai ki rantse ko kuda bazai bari ya taba ni ba”  “Samha kenan, haka yake indai yana so ya cimma burinsa makirin mutum ne, wuyarta ya kyalla ido yaga mace tofah sai inda karfinsa ya kare”  “Sheyasa har yau mamaki abin ke bani, amma fa Saudat kinyi kokarin zama dashi ke meyasa bai rabu dake ba kamar sauran?”  “Wallahi yaki rabuwa dani a cewarsa har yanzu baigama daukar fansar abinda mahafina yayi masa ba”  “Ikon Rabbi! Toh me yayi masa haka?”  “Wallahi Samha bansani ba”  “Allah ka bamu mafita”  “Ameen amma jikinki duk ciwo Samha kema ya dauki alhakinki da yawa”  “Ay in fada maki wallahi na dauka mutuwa zanyi, Allah kadai zai iya saka mana wannan cin zali nasa, Insha Allah zaiga sakamonsa ay Allah bazai taba barinsa haka ba”  “Insha Allah, kedai kar ki manta da abinda na fada maki duk rintse duk wahala kar ki bari ya kusance ki”  “InshaAllah bazan bari ba, zanyi iya kokari na”  “Yawwa Samha bari na koma kafin ya dawo banso ya gammu tare idan ya gammu akwai matsala”  “Gaskiyanki, toh Saudat nagode sosai Allah ya saka da alkhairi”  “Ameeen ya Allah, na tafi” daga haka tayi sauri ta ficce daga parlon ta bar Samha baki sake tana mamaki.  Wanka Samha tayi ta shirya cikin wata atamfa maroon color dinkin A shape ne, tana fitowa mai gadin wajen gate musamman ya aje shi saboda tsaro kamar wani yazo shi zai fara cin karo dashi, kuma shi ke ba guards signal da kowa ya boye indai Haidar zaiyi baki ko sun shigo basu ganinsu. Shi ya shigo da basket hannunsa yana washe baki.  “Madam ga abinci inji mahaifiyar oga”  Kar6a tayi ta aje don ita bata marmarin wani abinci, yanzu matsalar ta uku Zuwa hudu, na farko yadda zata rabu da azzalumin mutumin nan, na biyu yadda zata tona masa asiri kuma tanaso hukuma ta hukunta shi, na uku cigaban karatunta, da wannan tunanin ta shige dakinta ta rufe da key.      ***      Karfe hudu daidai ta farka, bayan tayi sallah tafara tunanin fitowa don batasani ba koya dawo, zamanta tayi dakin har akayi magrib, nan tayi sallarta har dai akayi isha’i bata tashi ba, a tsorace take kar ya dawo amma dai ta dake duk da ta rufe kofar da key amma yan cikinta basu daina juyi ba, shirin baccinta tayi duk da yunwar dake addabarta amma taki fita ta bude don gaskiya bataso su hadu.   Kwanciya tayi ta dukunkune wuri daya tana addu’a Allah yasa kar yazo ya addabe ta da knocking. Har dai bacci 6arawo ya sace ta.  Kiran farko ta farka, tayi mamakin ganin bai tashe ta ba, kodai baya nan ne? Addu’a take Allah yasa ma idan ya tafi kar ya dawo koma ya mutu. Da wannan tunanin ta shiga toilet ganin al’adarta yasa taji wani irin dadi tasan dai komin kwakwarsa ya rabu da ita. Kimtsawa tayi ta fito ta yi yan addu’ointa sannan ta kishiginda ta koma bacci, koda ta farka batasan ko karfe nawa bane don ba waya hannunta.   “Samha ki fito kici karya inaga Haidar baya gari kila ya tafi fashi da makami fa”  Oh Allah! Wai sai dai ace mijinka ya tafi wannan gur6atacciyar sana’ar da ko dadin ji babu?  “Samha! Kinaji na? Nace ki fito ki karya baya nan”  “E..hh inaji Saudat gani nan, nagode”  Fitowa tayi nan taga Saudat tsaye da cooler din abinci. “Gashi kici, don Allah ki dina kulle kanki cikin daki ke kadai ba kyau. Anything can happen a rasa yadda za’a shiga a bude”  “Toh ya zanyi tsoro nakeji kar ya dawo”  Yar dariya tayi “Ki kwantar da hankalinki idan yayi tafiya, irin wannan tafiyar sai ya kwana biyar bai dawo ba, don haka enjoy yourself while it lasts”  “Nagode”  “Toh kici abinci ko, bari na tafi”  “A’a ki tsaya nan muyi kallo mana dan hira”  “Toh shikenan Samha nagode”  Kunna masu tv tayi nan suka yi ta kallo suna hira gwanin dadi. Sallah kadai ke tashin Saudat kasancewar Samha na hutu.   Haka kullum suke wuni suna kallo, tun suna sa ran dawowarsa har suka manta suka saki jikinsu.     ______   Zaune take a daki tana kallo kasancewar dakin akwai tv, ita sam ta daina rufewa yanzu saboda taga baida niyyar dawowa.  Haidar ya wani hankado kofar bam! A razane ta mike ganinsa yan cikinta suka kada suka bada wani kulululu!    “How dare you go against my orders!?” Abinda ya fara fadi kenan yana shigowa  “Uhm... I don’t understand what you mean?” Ta fada cikin rashin fahimtarsa  He moved dangerously towards her idanunsa wane kura taga nama.  “I said how dare you? Waya baki izinin magana da Saudat?”  “I still don’t unders...”  Bata karasa ba a sanadin gigittacen marin da ya kai mata, Ya Allah har ta manta yadda dukansa yake, ihu tasa, squeezing gashinta yayi take ta kara sautin ihunta.   “Are you now both spying on me? Hade kanku kukayi zaku zama friends? Uban me ta fada maki a kaina?”  “Bata fada man komai ba...”  “Don’t you dare play dumb with me Samha,  bazai maki da kyau ba kinsani sarai! Zan iya halaka ki ko daya daga cikin members na family dinki karamin aikina kenan...!”  Kyarma ta farayi jin ya ambaci family dinta, wani karfi yazo mata take ta kalle shi cikin ido cike da tsana tana nuna shi da yatsa.  “You have got the wrong person this time around Sir Aliyu Haidar! It’s enough of what you did to me, I have tolerated enough from you and now don’t you dare attack any of my family I am warning you!”  Dariyar mugunta yayi, sannan kuma take ya daure fuska yana kallonta cikin ido, tana kallon anger cike a fuskansa. Tsoro ya cikata ta fara kyarma  Wuyanta ya shako sannan ya daga ta sama, juyi yake da ita tana ihu wullata yayi take kanta ya bugi tiles!  Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah!  Kwallo ya shiga yi da ita yana harbinta da kafansa, ihu take iya karfinta cikin azabar ciwo, ya cigaba da kai mata duka da kafa tun tana gani biyu biyu har idonta ya rufe ruf....!                    Thanks for reading! ๐Ÿ˜ท

No comments: