Friday 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 13&14

πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’


Written by MSB✍🏻 
Story by Maryam Sb (MSB) πŸ˜˜πŸ’• 




πŸ‘„πŸ’‹




Page 13-14


A hankali ta bude idanuwanta da take jin kamar buhu aka daura masu, take ta maida ta rufe su gam gam saboda hasken dakin, kanta ta dafe dake barazanar rabewa biyu, dark lashes nata ta motsa ta dan kalla inda take, take ta gano tana asibiti ashe,  batasan meya kawo ta asibiti ba amma kuma events da suka faru suka shiga dawowa mata she began panicking duk da idanuwanta were half open take ta fara kokarin tashi zaune. 

“Samha, Alhamdulillah Allah kin tashi?” Mami tace cike da damuwa. 

“Ina zakije? Calm down ya Samha bakida lafiya” cewar Amal. 

“Sorry baby sis, Allah baki lafiya” cewar Areef dake zaune gefenta


“Faw...” she began with an itchy throat, Amal tayi sauri ta debo ruwa suka shiga bata a hankali itada Areef, kadan tasha ta shiga ture cup din da hannu. Da suka tabbatar ruwan ya shiga makoshinta Amal ta mayar da cup din ta aje. 


“Ya jikinki yata, take heart kinji?” Cewar Abba mahaifin Fawzan. 


Kallonsu take yi daya daya kamar taga sababbin halittu taki cewa komai, sai ido kawai. 
Bude kofar dakin akayi aka shigo Hilwa ce ta shigo da sauri mom da dad na biye da ita a baya. 


“Samha!” Cewar Hilwa tare da hugging nata tana kuka. Take kowa ya soma sharar kwalla. 


Janye jikinta tayi a hankali tare da riko fuskanta da hannuwanta duka biyun
“Ya jikinki? Kiyi hakuri kinji dukkan mai rai mamaci ne” 


“Allah baki lafiya ya kuma gafarta masa” cewar mom da dad


Kallon mamaki Samha kema Hilwa da su mom, sannan ta shiga ture Hilwa daga kusa da ita a tsorace tana ja baya. 


“Meye haka Samha?” Ta fada cike da mamaki

Still kallonta Samha keyi taki cewa komai tunda tace Faw.. bata kara magana ba. Jikin kan gadon asibitin ta jiginta tare da kura ma wuri daya ido bako motsawa, tafi minti goma a haka, tuni sun fara tsorata suna ta magana amma taki kallon kowa kuma taki motsawa daga inda take.


“Areef yi sauri ka kira Doctor” cewar Dad 

Da sauri Areef ya fita inda mom ta dawo kusa da ita tana cigaba da mata magana amma yadda take haka take tsorata kam sun gama tsorata. 


Minti kusan uku sannan Areef ya dawo shida doctor a tare. 

“Sannunku” yace da mutanen daki

“Yawwa Doctor duba mana ita taki magana ta kuma ki motsi” mom ta fada tana mikewa daga kan gado don bashi wuri. 


“Samha ko?” Doctor din ya fada yana kallonta.

Bata kalleshi ba haka ma bata motsa ba. 
Examining dinta ya shiga yi har kusan 30 seconds sannan ya mike yana kallon su mom.


“Tunda ta samu labarin nan tayi kuka?” Ya fada yana kallonsu

“A’a doctor” cewar Mami 

“You have to get her to cry, that’s the only way da zata samu saukin radadin dake zuciyarta, she’s in a lot of pain wallahi, yin kuka a gareki shi zai sassauta mata abinda takeji”


“How doctor?” Cewar dad yana kallon Doctor din.


“I don’t really know, i think kuyita nanata mata mutuwarsa kuna girgiza ta kila zatayi kuka, but ba guarantee, just try she’s lost in her own world” 


“Ok doctor zamu gwada”

“Allah ya bata lafiya, kuna iya tafiya gida zan sallame ta yanzu”


“Mun gode doctor”













***






Jawo ta mom tayi daga kan gadon asibiti, bayan ta samu ta mike tsaye ta shiga tafiya da ita, yadda kukasan gunki haka ake janta amma idanuwanta na nan kafe jikinta ma ko motsi batayi, kafafuwanta ke motsi shima sai inda akayi da ita. 




Bayan sun isa gida suna kai ta dakinta suka zaunar da ita kan gado.
“Hilwa kawo mata koda tea ne, rabonta da abinci tun shekaranjiya” 


Bayan an kawo tea mom ta zaune don bata, amma ina tama ki bude bakin bare tasa ran zata sha, tafi minti biyar tana kokarin bata tea dinnan amma ina, tayi fadan tayi rarrashin, tayi nasihar amma ina a banza. Samha ko motsawa ma batayi.


Data gaji ta ajiye tea din bisa drawer ta mike tana kallon Dad
“Wai ya zamuyi ne da ita?”


“Abinda Doctor yace, shi zamuyi”

“Toh ko na gwada?” Cewar Hilwa tana kallon mom da dad. 

“Eh gwada” cewar dad.


A hankali ta taka gadon ta zauna tana kallonta, second kusan goma tana kallonta cike da tausayawa kafin tayi karfin halin cewa

“Samha, Fawzan is no more, ya riga ya amsa kiran mahaliccinmu, ya rasu”
Ta fada tana kallonta amma ina ko motsi batayi ba. 

“Fawzan ya rasu Samha!” Ta fada da dan karfi hawaye na sauko mata. 

Nan ma dai bata motsa ba.


Nan ta shiga girgiza ta da karfi tana fadin
“Ko ki yarda ko kar ki yarda ya riga ya rasu! He’s no more! Fawzan ya koma ga Allah! Kina jina Samha! Fawzan ya rasu! Ya rasu! Ya rasu! Ya rasu!” Ta fada tana girgiza ta iya karfinta tana kuka.


A hankali tasa hannu ta ture Hilwa sannan ta zagayo da kwayar idonta tana kallon Hilwa tana girgiza kai 

“A’a bai rasu ba” 


“Ya rasu!” Cewar Hilwa cikin tsawa

“Bai rasu ba” ta fada tana kallon kofa

“Ya rasu!”


“Bai rasu ba”

“Nace ya rasu!”

Dad’e kunnuwanta tayi da hannuwanta iya karfinta sannan ta kurma uban ihu tuni mutanen dake cikin dakin sun tsorata, haka ta dinga ihu kamar sabuwar mahaukaciya bako tsayawa, magana suke mata amma ina kururuwa kawai takeyi tama ki sauraronsu. 



“Ya zamuyi yanzu?” Cewar Areef a tsorace

Mom, Hilwa da Amal daman tuni kuka suke.

Dad ne yayi karfin halin matsawa kusa da ita  tare da rungumota, kwace kanta ta shiga yi tana cigaba da ihunta, haka suka dinga kokowa da shi da yake karfinsa dana ba daya bane tuni yayi hugging dinta gam gam, addu’a ya shiga yi mata inda ya umarci mom ta kira family doctor dinsu, har kyarma take wurin dialling number din. 


20 minutes ya dauka kafin ya iso. Yana shigowa ya soma jin ihu, da yake family doctor dinsu ne shigewa kawai yayi. Yana zuwa mom ta soma cewa

“Ta haukace ko?”


Yayi murmushin karfin hali yana kallon Samha yace 
“No da hankalinta, zan mata alluran bacci idan ta tashi she will be calm” 


Alluran aka shiga kokowan yi, sai da Areef da dad suka danne ta aka samu akayi. 

Minti kusan daya ihun ya fara raguwa, tun tanayi har ta koma yi sama sama idanuwanta suna rufewa, nan da nan ta kasa ihun kafin a hankali bacci ya kwashe ta mai nauyi.



No comments: