Friday 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 63-64

πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’  


Written by MSB✍🏻
Story by Maryam Sb (MSB) πŸ˜˜πŸ’•    

πŸ‘„πŸ’‹  


Previous page supposed to be 61-62 afuwan y’ll πŸ’•  



Page 63-64  



*******2weeks later   Haka rayuwar Samha ta kasance a kauyen su Adeel har ta saba da mutanen kauyen da kuma rayuwarsu. Gwaggo ko ta maida ita tamkar mahaifiyarta duk wani abu da ya shige mata duhu ko damuwarta takan fada ma Gwaggo ta kuma bata shawara mai kyau. Adeel kuwa yana matukar kulawa da Samha hakan ke kara qular da Shatu kishi ya turnike ta tamkar zata rusa ihu. Kullum cikin bata labarai yakeyi wani lokaci na ban dariya ko kuma na tausayi. Hakan yasa ta gane mutum ne shi mai son barkwanci sosai, har dasu Gwaggo yi yake ya maida su tamkar kakkaninsa. Kusan kullum sai Adeel ya kai Samha rafi don ya lura is her favorite place a kauyen, yawanci da anyi la’asar suke zuwa suyi zamansu karkashin bishiyar mango suna hira, a hankali Adeel ya shaku da Samha wanda indai har suna tare yakan kasance cikin nishadi marar adadi. Ita ma Kuma soyayyar da take ma Fawzan har yanzu bata gushe ba sai ma karuwa don haka Adeel yana da special place a zuciyanta, don a cewarta Fawzan ne ba Adeel ba.  Yau ma kamar kullum suna zaune karkashin bishiyar mango suna ta hira Samha tace “Wai nikam har yanzu baka fada man labarinka ba? kamar yadda na fada maka nawa” Yayi yar dariya “Khadija kenan, dan kauye har wani abin fadi yake dashi?” Ta dan 6ata rai “Eh mana, kawai ka fada mun nidai” “Toh ni dan kauyen nan ne, iyayena sun rasu” Cikin rashin fahimta tace “Ah bangane ba, su Gwaggo da Baffa fa?” “A hannunsu na tashi amma su suka fada mun iyayena sun rasu ina karami” Ta dan gatsi mango bayan ta hade tace “Uhm sheyasa nace kaine Fawzan, ta yaya bazaka san iyayenka ba?” “Bani bane, iyayena sun rasu Baffa kanin babana ne” “Haka dai kace, amma zan tabbatar maka kaine Fawzan” Dariya yayi sosai “Kin cika rigima, amma bani bane” “Kaine Allah” ta fada cikin dariya “Tam naji, nine shikenan ko?” Tayi murmushi  “Wai yau naga kamar kina cikin nishadi?” Ta kara murmusawa “Ba dole na kasance cikin nishadi ba har har ka manta gobe za’a bude mun idona? Gobe zan ga Fuskar dana dade bangani ba, gobe zan ga haske zanga mutane, zanga ruwa, zanga gidaje, zanga komai” ta fada cikin jin dadi. Cike da nishadi yace “Tabbas gobe zaki fara gani, ina tayaki murna” ya fada yana kalle kalle ganin duhu ya fara yi “Tashi mu tafi gida haka nan kinji?” “Tam” tace tana kokarin tashi tsaye, sandar ta kama ya rike suka cigaba da tafiya suna hira. Suna tsakar tafiya ne ya kalle ta cike da zolaya yace “Yanzu fa shikenan kin zama yar kauye kema kenan?” Dariya tasa “Kamar yadda ka zama ba” Ya fadada murmushinsa “Khadija kenan” “Fawzan kenan” “Bawani bashi bane” “Shine” “Bashi bane” “Shine” “Bashi bane” “Shine” Haka suka cigaba da fadi har suka iso kofar gida suna ta dariya.  “Ka bar mun kenan shine ko?” “Meyasa kikace haka?” “Gashi kayi shiru” “Ay mun iso gida ne sheyasa” “Bawani nan” Dariya sukayi duka suka sa kai cikin gidan, Ya gaida Gwaggo dake gyara masu tabarmar da zasu zauna a kai. Samha ta zauna shi kuma Adeel daki ya nufa wurin Gwaggo data shiga ciki bayan ta zaunar da Samha kan tabarmar. Hira sukayi da Gwaggo sama sama yana zolayarta tana ce masa shirin sallar magriba zatayi ya rabu da ita. Fitowa yayi tsakar gida ganin ba kowa yayi sand’a ya kwace mata sandar dake hannunta. Yar kara tayi tace “Waye?” Kashe murya yayi yace “Nice Khadija” ta kyalkyale da dariya sosai, cike da nishadi yake kallonta, shiko ya rasa me Samha ta ma zuciyarsa gaba daya ta gama dashi. Zama yayi a gefenta yana jin wani sabon al’amari a zuciyarsa game da ita, amma idan yana tuna tana da aure sai yayi saurin kawar da tunanin daga ransa, amma duk yadda yaso yin hakan ya kasa, ya gamsu yana son Samha kuma ya kudiri duk randa aka raba aurenta da mijinta zai maye mata gurbinsa, zai sata farin cikin da ta rasa a rayuwar aurenta, zai jiyar da ita dadin zaman aure.... “Fawzan...!” Ta fada da karfi a karo na biyar “Ya akayi Khadija?” “Lafiya kayi shiru tun dazu nake ta kwala maka kira haka?” “Lafiya lau, ina sauraren kiran sallah ne” “Tun yaushe aka gama kiran sallah?” “Ah haba!?” Yace yana tashi da sauri tare da ficewa daga gidan. Murmushi Samha tayi ta lalubo dakinta ta shiga don yin lazumi don tana hutun sallah ita. Shatu ta fito tsakar gida kamar tasa ihu haka takeji.

Sai da akayi isha’i ya shigo gidan, direct dakin Samha ya zarce ya ci karo da ita tana ta karatun qur’ani tana haddarta kamar kullum, abin na matukar burge shi yadda take da riko da addini duk da tana cikin wani hali. “Fawzan?” Tace tana motsa fuskarta “Uhm ya akayi kikasan ina nan?” “Zuciyata ce ta sanar dani” Kusa da ita ya koma ya zauna kan katifarta tare da tallabe hannayensa duka biyun a fuskarsa yana kallonta.  “Yadai?” Tace tana russuna kai “Menene?” Yace da ita yana murmushi  “Naji alamun kana kallona ne” “Kodai kina gani Khadija?” Yar dariya tayi “Ina ganinka da zuciyata Fawzan” “Wannan mutum yanada wuri na musamman a zuciyarki” “Wakenan idan ba kai ba?” “Shi mana” Cikin dariya tace “Kaga kar mu fara musu da kai bacci nakeji ka tashi ka fita daga dakinnan” “Naqi wayon ba inda zanje” “Shikenan matso da kunnenka kaji wani abu” Matsowa yayi gamida lumshe ido, dagewa Samha tayi ta saki wata uwar kara a kunnensa. Matsawa yayi a firgice ta kyalkyale da dariya. “Kai ashe ke muguwa ce Khadija bansani ba! Kin tsoratani fa sosai” “Toh ay na fada maka bacci nakeji kaki tashi ka fita, inaga wannan ce kadai hanyar da zan koreka daga nan!” “Sai na fadi ma Gwaggo!” Yace yana kwala ma Gwaggo kira Lekowa tayi daga bakin kofa.  “Barkindo lafiya wannan kira haka?” “Gwaggo kinga Khadija ko?” “Me tayi?” “Laa zaka hadani da Gwaggo ina zamana lau, Gwaggo shine fa yayi mun ihu a kunne, kila ma na kurmance fa” Mangare mashi kai Gwaggo tayi “Wane irin mugunta ne haka Barkindo?” “Kuma yanzu abin kaina ya dawo, toh da kyau kun hade mun kai!” Inna ta kwashe da dariya Samha ma haka, daga karshe shima yasa dariya, a daidai nan suka ji ihun Shatu a bayan Gwaggo. “Menene ke?” “Gwaggo faduwa nayi na bige kafa!” “Toh! Wudu muyal (yi hakuri/sannu) tashi muje na duba kafan” Zum6ura baki tayi ganin Adeel bai wani damu can ba ta mike da sauri “Ay banji ciwo ba Gwaggo” daga haka tayi saurin shiga dakinta cike da takaici (wayaga attention seeker!)...   Misalin karfe uku da rabi na dare hayaniya ce ta tashi Samha, gashi ba gani take ba ballantana tasan shin dare ne ko safiya? Da sauri ta mike jin hayaniyar tayi yawa yasa ta lalubo sandarta dake kusa da ita a ajiye. Mikewa tayi tana dogara sandar tana bin hanya ta samu ta fito daga dakin. Ihun mutane take taji daga waje da alamar kamar gudu akeyi. “Gwaggo...?! Fawzan....?!....Shatu....?!Fawzan!!!” Jin shiru yasa hankalinta ya tashi matuka, hanya ta fara lalube da sauri ta fito zaure tana sa kunne jin dai da gaske hayaniyar ce yasa gabanta ya fada. Shin meke faruwa haka kuma dare ne ko safiya? Hannunta taji an damqo yasa ta saki kara, toshe mata baki akayi da sauri  “Nine Khadija, kiyi shiru garin ba lafiya, wasu ne suka shigo kamar daga sama suka fara cinna ma garin wuta!” “Innalillahi wa inna ilahir rajiun... Su waye?” “Bansani ba wallahi” “Ina su Gwaggo?” “Na neme su na rasa sai Shatu na gani tana can na 6oye ta wani wuri zamu lalla6a muje mu same ta, don za’a iya sa ma gidan wuta muna ciki” Kyarma ta fara duk ta tsorata, a hankali suke tafiya garin sai hayaqi ke tashi, tari sukeyi a nan suka toshe baki suna cigaba da tafiya. Haka suka dinga tsallake wuta da kyar suka isa bayan wani katon icce inda Shatu ke tsaye a 6oye. “Yanzu ya zamuyi?” “Zaku iya jira nan na dubo su Baffa?” Da sauri suka ce a’a Karar tafiya sukaji kusa da su, 6oyewa sukayi su duka inda aka daka tsawa da karfi “Samha! Wallahi ki fito tun kafin na ganki da idanu na! Ki fito nace! An tabbatar mun kina cikin garinnan! Wallahi idan baki fito ba zan kashe kowa da kowa na cikin garinnan da ke kanki! Ki fito tun wuri in ba haka ba zan cigaba da kunna ma garinnan wuta!” Gabanta yayi mummunan faduwa, kyarma ta fara yi inda ta toshe bakinta da hannunta tare da hadiye wani miyau mai karfi.....!              



God bless y’ll! πŸ’•

No comments: