Friday 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 61-62


πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’


Written by MSB✍🏻
Story by Maryam Sb (MSB) πŸ˜˜πŸ’•    


πŸ‘„πŸ’‹    


Page 60-61  



Zaune suke gaba daya a parlon maama suna kallon labarai all of a sudden hoton Haidar ya bayyana akan screen din, cike da mamaki maama ta kalli Shukrah tace “Me kuma hoton Haidar keyi a...” “Shhh... see!” Zuwaira tace tana nuna tv din da mamaki inda suke sauraren me ake cewa “Wannan shine Aliyu Haidar wanda jam’ian tsaro ke nema ruwa a jallo, Aliyu Haidar an kama shi da laifuka kamar haka:  Na farko laifin kisan kai tare da amfani da sassan jikin yan mata yana tsafi dashi, Na biyu cutar da yara ta hanyar aurensu tare da azabarwa mai tsanani, Na uku munyi kwakkwaran bincike mun gano dan fashi da makami ne wanda suna aika aika a wurare da dama idan basu sami abinda suke so ba tofah suna kashe mutane, Haidar ya azabatar da matarsa da ya aura ba dadewa ba mai suna Khadija Ahmad (Samha), yarinyar tasha wahala hannunsa inda ta ku6uta daga hannunsa da kyar tare da kishiyarta Saudat Isma’il, yanzu haka yarinyar ta 6ata an neme ta sama ko kasa ba’a ganta ba, bincike ya tabbatar mana da cewar Aliyu Haidar shi ya tare mahaifin Samha akan hanyar sa ya nami yayi masa fashi inda basu samu biyan bukata ba suka harbe shi da bindiga a sanadin haka Allah yayi masa cikawa. Don haka muke son duk wanda yaganshi yayi gaggawar sanar da hukuma ba 6ata lokaci, duk wanda ya ganshi ya kawo mana shi gwamnati tayi masa alkwari kudi har naira million daya, don haka kar ku bari wannan gara6asar ta wuce ku, abu na gaba muna neman matar tasa Khadija data 6ata da Allah duk wanda ya ganta ya tuntu6e mu da wadannan numbers din kamar haka; 08132679801 ko kuma 07037637690” take hoton Samha ya bayyana a kan screen din tv din. “Iyayenta da yan uwanta suna cikin wani hali duk wanda Allah yasa ya ganta yayi gaggawar sanar damu, abu na karshe yan mata su hankalta da irin su Haidar don tsira da lafiyarsu domin Haidar mun gano yana dauke da HIV wato cutar kanjamau, hattara yan mata! bissalam ku huta lafiya” Tuni maama ta mike tsaye tana hada gumi hawaye ya wanke mata fuska, nuna tv din takeyi tana girgiza kai “Karya ne, wallahi karya suke sharri ne zasu kullawa dana” “Maama ki kwantar da hankalinki ba abinda zai samu Haidar da izinin Allah” “Yanzu sharrin da Khadija zata yi ma dana kenan? Abinda zata saka min da shi kenan? Ta bibiyi autana da sharri haka kurum!” “Yi hakuri, ki daina kuka InshaAllah Samha sai ta gane kurenta” “Shukrah in zama ne batayi dashi ta nemi saki amma basai ta yi masa sharri ba, dana da ko quda bazai iya kashewa ba ta yaya za’a danganta shi da mai kisan kai?” “Hakane maama meyasa Khadija zatayi mana haka? Yarinya mai hankali da tunani ashe ashe?” “A gaskiya bazai yuwu ba, akan me? Tashi muje ki kaini gidan nasu inga uwarta su fadi dalilin da yasa sukayi ma dana sharri? Me ya tare masu?” “A’a maama wannan fa zubar da mutunci ne kar kuje don Allah” “Rayuwar dana na cikin garari kice zubar da mutunci? A’a abinda yafi mutunci ma ya zube nace ki tashi! Idan bazaki kaini ba ay inada driver sai ya kaini” Ba yadda ta iya haka ta tashi suka fito da Shukrah da Zuwaira da Asma’u.   Da isarsu kofar gida maama ta fito a fusace ta shiga gidan yaranta suka bi bayanta. Mom na zaune parlor sanye da hijabi da carbi a hannunta, Amal da Saudat ma haka duk sun hada tagumi abin duniya ya ishe su.  Kai tsaye suka shigo babu ko sallama, ta dago tana kallon maama tayi murmushi. “Toh ashe baki ne a gidan namu, Bismillah ku shigo ku zauna” “Dakata marar mutunci! Ba zama ya kawo ni ba, nazo inji dalilin da yasa kuka yi wa dana sharri haka kurum mai ya tare maku?” “Ina kwana?” Saudat da Amal suka ce cikin ladabi da biyayya “Da ban kwana ba da kun ganni nan?” “Amal ku shiga ciki” da wuri suka haura upstairs.  “Hajiya Jamila, don Allah kiyi hakuri zan maki bayanin komai, abin bai kai na tashin hankali ba” “Ni ba wani bayani da zakiyi min in gamsu, har sai kunje kun janye karar da kuka kai ta kullawa dana sharri, ina Khadijar munafuka ki fito nan mana, zaku wani 6oye ta cikin gida” “Wallahi wallahi bamuyi wa danki sharri ba Hajiya, wace riba zan samu nayi masa sharri?” “Waya sani abu a duhu?” “Innalillahi wa inna ilahir rajiun! Don Allah ki saurare ni Hajiya na rantse da Allah maganar nan babu sharri a cikinta, duk abinda kikaji Haidar ya aikata su, ya azabtar mun da diya ya wahalar da ita, yanzu haka mun nema ta mun ra...” “Dakata banason bayaninki marar ma’ana da dadin sauraro, abinda nasani kawai shine kuje ku janye kara” “A gaskiya bazata janyu ba har sai an nemo mun diyata an kuma kwatar mata yancinta” “Aww! Haka zakice bayan kunyi masa sharrin? Wane yancin ma tukunna ? Ay sai dai a kwatar wa da dana yanci ba dai yarki ba” “Hajiya Jamila wai wane sharri? Maganar nan haka take ba sharri cikinta, kina zaune da danki bakisan halin da yake ciki ba wace irin uwa ce haka?” “Aww! Kuma yanzu magana zaki fada mun? A dakeni sannan a hanani kuka? Toh wallahi ina kara fada maki ku janye karar nan tun wuri, don nidai dana ba abinda yayi” “Haka dai kikace, amma danki yayi laifi dole za’a hukunta shi, don haka kije kiyi binciken halin da danki yake ciki wata kila xaki fahimta” “Nidai na fada maki, ku janye kudurinku tun wuri” “Bafa za’a janye ba yata ta bata yau kusan sati uku bamu ganta ba sai kice mu zauna mu sa ido kawai? Ina ay hakan bazai yuwu ba ma sam” “Toh shikenan shege kafa sa dan halak sai yanka” “Kidai yi hakuri ki binciko rayuwar danki shine kawai abinda zan iya cewa” “Kisani dana ko quda bai iya kashewa ballantana dan adam haba, idan wani abin yayi maku da bai maku ba kuyi hakuri amma banda sharri da Allah” “Allah yasani bamuyi ma danki sharri ba, yancin yata kawai nake bukata a kwatar mata” “Kisa fa kina nufin a kashe shi shima?” Sai ta fashe da kuka, su Shukrah na bata hakuri “Don Allah kiyi hakuri maama Allah zai bayyana mana gaskiya” “Bani nake da hukunci hannuna ba sai abinda hukuma ta yanke masa” inji mamaa “Allah ya isa tsakanina da ku, amma kusani koda kun kaishi kotu zamu daukaka kara” “Indai akan gaskiyar mu muke, ba matsala ku daukaka...” “Allah ya fiku! Aniyar ku ta koma maku” “Don Allah maama ya isa haka mu tafi gida haka nan” Zuwaira tace tana jawo hannunta, amma ina sai masifa da bala’a take zubawa kamar ba gobe. Da kyar suka fitar da ita daga gidan tana surutai suka tura ta mota.

“Da kun barni na nuna mata ni ba kanwar lasa bace” “Haba maama gaskiya bai kamata ba kin zubar da mutuncinki kawai da kika zo nan” zuwaira wacce ke tuqi tace, ko amsata maama batayi ba tana cigaba da kukanta “Wallahi kuwa da kin barsu kawai sai a kotun idan anje ayita da wajewa” cewar Shukrah  “Nifa banga dalilin da yasa zasuyi masa sharri ba, da kun bi a hankali zamu gano gaskiya” cewar Asma’u  “Don Allah rufe mana baki, rayuwar yayanki fa ake magana a nan! So kike a kashe shi ne?” Maama tace tana latsa waya “Hello Barrister! Don Allah kazo gida... a’a eh akwai wata yar matsala ne... yawwa nagode sosai... sai kazo” Kara latsa waya tayi  “Haidar... yaushe zaka dawo daga Taraba din?... toh har sai jibi? Kayi kokari ka dawo da wuri ina son ganinka... kabi a hankali ka daina yawan fita... nidai na fada maka kawai ka bi a hankali.... yawwa... sai anjima”  Suna isa gida ta dinga safa da marwa a parlonta. “Maama don Allah ki kwantar da hankalinki” daga mata hannu maama tayi “Ki barni kawai Shukrah ni kadai nasan me nakeji” Agogo ta kalla “Wai Barrister din bai zuwa ne?” “Yana hanya nasan” Tana gama rufe baki ta jiyo sallamarsa, da sauri ta kalli Shukrah  “Inaji gashi nan jeki shigo dashi” “Toh maama”  Sallama maama tayi masa ya amsa yana sipping juice din da aka kawo masa. “Wa’alaikissalam” Nan suka gaisa yace “Hajiya lafiya dai ko?” “Ina fa lafiya Barrister!” “Meyafaru?” Yace yana aje cup din hannunsa yana kallonta sosai Nan ta irga masa komai tana gamawa yace “Toh! Babbar magana shi Haidar din ne ake tuhumarsa da wadannan uban laifuka?” “Kaima dai ka gani Barrister, I want you to find the best lawyer koma a ina yake, I assure you ko nawa yake bukata zan bashi” “Wannan ba matsala bace, akwai wani lawyer danasani he’s good sosai, he never lost in any case, zan nemo sa” “Yawwa Barrister Please kayi kokari” “A’a kar ki damu Hajiya, I will try my best, just make sure akan gaskiyarku kuke!” “InshaAllah Barrister” “I think zan tafi yanzu, nasan zaku saurari sammaci soon, mu kuma we’re ready for them!” “Yawwa Alhamdulillah Barrister nagode sosai” “Kar ki damu Hajiya, zamuyi kokari sosai akansa” “Ina zuwa” Tashi tayi ta shiga ciki, ba’a jima kwarai ba ta dawo ta miko masa blank cheque. “Ka rubuta adadin nawa kake so a jiki, wannan somin ta6i ne, idan komai ya tafi yadda nakeso, akwai kyauta ta musamman” Washe baki yayi cike da jin dadi “Ahh Hajiya! Kai nagode kwarai Allah yasaka  da alkhairi” “Kar ka damu kai dai ka tabbatar aikinka yayi kyau” “Insha Allah Hajiya, kar ki damu” Har waje ta raka shi bayan ya tafi ta dawo cikin gida, tana ayyana yadda zasuyi nasara a case din.              



God I less y’ll! πŸ’• Alhamdulillah ala kulli halin.

No comments: