πFawzan ko Adeel?π
Written by MSB✍π»
Story by Maryam Sb (MSB) ππ
ππ
Page 15-16
_Dedicated to Asma’u Isa (Athmeen) thank you for the support really appreciate_π
Sai da ta dauki tsawon awa biyar tana ta bacci, lokacin data tashi da ciwon kai ta farka, hannunta ta dora saman goshinta tana addu’ar samun saukin ciwon kan da takeji, idanunta ta bude Hilwa da Amal ta gani zaune kusa da ita.
“Sannu ya Samha” cewar Amal
Kallonsu kawai takeyi ba tare data ce komai ba, kamar ta tuna wani abu kuma sai ta mike zaune a zabure, kafadunta Hilwa ta dafa
“Am sorry Samha but he’s gone”
Kallonta Samha take tana son gaskata zancenta.
“Daman ba mafarki nake ba? Ba Gaskiya bane... kuce mun yana raye...”
“Haba don Allah Samha! Sai kace ba musulma ba? Ina iliminki ya tafi? Kin san daidai kinsan tawwakali shi musulmin kwarai da tawwakali aka sanshi, na fada miki ya rasu ya rasu ko ki yarda ko kar ki yarda ya rage naki” Hilwa ta fada a fusace
“Ya Hilwa kiyi mata a hankali...” cewar Amal
Bata tanka ba illa wayar Samha ta dauko ta shiga nemo hotunan Fawzan, wanda suka dauka a randa zai tafi ta shiga nuna mata.
Bin wayar da kallo Samha tayi tana kallon hotunan a yayinda Hilwa ke ta scrolling tana fada mata cewar Fawzan ya tafi bazai dawo ba.
Bedsheet din dake kan gadon ta shiga damkowa da hannuwanta ta runtse idanunta gam gam.
“How?” Tace muryarta na rawa
Ganin Hilwa ta fara nasara yasa ta cigaba da magana
“Plane crash, ya mutu Samha, Fawzan ya tafi har abada bazai dawo ba, kiyi hakuri haka Allah ya kaddara...”
“Da gaske ya rasu? Ya tafi kenan ya rasu? Bazan sake ganinsa ba?” Ta fada wane yarinyar dake koyon magana
Amal ce ta rungume ta tana kuka
“Ya tafi ya Samha, dole zakiyi hakuri, ya rasu bazai sake dawowa duniya ba, Fawzan ya tafi... ya tafi har abada...” kasa karasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta tana matukar tausayin yar uwarta.
Suna kallon sadda idanun Samha ke ciccikowa da hawaye, nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tana nuna kirjinta.
“Zuciyata zata buga ya Hilwa, ku taimaka mun, ina ma mutuwar nayi nima kila dana samu sauki” tace cikin rawar murya
Kafin ta ankara hawaye sun fara zubo mata.
Tashi tayi daga gadon tana kallon Hilwa.
“Fawzan ya tafi kenan? Ya rasu?” Ta fada tana tambayan Hilwa, Amal kasa daurewa tayi ta fice daga dakin tana kuka.
Girgiza kanta Hilwa ta shiga yi alamun eh sannan ta shiga girgiza ta da dan karfi
“Ya rasu, nace maki ya rasu, ya tafi kiyi kuka Samha, Please cry na roke ki kiyi kuka...” ta fada tana gunjin kuka tana cigaba da girgiza ta.
“Innalillahi wa inna ilahir rajiun” tayi ta nanatawa a take ta kurma ihu tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, ganin haka yasa Hilwa yin hamdala gami da fita daga dakin da sauri.
Nan Samha ta zube kasa ta dinga kuka kamar ranta zai fita sai surutai takeyi, su mom ne suka tsaya bakin kofa suna kallonta cike da tausayi ba halin su rarrashe ta don kukan ake bukatar tayi daman.
Tafi minti talatin tana kukan nan, kafin a hankali ya fara ragewa, kwanciya kasa tayi hawayen na zuba tana ajiyar zuciya, mom ce ta isa inda take tana ganin mom tayi saurin rungumo ta, wani kukan ne yaci karfinta, sai da tayi mai isarta sannan dad yace.
“Ce Innalillahi wa inna ilahir rajiun” take tayita fadi, cikin ikon Allah ta rage radadin da takeji ta dan samu nutsuwa.
“Hada mata ruwan wanka kisa ruwan da zafi sosai” cewar mom tana rike da Samha.
Amal ta shiga tayi yanda mom tace kafin ta fito ta umurce Hilwa da ta damo custard sanin Samha nason custard idan akayi sa’a tasha.
Bayan Amal ta hada ruwan ne ta jata toilet tana tangadi kamar zata fadi, suna isa mom ta taimaka mata ta cire kayan jikinta bayan tayi brush, nan ta fita ta barta ta jawo mata kofa.
Tafi minti talatin ciki kafin ta fito mom ta taimaka mata don bata iya tafiya da kyau, mai Hilwa ta miko mata ta shafa sannan aka bata wata doguwar riga ta material marar nauyi, bayan ta kimtsa mom ta miko mata custard din.
“Sha”
Girgiza kanta ta shiga yi alamun a’a
Tsawa mom ta daka mata, ba shiri ta kar6a ta fara a hankali, rabi tasha tace ta koshi mom ta kar6a ta rufe.
“Please I want to be alone for some time” tace cikin rinanniyar murya
“Amma kuma...” cewar Amal
“Let her be Please” mom tace tana tashi da niyyar fita, Hilwa tabi bayanta sannan Amal ma ta fita.
Tunawa batayi sallolinta ba yasa tayi saurin tashi tayi alwalla ta fara ramawa, tana zaune bisa sallaya bayan tayi sallar isha’i ta dan dora kanta jikin gado, idonta rufe yake amma kana ganin gangarowar hawayenta, kuka ne ya kwace mata nan kuma ta shiga rera kuka.
“Fawzan....Fawzan... you are my everything, my first and last love, and you are gone...”
Ta fada hawaye na cigaba da kwarara wane ruwan sama mai karfi, tabbas da ciwo ita kanta tasan me take ji yanzu, ji take kamar kirjinta zai rabe biyu.
“Daman haka rabuwa da masoyi take da ake ta fadi? Ashe haka ake ji?” Ta fada tare da kara fashewa da wani kukan.
Kanta ta dora bisa gwiwoyinta tana cigaba da kukan.
“Ina ma ace mafarki nakeyi zan farka yanzu?”
Nan ta cigaba da kukanta ba tare da ta sassauta ba.
_*_*_*_*_*_*_*_
One month later (Bayan wata daya)
Da alama Samha tayi nisa a cikin tunaninta, zaune take tayi facing window din dakinsu tana ta kallon sauran ruwan saman da akayi yana dripping kadan kadan. Iska ne ya kada mata a fuska take tayi folding hannayenta sanyin na ratsa ko wace ga6a ta jikinta. A hankali dankwalinta ya zame daga kanta take bakin dogon gashinta ya bayyana.
Tun bayan rasuwan Fawzan nan take rayuwa, ta daina shiga cikin mutane, magana baifi tayi daya ko biyu ba, in ta
Kama ma girgiza kai kawai takeyi. Mom tayi fadan amma ina. Nan take zama tayita tunani, in ta tuna Fawzan kuwa ta dinga kuka kenan kamar an aiko ta.
Tabbas mutuwan Fawzan ya bar mata wani tabo a zuciyarta wanda bata tunanin warakarshi na kusa.
Kwankwasa kofar dakin akayi, nan ta farga ta dawo daga duniyar tunanin data lula, bata motsa ba haka ma bata ce komai ba.
A hankali ta shigo, ajiyar zuciya tayi daman tasan nan zata iske ta, hannunta ta dora bisa kafadun Samha.
“Yawan tunani zai ja miki wani ciwon ya Samha”
Shiru tayi na dan lokaci kafin tace cikin muryarta mai sanyi kamar wadda aka tilasta ma yin magana.
“Wallahi Amal nayi iya kokari na ganin na daina amma na kasa”
Amal ta girgiza kanta cikin fahimta sannan ta zauna kusa da ita.
“Haka ne but try harder, Allah ya sassauta miki ya Samha”
Juyowa tayi ta kalle ta gami da yin dan karamin murmushin da bai kai zuci ba
“Amin” tace idanunta na kokarin kawo ruwa.
Da sauri Amal ta dan murza hannuwanta alamun kar tayi kuka.
“Haka ake ji idan ka rasa wani na kusa dakai, hakurin nan dai shi zakiyi, Allah yana tare da masu hakuri”
Ajiyar zuciya Samha tayi
“Kinsan me?” Tace tana kallon window din dakin
“A’a sai kin fada”
“Nasan Allah yanada dalilin dauke Fawzan, maybe we are never meant to be together”
“Hakane, kuma kinsan life goes on dai ko? Ki manta da komai ki dawo yadda kike da, I want my annoying sister back, I don’t like this one, soon zaki shiga University, I want you to change please”
“I need some more time, nasan with time komai zai zama normal”
“That’s my sisi, don Allah ki tashi muje shopping sai mu biya mu dauki Yasmin” tace tana kokarin dragging dinta daga gadon
Girgiza kanta ta shiga yi tana kokarin kwace hannun
“No! Kuje kawai bazan je ba”
“Please ya Samha, it’s been a while da muka fita Please, you need some fresh air, na tabbatar zaki samu sassauci”
Shiru tayi kamar tana tunani
Hade hannuwanta Amal tayi wuri daya alamun roko
“Please, Please, please, Please, Please.....”
“Ok naji!”
Tashi tayi ta daka tsalle
“Yeey! Tashi ki shirya mu tafi, yau su mom zasuyi farin ciki zaki fita”
A kasalance ta tashi ta zura bakar abaya, sai ta yi rapping gyalenta, turare ta feshe jikinta dashi sannan ta saka takalmanta tare da dauko hand bag dinta, Amal ce ta shigo
“Am so happy today wallahi, gashi dad ya bamu kudi mu siyo abinda muke so”
Dan karamin murmushi kawai tayi tare da ficewa daga dakin. Da sauri Amal ta shirya ta fito itama.
Tunda suka shigo wurin yake kallonta, ko wane motsinta akan idonsa, bayan sun gama shopping ne suka tattara suka fita.
Sauri Haidar yakeyi ya biya kudaden don kar su tafi, amma ina yana fitowa motarsu na barin layin, dafe kansa yayi yace
“Who is she?”
Yace yana bin motar da kallo....
π€
No comments:
Post a Comment