πFawzan ko Adeel?π
Written MSB✍π»
Story by maryam S bello (MSB) π π
ππ
Page 08
Tunda Fawzan ya sanar mata da batun tafiyarsa hankalinta ya kasa kwanciya wadda ta rasa dalilin haka, duk yadda taso daina damuwa abin ya gagara, har mom ta gano hakan kwata kwata ta daina walwala yanzu ta koma shiru shiru, ba abinda takeyi sai zaman daki tayi kwance ta kura ma wuri daya ido, ko kuma kawai taji gabanta ya tsananta bugu.
Ko waya Fawzan ya kira ta har ya gano akwai abinda ke damunta duk kuwa yadda taso dannewa.
“Princess? Kina jina?”
“Me kace?”
“Yanzu duk zubar da nake bakiji ba?”
“So...r....”
“Wai meke damunki haka?”
“Babu”
“Ban yarda ba”
“Da gaske...”
“Meyasa kika chanza toh? Ai da ba haka kike ba”
“Na chanza me? Ya nake da?”
“Hmm, kin san me nake nufi”
“A’a”
“Toh bye”
“No wait...!”
“Then tell me, what’s bothering you”
“Nifa bansani ba, kawai haka na tsinci kaina”
“Ki yawaita addu’a kinji? Kuma ki cire ko meke cikin ranki kar wani ciwo yaje ya kama mun ke fa”
“InshaAllah”
“So me kikeyi yanzu?”
“Babu”
“Ba islamiyya ne yau?”
“Sai anjima”
“Baki shiga kitchen?”
“Har mun gama”
“Wow! Me kika girka mana?”
“Jollof”
“Toh zanci”
“Ba matsala”
Nan yayita janta da hira har ta saki jikinta, dadi sosai yaji.
Kullum haka yake kiranta yayita sata dariya, har ya samu ta dan chanza tana hira sosai kamar da.
Duk sadda zaizo wurinta sai ya tabbatar ya kawo mata abinda tafi so, ko don taji dadi, idan ya zo ma ya lura sai tayi ta kallonsa yarinyar dako hada ido da da kyar takeyi dashi.
Sai ya kira sunanta sannan tayi saurin sunkuyar da kanta kasa.
Haka zasuyita hira da kyar yake tafiya gida.
A waya ma haka suke wuni suna makale, duk dai don kar ta shiga damuwa kokarin faranta mata rai yakeyi.
Ranar da zai tafi flight din na karfe 1 ne amma tun 9 yake gidansu, tsaraba ya kawo mata da yawa, amma koda yazo sai yaga damuwar da take ciki yau tafi ta kullum, hankalinsa duk ya tashi, ji yake kodai ya fasa tafiyar ne?
Kallonsa takeyi take hawaye ya cicciko mata da sauri ta kawar da fuskarta gefe tana sharar kwalla.
“Haba princess, so kike na fasa tafiyar ne? Just say it wallahi bazan tafi ba”
“Banfa ce ba”
“Toh menene?”
“Ni fa kawai kaina ke ciwo”
“Bawani, zo kigani”
Ta taso, mikewa yayi ya dauki wayarta ya dinga masu selfie, wani ta daure fuska wani yayi forcing dinta tayi dariyar da bai kai ciki ba.
Karfe 11 ya mike da niyyar tafiya, ta raka shi wurin mota duk yadda taso daurewa ta kasa ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, sannan ta fada jikinsa duk da tasan bai kamata ba amma she can’t resist, mutuwar tsaye yayi inda hawaye ya gangaro masa ba shiri, gogewa ya shiga shirin yi amma ina ashe shima kukan yake.
Sun dauki tsawon minti goma a haka bamai rarrashin wani, shine ya fara dakewa sannan yasa hannu ya janyeta daga jikinsa, tissue ya bude motarsa ya dauko ya shiga share mata hawaye, da kyar ya samu kukanta ya rage.
“Wai princess da kike kuka sai kace wanda idan na tafi bazan dawo ba?”
“Ni ji nake kamar kar ka tafi, zuciyata ta kasa samun nutsuwa” ta fada tana share hawaye
“Haba princess dina, baby na, my heartbeat, my world, my soulmate my life, my everything don Allah ki bar kuka, addu’arki kawai nake bukata”
Murmushin jin dadi tayi tana share hawaye
“Kamo ta nan, kamo ta nan...” ya fada yana yi mata wasa wane yarinyar goye
Batasan sadda ta kyalkyale da dariya ba shima yana tayata.
“My cry cry baby, zo ki hau na goya ki kafin na wuce”
Turo baki tayi cike da shagwaba
“Uhm uhm sai kace wata baby”
Yayi dariya
“Toh mecece? Yanzu fa kika gama kuka..” ya fada yana tsare ta da idanu.
Ta turo baki
“Indai hakane kaima baby ne, ina kallonka kana kukan kaima”
Dariya yayi ganin yadda take masa magana cike da shagwaba, sannan ya zaro idanu cikin wasa
“Kuka kuma? Nikuma yaushe nayi kuka?”
Harara ta watsa masa tare da sauke kanta kasa.
“La ka manta bakayi sallama da su mom ba”
Sosa kansa yayi
“Ta ya zan tuna bayan kin tayar mun da hankali?”
Murmushi tayi cike da kunya sannan ta juya ta soma tafiya cikin gida, kallonta yake cike da so sannan kuma yabi bayanta yana murmushi.
Bayan ya shiga parlor ita kuma ta wuce sama dakin mom dinsu.
Sallama tayi ta shiga, mom na saka kaya da alama wanka ta fito ta amsa sallamarta.
Kusa da ita taje sannan tace
“Mom”
“Na’am”
“Mom ga Fawzan zai maku sallama”
Mom ta kalle ta tace
“Me kuma ya samu idanunki haka jawur?”
“Babu abu ya fada mun a ido” ta mata karya
“Samha kenan, ina Fawzan din har tafiyar ta tashi kenan?”
“Wallahi kuwa”
“Toh muje” ta fada tana saka hijabinta.
A parlor suka shiga yana zaune kasan carpet, mom suka shiga da sallama.
Bayan mom ta zauna ya soma gaishe ta cikin ladabi da kunya.
“Har tafiyar tazo Fawzan?”
“Eh wallahi yanzu ma zan wuce”
“Allah sarki, Allah ubangiji ya tsare hanya, Allah ya kare, Allah yasa alkhairi ya bada sa’a, Allah kuma yayi maka albarka”
Cikin jin dadi yace
“Amin ya Rabbi”
Tashi mom tayi tana mai cigaba da masa addu’a sannan ta fice.
Kallon agogonsa yayi ya zaro ido
12:15
“Kai! Bari na tashi”
Jiki ba kwari duk suka tashi suka soma takawa waje.
“Idan kika sake yi mun kuka, komawa gida zanyi na harhada kayana na tafi bazan sake dawowa ba”
Ta zaro ido
“Nasan wasa kake”
“Allah da gaske”
“Am sorry please”
“It’s ok just promise me bazakiyi ba”
“InshaAllah”
Har mota ta rakasa ya shiga
Dad’ad’en kalame ya shiga furta mata, kamar kar su rabu
“Toh princess sai Allah yayi mana dawowa”
Ya fada yana kokarin tada mota.
Idanunta suka kawo ruwa.
“Aw kin manta me nace?”
Da sauri ta goge tana murmushi, murmushin yayi shima
“That’s my strong princess”
Tayi murmushi.
Waving ya soma yi mata yana fadin
“I love you, take care of yourself for me”
Itama ta mayar masa tana murmushi
“InshaAllah and you do thesame”
Yayi murmushi sannan ya juya kan motar, suka cigaba da waving ma juna har ya bace daga layin, ajiyar zuciya tayi tana masa addu’a Allah ya tsare mata shi.
Hanyar airport yayi, he left with a heavy heart, missing din Samha yakeyi amma dole ya daure, yasan idan ya mallake ta ko ina da ita zai rinka tafiya.
Shigewa tayi dakinta tana tunani gabanta kawai ke faduwa, nan tayi ta addu’a har ta samu sassauci.
Kiran mom ne ya katse mata tunani
“Samha! Kizo ku nema abinda za’a girka da rana ni fita zanyi”
“Toh mom!”
Wardrobe dinta ta bude ta dauko wata doguwar riga ta material don kayan jikinta sun ishe ta kuma, sakawa tayi tare da daukan hula kalar kayan ta sauko kasa.
Kitchen ta nufa, aikin ta soma amma hankalinta naga Fawzan.
“Allah ya kaika lafiya Fawzan” tace a hankali zata fara blending kayan miya.
Grab your popcorn because we are going on a rollercoaster ride!
No comments:
Post a Comment