πFawzan ko Adeel?π
Written by MSB✍π»
Story by Maryam Sb (MSB) ππ
ππ
Page 59-60
Sai yanma lis Gwaggo ta dawo a gajiye, ganin Samha tayi zaune tsakar gida kan tabarma. Zama tayi gefenta tana murmushi “Khadija kai kadai?” “Gwaggo sannu da dawowa ina wuni?” “Lafiya lau Khadija yaya jikin? Nace kai kadai ina Shatu ko Barkindo?” Tayi murmushi “Shatu na ciki Fawzan kuma ya fita” “Wai har yanxu bazaki daina kiransa da wannan suna ba” Ta sake murmusawa “Gwaggo kenan, ni nasan dalilin da yasa nake kiransa haka” “An fada maka bashi bane ay” Murmushi kurum tayi don bata son jayayya da Gwaggo. Gwaggo ta shiga bude wata madaidaiciyar leda “Kaga yan kaya na siyo maka na kai maki dinki naga bakada kaya” Tayi murmushin jin dadi “Laa Gwaggo harda wahala haka? Nagode sosai Allah ya saka maku da mafificin alkhairi, yadda kuke dawainiya dani Allah ya biya ku da gidan aljanna” Cikin jin dadin addu’ar Gwaggo tace “Ameen Khadija, bari na kai maki su dakinki ko, bari na dawo sai na taimaka maki kiyi wanka sai ki chanza kaya” Cikin murmushi tace “Toh Gwaggo na gode” Janta daki Gwaggo tayi ta taimaka mata ta cire kayan jikinta ta bata zanin wanka ta daura ta saka mata hijabi, har cikin kewaye ta kaita tare da ruwan wanka, ta damka mata soso da sabuli a hannunta. “In kin gama ki buga kyauren” Ta gyada kai, Gwaggo ta fita ta rufe mata kofar, bayan kusan minti talatin ta buga kofar Gwaggo tayi saurin bude ta. Ruwan alwalla Gwaggo ta zuba mata a buta tayi. Gwaggo ta taimaka mata ta kimtsa cikin yar atamfa green and yellow color dinkin riga da zani da dankwalin, kuma ta danyi kyau ba laifi. Hijabinta ta saka sannan ta tada sallar isha’i don Shatu taki taimaka mata da ruwan alwalla. Tana gamawa ta jiyo sallamar Adeel, tana ji suna magana da Gwaggo kafin ya shigo dakinta da sallama, sai da ta shafa addu’a ta amsa sallamar da murmushinta mai kyau. “Khadija kin gama sallar?” “Eh na gama” “Toh kin shirya?” Cikin rashin fahimta tace “Ina zamuje?” Yayi murmushi “Har kin manta nace zan rakaki ki zaga gari?” “Oh hakane, eh na shirya” Jagora yayi mata suka fito daga dakin. “Gwaggo zan kaita ta ga gari” “In banda abinka ay ba gani zatayi ba” “Eh duk da haka Gwaggo kinsan zama wuri daya bashida dadi” “Gaskiya ne, a dawo lafiya” “Allah yasa” Daga haka suka fice, Shatu tayi saurin fitowa daga dakin tana ta 6ata rai “Ina kuma zasuje Gwaggo?” “Ganin gari” “Ganin gari da makauniyar?” “Makauniya kuma? Ay ba makauniya bace idonta ne yaji rauni shine aka rufe mata shi sai ciwon ya warke” “Ay bata gani” “A’a da an bude zata fara gani kamar kowa” Ta zum6uro baki “Toh zanje gidansu Jummala” “Bazaki ba, bakida aiki sai yawo” “Haba Gwaggo ya za’ayi ki bar makauniya ta fita sai ni da idanu na ki hana ni fita?” Gwaggo batasan sadda ta mangare mata baki ba “Banace kar ka sake kiranshi makauniya ba?” “Yanzu Gwaggo akan wannan bakuwar zaka dakeni?” “Eh mana ka iya bakinka” Tashi tayi ta wani shige daki a dole tayi fushi, tanajin Gwaggo nata mita akanta. Tafiya suke a hankali suna hira jefi jefi. “Amma daga ji garinnan nada kyau” “Sosai ma” “Mutanen masu kirki kuma, naji kuna ta gaisawa dasu suna mani sannu” yayi dariya “Hakane kuma suna da dadin zama, amma sunada ban haushi wani lokaci ba” Tayi murmushi, ya kalleta she looks happy, lallai zama wuri daya baiyi ba. “Akwai rafi kusa?” “Kina son zuwa wurin?” “Eh wallahi” Tafiya suka cigaba da yi har suka iso rafin kusan minti goma sannan suka isa Karar ruwan taji da wani iska mai dadi suka kada ta. “Wow, daga ji wurin nada kyau sosai” “Kwarai kuwa yanada kyau, nan nake yawan zuwa na zauna idan banida abinyi” “Wane aiki kakeyi?” “Gona mana, amma muna zuwa farauta da Baffa duk ranar asabar da lahadi” “Da kyau” tace cikin murmushi shiko kallon dan bakinta yakeyi da alama dai bakin Samha na birgeshi. Dan karkashin wata bishiya ta iccen mangoro suka zauna suna cigaba da hira. “Wai da gaske bakai bane Fawzan?” “Baki yarda ba har yanxu ko?” “Hmmm, gaskiya abin da kamar wuya, sai idan naga fuskarka zan yarda bakai bane” “Aiko idan kika gani zaki kara yarda da kyau” “Idan naga fuskarka zan kara yarda kaine” Yayi dariya “Khadija kenan bakida dama” “Ay gaskiya ce” “Uhm” Tashi yayi ya fara katsar mango “Me kakeyi?” “Mangoro nake katsar maki” Tayi yar dariya “Ko Bazaki sha ba?” “Zan sha idan zaka sha” “Angama” Gama katsa yayi yaje ya wanko ya miko mata. Suna sha suna hira sama sama. Sai wurin shidda ta wuce suka tashi suka fara tafiya zasu koma gida. Sai da sukayi nisa sosai Shatu da Jummala suka fito inda suka 6uya. Rike baki Jummala tayi “Ay na fada maki da matsala tun farko” “Na shiga uku na lalace zata kwace man Barkindo na” ta fada tare da dora hannu bisa kai sai kace wacce aka yi ma albishir da gidan wuta
“Kwantar da hankalinki maganinta zamuyi, gargadi zamuyi mata ta rabu dashi tun wuri” “Eh kin kawo shawara” “Mu tsorata kawai shine magana” “Yawwa yar gari shine bayani, da nice wata take makale ma Hamma wallahi ubanta zanci bazan yarda ba” “Ah toh ay nima bazan yarda ba” Tafiya suke suna shawara yadda zasu 6ullo ma lamarin, daga karshe suka yanke shawarar yadda zasuyi mata. Washe gari kowa ya fita aiki, Gwaggo ma ta tafi saro nono inda Shatu da Samha kadai ke gidan, fitowa Shatu tayi waje taga Manu da Jummala kofar gida (Manu irin yan iskan samarin kauyen nan ne wadanda sukayi kaurin suna sun gagari kowa a garin, mata da yawa tsoronsu sukeyi saboda iskancinsu) “Yawwa Manu kasan me zakayi ko?” “Nasani amma dakata, nawa zaki bada?” Tayi dariyar mugunta “Haba Manu nice fa Shatu, kaima kasan zan bada abu mai tsoka” “A’a kar sai daga baya ki kawo mun wasa wallahi koya maki hankali zanyi” “Kaga Manu zata baka wallahi ko zuwa gobe” Jummala tace tana kallon Shatu “Kin tabbata kin fasan banida kyau, banida mutunci wallahi” “Eh wallahi zan baka dubu 2 tayi?” “Idan na kar6i dubu 2 Allah tsinan albarka” “Haba Manu wallahi banida su wannan ma Baffa zan ma wayau ince daga makaranta akace mu kawo” “Na fada maki a’a ki bada dubu 3,500 kawai” A tsorace suka dago suna kallon Manu “Haba Manu, toh zan fara baka dubu 2 gobe sai na ida cika maka sauran daga baya” Sai da ya yamutsa bakin bakinsa sannan ya zuqi taba ya fesa mata a fuska, kauda fuskarta tayi tare da toshe hanci. “Toh kayi sauri kar su Gwaggo su dawo, bari mu jira ka nan” Shiga cikin gidan yayi yaja ya tsaya bakin kofa, hango ta yayi kwance kan tabarma tana karatun qur’ani cikin zazzaqar muryarta mai dadin sauraro, sai kace karantowa takeyi. Takowa ya fara yi cikin gidan a hankali, jin motsin tafiya yasa ta tashi zaune a tsorace “W....waye nan!?” Shirun da taji sai karar tafiya yasa ta kara tsorata tana kokarin tashi tsaye. “Wai waye don Allah?” Ta fada tana kalle kalle kamar mai gani. Cikin muryar yan daba yace “Bawan Allah ne! Wurinki nazo” Hadiye miyau tayi da karfi ta fara tafiya tana bin bango. Binta ya shiga yi tana tafiya a tsorace ba tare da tasan ina ne hanyar ba. “Ki tsaya ba cutar da ke zanyi ba gargadi kawai zan maki” “Gar...gadin me?” Daf da ita yazo tayi saurin matasawa tare da fasa ihu, guduwa tayi tana laluben hanya da sauri. “Gargadin xan maki akan ki rabu da Barkindo, ba naki bane, in ba haka na lahira sai ya fiki jin dadi” “Aw wai sheyasa kazo nan? Ay ni mai rabani da Fawzan sai Allah” “Kikace me? Waye haka!?” “Shi wanda kake nufi mana” Jin alamar yana tahowa yasa ta ruga tare a fasa ihu, bata ankara ba taji tayi karo da abu tim! Kara fasa ihu tayi a gigice “Khadija?” Jin muryarshi yasa ta saki ajiyar zuciya tana nuna wuri da hannunta “Menene?” “W...ani ne ya shigo nan gidan” Ganin Manu tsaye bakin kofar fita yasa Adeel yace “Mekika shigo yi nan gidan?” “Aiko ni akayi” “Waya aiko ka?” “Shatu mana, gargadi nazo yi ma wannan” “Akan me wai?” “Akanka!” “Sai aka ce ka shigo gidan mutane kai tsaye saboda bakada hankali ko?” Nuna shi Manu yayi da yatsa “Kar kace zaka gaya mun magana zanyi kasa kasa dakai aradu” Biyo shi yayi Adeel da gudu Manu ya fita yana zuwa ya watsa ma Shatu da mugun kallo “Kudinki sun koma dubu 5, idan baki bani ba zuwa gobe zaki gane kurenki” yana gama fadin haka ya kama hanya yana tafiya yana baza rigarsa da ko botton bai 6alle ba kirjinsa a bude. Finciko ta Adeel yayi ya shigo cikin gidan da ita tana ihu, tuni Jummala ta ruga a guje sai gida. Yana zuwa ya wullata kasa “Meye hadinki da Manu?” Ta fara kakkarwa, ya daka mata tsawa “Ba magana nake dake ba!?” “Ba...bu wallahi” “Karya kike, ki fadi man tun kafin raina ya 6aci” ya fada yana zaro belt dinsa, tuni Shatu ta rikice tana ihu “Don Allah kayi mata hakuri” Samha dake tsaye tana saurare tace Bai kulata ba yayi kan Shatu gadan gadan zai shaud’a mata belt din, rikitaccen ihu tasa “Wayyo Allah! Na tuba yaya na tuba! Kar ka dakeni!” “Toh kiyi magana meya hada ki dashi?” “Da...ma kawai cewa nayi yayi mata magana ta rabu da kai” “Wa?” Tayi shiru tana kakkarwa Zabga mata belt din yayi a jiki tuni ta rude da ihu. “Nace wa?!” “Ita!” Ta nuna saitin Samha “Bakisan halinshi bane da zaki je wurinshi? Ashe bakida hankali! Toh bari kiji in fada maki taqi ta rabu dani din! Yanzu ma muka fara shakuwa da ita” “Kar ka man haka....!” Kara zabga mata belt din yayi da karfin gaske. Ta fasa ihu “Idan na sake ji kinje wurin Manu koda wasa ranki sai yayi mummunan 6aci! Kinji ni?” Tayi shiru ya kara zabga mata belt din, da wuri ta fasa ihu Da sauri tace “eh” “Kayi hakuri Fawzan” tace a tsorace. Kallonta yayi yace “Kiyi hakuri abinda ya faru kinji?” Yana gama fadin haka ya fice daga gidan rai a 6ace. Da sauri Shatu ta mike tsaye ta tako wurin Samha “Yau akanki Barkindo ya nada mun duka, abinda bai ta6a mun ba yau saboda ke anyi mun shi” ta nuna ta da ya yatsa kamar Sanha tana ganinta. “Wallahi wallahi sai na dauki fansar abinda yayi mun a kanki, munafuka kawai” ta dungure mata kai ta wuce fuu ta shige dakinta ta bar Samha tsaye tana mamakin abin.
God bless y’ll! π
No comments:
Post a Comment