πFawzan ko Adeel?π
Written by MSB✍π»
Story by Maryam Sb (MSB) ππ
ππ
Page 51-52
Bayan fitarsa Samha ta rushe wani irin kuka mai ban tausayi, nan ta dinga kuka gashi ba halin ta share hawaye saboda hannu an daddaure, sai data gaji don kanta tayi shiru, take kanta ya fara tsananin ciwo, lumshe ido tayi tana jin zogin kafarta mai ciwo, ba’a juma ba baccin wahala ya dauke ta daga zaune a dauren. Farkawa tayi taga dakin duhu, hasken kadan ne wanda hasken yar window din dakin dake haskowa alamar hasken farin wata ne, don dakin ko fitila daya babu, take ta gane dare ne yayi, nan ta fara tunanin Saudat shin taje police station din ko kuwa bata ma gane wurin ba? Shin ta gane gidansu ta fada masu ko kuwa? Ko sallah batayi ba, ya salam rabonta da sallah tun gida da tayi subh. Kokowa ta shiga yi da kujeran amma ina ta kasa koda motsi saboda irin daurin da aka mata. Hakura tayi ta bari tana maida numfashi kamar wacce tayi gudu, duk tayi baki ta jeme kamar ba Samha yar gayu ba, fuskarta duk tayi duhu, gashin kanta kuwa ya jike ya bushe duk yayi wani iri. Nan tayi zuru tana kare ma dakin kallo wanda ta tabbatar ko karen gidansu baza’a barshi ya kwana nan ba, window daya ce dakin wata yar karama tana tunanin ko kanta bazai wuce ta nan ba. kuma window din tana can sama ga dakin tsawo ne dashi. Ajiyar zuciya ta saki haka ta zauna ga tsoro ya cika ta, ba’a jin motsin komai sai kukan tsuntsaye, da alama cikin daji take. Dakewa tayi tana addu’ar Allah ka kawo mata dauki har 6arawo bacci ya kwashe ta. Farkawa tayi a gigice sakamon jin hannun mutum a fuskarta, bude ido tayi ganin mugun nan ne Haidar ke shafa mata fuska. Kauda fuskart tayi da sauri hade da runtse ido gam gam. “Awwn good morning sunshine, I know you have a very wonderful night right sweetie?” Shiru tayi bata tanka ba, ya kara matso da bakinsa yana neman kissing dinta, ta datse bakinta gam, ya kece da dariya. “Baby I brought you breakfast, I know you must be very hungry baby girl” Kallonsa tayi a wulakance tace “Ko yunwa zata kashe ni bazanci abincinka ba” Ya shafa kanta “Are you sure darling?” Ta harareshi sannan ta kauda fuskarta gefe guda. “Alright alright don’t be angry ok? You need to eat cuz you need the energy for me baby” “Me kake nufi?” Ya kece da dariya “Do you think I will let you go just like that? Ban yi abinda yasa na aure ki ba, do you think am a fool?” Yasa dariya “no baby, I have to do it before you go” “Allah ya tsare ni! Ko zaka kashe ni bazan yarda ka kusance ni ba...” Yakara kecewa da wata irin dariya “See who’s talking now! Let me see how you are ever gonna stop me from archiving my...” “You will you not dare touch me Aliyu Haidar! I won’t let you!” “Really?” Yace yana janye mata gashinta da ya rufe mata goshi da ido, ta fizge fuskarta, ya damqo mata gashi, ya shiga shafa mata baki da yatsansa, bai ankare ba ta gartsa masa cizo a hannu, da sauri ya janye hannu yana yarfa shi a iska. “What the hell!” Ya shako mata wuya, ta fara kakarin amai, sai dai yaga tana neman siqewa ya saketa da karfi, ta dinga maida numfashi, dariya tasa “Aliyu Haidar am not scared of death, you can go ahead and kill me you’re free” “I won’t kill you just yet, until am done with you” “And that can never happen” “Then let’s see” ya fada yana mikewa zai fita “Aliyu Haidar!” Ya wani juyo gami da harde hannayensa wuri daya “Yes darling na dawo ne? Halan you need me” “No God forbid! I need to pray!” “What?” “You heard me right, nace sallah zanyi” “Toh kiyi mana waya hanaki?” “Kaji tsoron Allah a haka zanyi sallar? Ba alwalla ba komai? Anya Haidar Allah bazai kama ka ba kuwa? Sallah tana gaba da komai...” Daga mata hannu yayi “Da Allah dakata a nan malama, kinfini sani ne? Shut that your dirty mouth! So kike ki sake guduwa ko? Not again young lady. I won’t let you go anywhere again” Murmushin takaici tayi “Allah ya isa” Ya kece da dariya “Dabai isa ba yayi ki ne? I will be right back!” Daga haka ya fita tare da rufe kofar da key. ******
“Mom wai nikam lafiyan Samha kuwa? Aure kusan wata hudu amma bata ta6a zuwa gida ba? Kuma ya za’ayi ko munje bama samunta a gida? Ni ina ji a jikina something is not right” “Bake kadai ba Amal, ni jiya har mafarki nayi mijinta na ta binta da wuka yazo caka mata kenan na farka” “Toh bakiga ta fita da gudu ba tana kuka ba? Daga ranan bata sake dawowa ba” “Amal ko dai ki tashi mu tafi gidan nata mu shiga muga ko lafiya” “Gaskiya mom, hankalina zaifi kwanciya” “Tashi mu...” Shigowar mai gadi ce ta katse masu hirar tasu. Muskutawa yayi “Hajiya barka da safiya” “Yawwa Balarabe barka dai” “Hajiya kinada bakuwa waje” “Ikon Allah wacece haka da sassafe?” “Toh bandai santa ba yarinya ce tace da Allah tana sallama da Hajiyar gidan” “Allah sarki kace ta shigo mana” “Toh Hajiya” daga haka ya tashi ya fice Sallama Saudat tayi daga bakin kofa, amsa sallamar tayi mom sannan tace “Bismillah bakuwa shigo mana” Da ladabi ta gaida mom, bayan ta amsa da fara’a tace “Sai dai ban waye ke ba baiwar Allah” Saudat tayi murmushi “Eh hakane kam baki sanni ba, da farko dai sunana Saudat Isma’il, kuma ni kishiyar Samha ce uwar gidanta” A razane mom da amal suka mike tsaye “Kishiya kuma? Ay baiwar Allah Samha bata da kishiya” Saudat tayi murmushin takaici “Don Allah ku zauna hajiya, yanzun ma Samha ce ta aiko ni nan” Da kyar suka zauna mom tace “Ina jinki” “Kamar yadda nace nice kishiyar Samha to tabbas haka maganar take, ita kanta Samha batasan dani ba sai data shiga gidan tasan dani, wallahi Hajiya zanyi takaicin sanar daku cewa Haidar ba mijin aure bane, saboda tunda Samha ta shigo gidannan take fuskantar kalu bale, Samha tasha wahala har kusan kasheta yakeyi, Samha bata isa ta fita ko nan da kofar gida ba, saboda masu tsaro, wato dai gana mata azaba kawai yakeyi, nima sadda ya aure ni haka yayi mani, in takaice maku zance Haidar ya auri mata sama da ashirin, ko wace ya gama da rayuwarta sai ya rabu da ita, mutumin bashida imani ko kadan, Haidar yana da wani sirri da Samha ta gano wanda ya razana ta, yanada cutar HIV, dan fashi da makami ne, yana kuma amfani da bangaren jikin yan mata yana tsafi dashi, wanda mukayi bincike muka gano” Mom kuka Amal kuka “Innalillahi wa inna ilahir rajiun! Haidar din da nasani wai, mutumin kirkin nan dai? Yanzu kina nufin ya shafa ma yata kanjamau?” “Shi fa, amma fa ba mutumin kirki bane, don bayada imani ko digo a zuciyarsa, a’a bai shafa mata ba” “Toh yanzu ina ya Samha din?” Cewar Amal “A ranar da muka masa bincike shine muka samu muka gudo, muna tsakar gudun ne takalmin Samha ya katse wanda ta sanadin haka ta taka kwalba, shine ta bani evidence din na kai police station ta kuma bani address dinta, naje police station din I file a complaint, sai muka koma da police din inda na baro ta amma babu alamunta, shine muka tafi can gidansa shima wayam shine aka kama guards dinsa guda 6, suna hannun hukuma anyi anyi su fadi ina yake sunce basu sani ba, shine na taho nan tare da yan sanda guda biyu” Tashi mom da Amal sukayi da sauri suna salati suna kuka. “Ina police din?” “Suna waje” Fita sukayi inda suka tarar dasu waje tsaye. Suna ganin su mom suka taho inda suke “Am inspector Okoye” ya nuna ID card dinsa. “Inspector ya ake ciki toh yanzu?” “I assure you ma’am we’ll do absolute everything in our power to find your daughter, she will be back safe and sound” Dayan inspector din ya nuna nasa ID card din “Inspector Yunus Jamil, Hajiya kar ku damu zamu nemo maku diyarku, all we need is her picture, what she’s wearing, her description dai, shi kuma we make sure hukuma ta hukuntasa daidai laifinsa” “Mungode sosai, bari na kawo hotonta, Saudat sai ki fada masa kayan da tasa” “Wata red and cream atamfa ne jikinta dinkin riga da skirt, she’s white in complexion, tana da tsawo average height” tana fadi suna rubutawa bayan sun gama mom ta dawo “Gashi” suka duba suka saka a file “Ma’am ga wannan keko mahaifinta kuyi signing a nan” yace yana mika mata paper din “Well babanta Allah ya mashi rasuwa bari nayi signing” “Allah ya jikanshi, batada yaya?” “Tana dashi yayi aure ne” “Ok ki kirashi sai ki fada masa ya same mu office din mu ga address din” “Insha Allah, please kuyi kokari ku gano mana ita” “Don’t worry ma’am, ga wannan yarinyar please ku rike ta kafin mu kammala case dinnan, sai mu taimaka mata ta koma garinsu” “Ba damuwa Amal kaita ciki” “Toh mom” “Toh inspector mun gode sosai, try your best” “We’ll” daga haka suka fita.
God bless y’ll ❤️
No comments:
Post a Comment