πFawzan ko Adeel?π
Written by MSB✍π»
Story by Maryam Sb (MSB) ππ
ππ
REMINDER Don't forget to fast on the Day of Arafah. It expiates the sins of the previous year and of the coming year. (sahih Muslim)
Page 67-68 Gaba daya su mom na kofar gida tunda inspector ya sanar da su anga Samha ya shaida masu suna hanya ma. Dadi kashe su tuni an tashi an fara gyara gida, gyara na mussaman aka ma dakin Samha aka kunna ma gidan turaren wuta, gaba daya favorite abincinta aka girka da snacks da drinks din da tafi so. Har sun soma gajiya da jiransu, and sun gaji da tsayuwa ma nan har yan unguwa sun fito kallon ikon Allah. Can motar yan sanda tasha kwana tana jiniya parking tayi kofar gidansu Samha inda inspector din ya fito shida Areef suna murmushin nasara, da gudu mom suka yi kansu suna dube dube jiran ta ina zata fito, Areef ne ya zaga ya bude seat din baya inda ya kamo hannunta suka nufi inda su mom suke, sakin baki mom tayi tana kare ma Samha kallo da idanunta ke rufe, kayan jikinta take bi da kallo cike da al’ajabi baki sake. Hilwa ce da Amal sukayi saurin hugging dinta suna kuka, laluben fuskarsu takeyi tace “Amal? Ya Hilwa?” Sai tasa kuka “Kune? I missed you so so much you have no idea how much I miss you sisters!” “What happened to your eyes?” Hilwa tace tana shafa wurin “Is a long story! Ina mom da dad?” Tace cikin jin dadi, murnar su ce ta koma ciki mom tace “Gani nan Samha! Gani nan yata” Hugging nata tayi take suka fashe da kuka, rike ta gam gam Samha tayi like her life depends on it. “Samha sannu kinji? Sannu Samha! Ga Saudat nan kusa da ni” da sauri Saudat ta bata big hug cikin farin ciki “Muje ciki ki huta kinji?” Mom tace tana jawo hannunta “Mom ina dad?” “Am... yayi tafiya muje ciki” “Not yet there’s someone I will like you to meet” “Waye?” “Ya Areef ka fito dasu please” Sakin baki kowa yayi yana zuba ido don ganin su waye Samha ke nufi. Fitowa yayi a hankali Shatu na biye dashi a baya, wani uban ihu Amal ta fasa take jikinta ya fara rawa ta 6uya bayan mom da itama tayi mutuwar tsaye. Hilwa kam ma jikinta mutuwa yayi da ciki da ya kai kusan wata bakwai jikinta gaba daya ta kasa motsi sai kallonsa take baki sake. “Fatalwa! Mom fatalwa!!” Amal tace tana kara shisshige ma mom “No Amal! Ba fatalwa bane Fawzan ne da kika sani found him!” “Ina wuninku?!” Yace yana murmushi Ihu Amal tasa tayi cikin gida a guje, mom tabi bayanta da sauri, Hilwa ce ta dake ta kamo hannun Samha ta kalli su confused Adeel tace “Kuzo mu shiga ciki!” Binta sukayi gaba daya cikin gidan. Areef ne ya tsaya suka cigaba da tattaunawa da inspector din “Kuje ku kai masu sammaci har gida” “Eh gobe nake so naje na kai masu” “Yawwa haka yayi” “Mungode sosai inspector see you soon in court” “Insha Allah bari mu tafi Allah ya kyauta gaba” “Amin amin” yace yana bashi hannu sukayi shaking. Bankwana sukayi ya shiga cikin gida shima. Mom ce ta taimaka ma Samha tayi wanka ta bata kaya ta saka. Shatu ko in banda kauyanci ba abinda takeyi ta saki baki kawai tana Kallon ikon Allah. Da kyar suka samu tayi wanka shower na budewa ta fasa ihu kamar wacce aka biyo zaa kashe. Sai dai Amal ta tara mata a bucket tayi wanka, kaya aka bata ta saka. Sannan mom ta kira su dining gaba daya don cin abinci, Amal kin fitowa tayi saboda bataso taci karo da Adeel da kyar dai Hilwa ta fiddo ta. Ra6e ra6e takeyi tana xare ido, kusa da mom da xauna kan dining, serving Hilwa ta ma kowa, Basmati rice da shredded chicken sai salad, Shatu ta kalli plate dinta tana tunanin yadda zata ci abincin, ganin haka yasa mom ta mika mata spoon amma ina bata iya amfani dashi ba sai dai tasa hannu ta fara ci hannu baka hannu kwarya, kallonta kawai sukeyi kamar wacce ta shekara bataga abinci ba. “Mom An sa ma Fawzan abinci?” “E..eh ansa masa gashi yana ci” Tayi murmushi “Yawwa” Mom ke taimaka ma Samha har suka kare cin abincin suka tattara suka koma parlor. *****25 minutes later...
“Oh innalillahi wa inna ilahir rajiun, Allah abin godiya, yanzu kina cikin wannan halin duk bamu sani ba? da wani abu ya faru dake Samha bazamu ta6e yafe ma kanmu ba, oh Allah ka yafe mana...” mom ta fada tare da share hawaye “No mom, ba laifinku bane, laifina ne da ban sanar daku ba har nan nazo gida but lokacin ina cikin tashin hankali saboda nasan Haidar ne ya tare dad ya masa fashi, but I couldn’t control myself har na kwashi kafa na koma, and kuma kunje an hana ku shiga ne, so stop blaming yourselves” “Ya Rabbi ashe haka Haidar dinnan yake? Who could have thought zai aikata haka?” Areef yace cikin jimami “A gaskiya Haidar azzalumi ne, haka kika sha wahala ya Samha? A gaskiya kinga duniya Allah ya saka maki” “Ameen, ay zai sha mamaki lokacin da aka yanke masa hukuncin kisa” Hilwa tace “Tab! Amma Haidar Allah ka rabamu da irinsu, Allah shi zai saka maku duk wanda ya cuta ya kuma zalunta” mom tace “Insha Allah” “Wadannan sune wadanda kike zaune gidansu?” “Eh mom sune wato sun kula dani sosai, unfortunately Haidar ya bini ya kakkashe mutane da dama a ciki harda iyayensu” “Ya salam ya karin hakuri?” Sukace gaba daya “Alhamdulillah” “Allah gafarta masu” “Ameen” “Amma gaskiya kamar Fawzan duk da dai yace mana bashi bane” “No mom Fawzan ne, don kafin Baffa ya rasu naji yana ce masa ya nemi iyayensa da asalinsa” “Ko?” Cewar mom “Allah kuwa, kawai I think Fawzan lost his memory sadda yayi accident din” “Anya Samha? Shida ya tafi wata kasar me ya kawo shi kauye?” “Allah masani but duk sadda yayi regaining memory dinsa zaki tabbatar da haka” “Uhm Allah yasa haka toh, ki shirya anjima bayan isha’i zamuje asibiti a duba mun lafiyarki gaba daya” Ta gyada kai “Samha....!” Muryar Yasmin ce ta daki dodon kunnenta “Oh my God! Yasmin kina ina?” Mutuwar tsaye tayi ganin Samha, ta toshe bakinta da hannunta “What happened to your eyes babe?” Tace tana hugging Samha “Long story, I missed you babe” “Missed you more” “Yasmin ba gaisuwa kinga kawarki kin manta damu” cewar Hilwa Nan ta gaishe su cikin jin kunya taja hannun Samha suka haura sama. “I cannot believe this babe, Haidar din da kansa yayi maki haka?” “Wallahi kuwa Haidar din da kika sani dai” “Nifa tun lokacin da nake zuwa gidanki kullum ace baki nan and wayanki kashe na fara sensing wani abu” “Uhm at first ban yarda ba, amma daga baya na tabbatar mutumin nan bayida feelings is he even human?” “I don’t even think so!” “Allah ya saka maki” “Ameen babe” Nan suka cigaba da hira Samha na bata labarin abubuwan da yayi mata Yasmin harda kuka tayi na sosai ta tausaya wa Samha. ____________ A fusace ta shiga cikin police station din, tana shiga ta tarar da yan sanda. “Who gave you the right to arrest my son!?” “Excuse me madam, who are you?” “Kar ka gaya man maganar banza a nan! Ku kama dan nawa ka kuma tambaye ni ko ni wacece?” “Sorry we are just doing our job, what’s your son’s name?” “Aliyu Haidar Jamil!” Duba wani dogon book yayi nan yaga sunansa, da kuma laifin da ake tuhumarsa “See” yace yana nuna mata “Shine, inaso a bani bailing sa” “Sorry madam hakan bazai yuwu ba, laifin da ake tuhumar danki manyan laifuka ne don haka bazamu iya baki bailing nasa ba” “Wallahi karya ne! Dole zaa bani bailing sa” Bazamu bada ba gaskiya, sai dai kiyi hakuri har sai anje court tukunna” Huci takeyi sosai “Yanzu yana ina? Ko bazaa barni na ganshi ba?” “Za’a barki you have 15 minutes kacal” Wucewa tayi fuu inda wani police ya kaita cell din Haidar. Tana zuwa ta kirasa “Aliyu!” Da wuri ya taso ya matso inda take “Maama! Please get me out of here am feeling suffocated already! Bazan iya kwana nan ba” “Nayi iya bakin kokari na sunki bani bail dinka sunce sai anje court” “Yanzu maama sai ki barsu su kaini court?” “Toh ya muka iya?” “Nooo! Karki bari su kaini please maama help me out” “Ba yadda zamuyi sai anje! But I assure you mune da nasara a can” “Mom please ko nawa ne ki kashe muci case dinnan” “Kar ka damu, just be positive kaji? Everything will work on our favor!” “Yawwa thats my mom” “Toh bari na tafi, just take care ok!?” “I will” Nan ta wuce ta tafi shi kuma ya dinga kallonta ta cikin cell din, runtse ido yayi gam gam. Abu yaji an wullo masa ta kasa ya kalla yaga abinci ne kamar fate fate ko kalar kadai yasa yaji tuqar amai. “Idan kaga dama kaci abincin nan!” Wata nurse ta daka masa tsawa Tsoshe hanci yayi da sauri “God forbid baxan ci wannan kazantar ba!” “Then suit yourself” tana gama fadin haka ta kama hanya ta wuce, wani irin zafi yakeji kamar zai mutu. A hankali yace “I know I can count on you mom, you’ll get your son out of here...!”
God bless y’ll! ❤️
No comments:
Post a Comment