💄Fawzan ko Adeel?💍
Written by MSB✍🏻
Story by Maryam Sb (MSB) 😘💕
👄💋
Page 83-84
“Munifa kiyi sallar magrib ki cire ma Samha henna!” “Hanifah ke kuma idan an cire mata henna din tayi sallar magrib kiyi mata coiling hair dinta!” “Amal start her makeup!” “Yusra duba jakar da mukazo da ita ki fitar da kayannan!” Anty Safaa threw orders from one end to another, gaba daya suna sama dakinsu Amal. Samha was now freshly bathed and shaved, tayi wanka cikin wani abu kamar milk, farin color ne dai kuma yana kamshi. An wanke mata dogon hair dinta anyi coiling nashi sai sheqi yake da salqi. Gaba daya jinta dai take kamar wata princess, wannan ko aurenta da Haidar ba’a gyarata haka ba, gaba daya she looked so confused ta rasa gane meke faruwa. “What’s all this about?” Samha tace tana jiran Amna ta gama alwala ta shiga. “Can you kindly stop asking questions please? Do you want the surprise to be ruined again ha’an wannan Khadijan!” Hilwa tace tana cin cookies din da Samha tayi da safe. She rolled her eyes “Whatever don’t tell me” “Samha am hungry I will eat food before you pray” Yasmin tace tana tashi daga kan fluffy carpet din dakin. Hanifa ma ta mike daga kan carpet din itama “Me too let’s go and raid their fridge Yasmin” Suka fice da gudu suna dariya “Yasmin don’t touch the cake in the fridge please!” Dakin ya rage daga Samha, Munifa, Hilwa, Anty Safaa, Amna and Siddiqa. Samha wondered what they’re planning for her, it’s not even her birthday rather it’s Amal, she’s not even close to her graduation. Nan ta cigaba da saka da warwara ta rasa ganewa. Amna ce ta fito daga bathroom nan Samha ta shiga itama. Bayan ta gama sallar ne Amal ta fara mata makeup. “Ya Hilwa when is your due date?” Tana zaune kan gado wannan karon mango take sha tace “Third week of next month” Ta gyada kai tayi shiru aka cigaba da applying mata stuff a fuska kamar su foundation, eyeliner, kohl, lipstick, highlighter etc Yasmin da Hanifah suka dawo nan suka cika dakin da surutu Yasmin can talk for Africa, Volume din tv is high, baby Asaad ma hira yake taya su you can imagine hayaniyar dakin. An kammala makeup din around 8pm haka abinda kadai ya rage kaya. “Hanifah miko mun kayannan please” Anty Safaa tace tana mai tashi daga kan gado. Miko mata ledan kayan tayi ta fido tana mai dagawa sama, gaba daya suka bude ido suna kallon wannan floral gown din. It was dark pink in colour in fact very dark, it has a very simple design only two big golden buttons and a golden flower around the chest area. “It’s nice” Samha tace cikin murmushi tana mai kar6ar rigan daga hannun Anty Safaa. It was silky and soft with a v neck neckline. “Samha Please hurry up and wear it, akwai sauran aiki daura head and costumes” Yasmin tace tana tura ta wurin closet. Sanyawa tayi ta kalli kanta a mirror, tayi bala’in yi mata kyau ta hau da skin color dinta and tana jan kasa daga baya. “Ki fito haka nan muna son gani muma!” Yasmin tace da karfi Tana fitowa kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa! “Wow...” “Omg!” “Babe fire!” “You look like an adorable baby” “O’o guys stop!” Tace cikin jin kunya “Seriously you look beautiful” Yasmin tace tana kashe mata ido daya “Can you at least give a hint! Please” “Nope!” “Zauna” Yasmin tace holding head din da zaa daura. Nan ta zauna aka daura, bayan an gama aka bata matching shoes and purse, aka saka mata costumes. “ wow! Sai kace wata amarya” Cewar Amna Anty Safaa’s phone started ringing fita daga dakin tayi da sauri, bayan wani lokaci ta dawo tana kallon Samha. “Oya let’s go!” Dariya sukayi kowa ya tashi yana shiri. “Whaaat? Are you guys leaving now?” Ta tambayi Hanifah da Munifah ganin basuda niyyar tafiya. Sukayi murmushi “Nope!” Yasmin tace with a smirk “Zamu huta a nan” Twins din suka gyada kai a tare with a smirk too. “Zamu wuce kafin ki dawo” Those three hope they’re not up to something hmm!! Cikin ford din Anty Safaa duk suka tafi inda Anty Safaa ke driving. Throughout the journey Samha nata tunanin inda zasu je da kuma abinda zaa shirya mata haka. ___________ Finally suka iso at a brightly lit place. Gaba daya ko motsin qwaro ba’aji a wurin, the drive wasn’t long as Samha expected. Fitowa sukayi duka suka ce “Bye Samha and have fun” A tsorace tace “Fun alone? I don’t understand meyasa bazaku shigo ba?” Suka kyalkyale da dariya “Nothing will bite you, just go inside joor” Ta sauke ajiyar zuciya tace “Ina zanje?” “Straight to that building” Ta daure with a final goodbye to all of them and stared walking to the hall, gabanta in banda dukan uku uku ba abinda yake, she couldn’t wait to see what they’re up to! Tana shiga ciki taja tsaya ganin duhun wurin, hasken colors ne kawai ke tashi wurin kamar red, green, blue just like disco lights dai. Wurin kamar hall amma can end din kamar tunnel. Daga can nesa take hango inuwar mutum alamun yana tahowa, a tsorace ta dinga tafiya a hankali koma waye shima yana tahowa, she started seeing his face gabanta yabada wani dam! Is she dreaming? She couldn’t believe her eyes! Kwalwata ta tsaya cak da aiki... ya sakar mata da murmushinsa mai fizge zuciya. Gaba daya ga6o6in jikinta suna responding on how happy she was. When they finally reached each other, idanunsu suka kafe cikin na juna. Sanye yake cikin wani navy blue suit da wandonsa, sai red tie! “FAWZAN KO ADEEL?” Tace her voice almost cracking Ba tare daya bata ansa ba kawai taga ya zube kasa bisa gwiwonsa idanunsa taf da kwallar zallar farin ciki. “First of all of yes I am Fawzan, your dearest Fawzan, no Samha don’t make me stand I want to say few things to you” Ya hadiye kukan farin cikinsa yana kallonta cikin shaukin so kamar ya hadiye ta. “Samha you’re the best thing that ever happened to me, you make me happy, you’re my life without you I cannot survive, my soulmate, the love of my life, you’re my everything Samha, you love me with every situation I am in!” Dagowa yayi a lokacin ne kuma hawayen sunyi nasarar saukowa yayi sauri ya goge, jikinta a mace take kallonsa, her heart is already swelling of happiness she listened to the man she ever loved continued his speech. “I see my future when I looked at your beautiful eyes, Samha am on my knees to ask you to marry me, baby na will you do the honor of making me the happiest man on earth and marry me?” He asked giving her his million doller smile. A hankali music ke tashi inda hall din ya washe da tsananin haske, take taga uban mutanen dake kewaye dasu suna tafi raf raf raf!!! Wasu ta sansu don harda family dinta da nashi, rasa abinda zatace tayi don farin ciki hawaye kuwa already ya wanke mata fuska inda take tayi joining dinsa on the floor tana girgiza kai cikin tsananin farin ciki tana kuka sosai. God bless y’ll! ❤️
No comments:
Post a Comment