πFawzan ko Adeel?π
By MSB
ππ
Page 01
Karfe 8 na dare ta fito daga bathroom da alama wanka tayi, daure take da dark purple towel, gashin kanta wanda yake digar ruwa ne take ta faman tsanewa a jikin mirror, bayan ta kammala tsanewa ne ta fara shafa masa mayuka sannan ta taje tayi parking can tsakiyar kanta amma jelar ta sauko bisa kafadunta.
“Ya Samha!”
Yarinya ce yar kimanin 14 years ta shigo hannunta rike da wata waya kirar iPhone 6S fara mai pink cover, juyowa Samha tayi hade da murtuke fuska tace
“Bana hana ki daukan mun waya ba Amal?”
Amal tayi dariya tana mika mata waya tace
“Ya Samha can fa naganta parlor tana ringing shine fa na kawo miki” ta furta hakan hade da yin dan karamin pouting.
Samha tayi murmushi hade da hugging Amal.
“Sorry my cutie, and thank you”
Amal na fita Hilwa ta shigo a guje kamar wadda barayi suka biyo, sanin halinta ya sanya ma Samha bata damu ba don Hilwa haka take kullum cikin gudu take kamar wata yar 12 years alhalin she’s 20 years. Elder sister din Samha da Amal ce, Samha is 16 years Amal 14 sai Hilwa 20.
“Haba mana ya Hilwa tashin mun daga kan gado ki koma naki”
Ta fada tana saka kayan baccinta da ta fiddo a wardrobe.
Hilwa ta dan tabe baki cikin wasa
“Wai ke yarinyar nan sai kace gadon gold ba damar a hau kin kama masifa kenan”
Samha ta tabe baki itama
“Eh ga naki nan ki koma mana, ke kike mun gyara ne kullum? Gaskiya ki tashi ya Hilwa” ta fada tana nuna gadon Hilwa dake gefen nata.
“Bazan tashi ba...” tace tana gyara kwanciyarta ma.
Samha wani tsalle tayi ta fara kokarin dragging Hilwa daga gadon, nan suka fara kokawa har sai dai mom dinsu ta shigo ta fara fada, sai a sannan suka natsu.
“Hilwa kar ki kara jan kanwarki fada kina jina?”
“Yes mom” ta fada hade da jumping kan gadonta ta kunna laptop nata zata fara kallon series.
Bayan Samha ta gama kimtsawa ta fesa turare ta tattara towel dinta ta kai bathroom, ta kimtsa dakin, tana gamawa wayarta ta fara riging, lekawa taga an sa “Soulmate” take wani irin dadi ya lullube zuciyarta fes, kan gadonta tayi jumping ruf da ciki da pillow gabanta ta dora hannunta a kai.
Hilwa kallonta kawai takeyi don tasan wanda ya kira, kowa na gidan ya sansu tare saboda tun tana JSS1 yake sonta har kawo yanzu da take shirin kammala secondary school nata.
Lumshe ido Samha tayi tare da daukar wayan tace
“Hello!”
No comments:
Post a Comment