Thursday, 13 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 05

πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’

Written by MSB✍🏻
Story by Maryam Sb (MSB) 😘 πŸ’•

πŸ‘„πŸ’‹

Page 05

Yau ne ranar dasu Samha zasu fara exams, tun da sassafe ta tashi bayan tayi wanka ne ta sauko downstairs nan ta tarar da Amal cikin uniform Bisola na taya ta saka socks a parlor.

“Ya Samha morning”

“Morning Amal, kizo muyi breakfast mu tafi school, Bisola is breakfast ready?”

“Yes ma” Bisola tace tana dan rissinawa alamun girmamawa.

Kan dining ta wuce ta tarar da doya da kidney sauce, zuba musu tayi itada Amal a plate daban daban, suna tsakar ci ne mom ta sauko da kayan bacci tace

“Ah Samha har kun shirya?”

“Eh mom”

“Toh yau sai dai yayanku Areef yayi dropping naku Salisu yayi tafiya kauyensu an kirasa kanwarsa ba lafiya”

“Ayyah Allah ya sauwake”

“Amin” mom tace tana shiga dakin Areef dake downstairs.

“Areef! Kai Areef wake up!”

Motsawa yayi cikin muryan bacci yace

“Ohhh! Mom meyafaru?”

“Tashi zakayi ka kai kannenka school kasan yau Samha ke fara WAEC kuma Salisu bazai zo ba”

Da kyar ya bude idonsa ya kalleta

“Toh mom, bari nayi wanka”

“Kayi sauri kar su makara”

“Ok”

Karfe 7:40 ya kaisu school, nan Samha ta hadu da Yasmin, suka cigaba da karatu har suka shiga practical dinsu, bayan sun gama Areef ya dawo ya dauke su.

Bayan taci abinci tayi wanka ne taci karo da message na Fawzan, yana sending mata best wishes na exams dinta and how much he loves her. Dadi ne ya kamata yadda tayi dace da mai sonta sosai.

Kullum Areef ke kaisu at times daga can zai wuce office, har yayi kwana 7 sai a na 8 Salisu ya dawo ya cigaba da kaisu.

***

Samha ta kammala exams nata lafiya saura Neco, ranar data kammala ne Fawzan ya kirata yake shaida mata yana so ya turo magabatansa suzo gidansu, ta sanar masa zataje ta fadawa mom duk yadda sukayi zata kirasa.

Mom na kitchen itada Hilwa suna aiki Samha ta shigo, gefen mom ta tsaya tace

“Mom”

“Na’am Samha ya akayi ne?”

“Da...man...” sai kuma tayi shiru

“Daman me?” Mom ta fada tana cigaba da abinda take

“Daman wai... Fawzan ne...”

“Idan bazakiyi magana fita ki bani wuri baki gani inada abinyi ne?”

“Wai Fawzan ne yace yana so ya turo iyayensa nan gidan” ta fada tana wasa da fingers nata.

“Masha Allah, zanyi magana da babanku kome kenan zan fada miki”

“Wow burin masoya ya kusa cika” Hilwa ta fada cikin dariya

“Ya Hilwa!” Samha ta fada tana fita kitchen din da gudu

Tana jin dariyarsu mom sadda ta fice.

Da daddare bayan sallar magrib mom ta kira Hilwa lokacin tana bisa sallaya tana karatun qur’ani. Saida ta karasa karantawa ne ta maida shi ta aje sannan ta fita, dakin mom taje inda ta ke lazumi, samun wuri tayi ta zauna kasa kanta kasa tace

“Mom ina wuni?”

“Lafiya lau”

“Gani mom”

“Daman nayi magana dad dinku yayi na’am da magnar sai ki sanar dashi Fawzan din ya turo”

Kanta kasa tace
“Toh mom”

“Shikenan tashi kije”

Ta tashi ta fita murna a wurinta baya misaltuwa ji take kamar an mata kyauta da gidan aljanna.

Waya ta kira Fawzan yana dauka yace
“Kashe na kiraki”

“Okay” ta kashe

Bayan ya kira suka gaisa yace
“Baki bani feedback ba”

Tayi shiru bata ce komai ba.

Gabansa ya fadi
“Ya haka princess? Lafiya lau dai ko?”

“Da matsala ne dear”

Ya mike zaune gabansa ya tsananta bugu
“Matsalar me?”

“Wai dad ya mun miji yace kayi hakuri...”

“What? How come? Haba Samha kowa yasan ke nake so taya za’a mun haka?”

Dariya ta kwashe dashi tace
“Calm down wallahi wasa nake, dad yace ka turo”

Hamdala yayi inda yace
“A gaskiya sai na rama kin tayar mun da hankali ba kadan ba”

Cikin shagwaba tace
“Am sorry”

“Forgiven”

“Thank you”

Nan suka cigaba da hira har sai da aka kira isha’i sukayi sallama kowa ya tafi yayi sallah.

***

Washe gari da yamma akazo gidansu Samha, gaisuwa an karbe su a mutunce, inda akayi maganar sa rana aka tsaida nan da wata biyar, dangin Fawzan suka bukaci hakan saboda ginin da zai fara da dan sauran shirye shirye, suma iyayen Samha sunce ba matsala don za’ayi bikin yar uwarta nan da wata biyu, bayan an kammala komai washe gari aka kawo kayan sa kwanan biki, komai ya kammala lafiya sai dai fatan Allah kaimu lfy.

A ranar masoyan kasa bacci sukayi kowa yana nuna farin cikinsa da zakuwar zuwan wannan rana!

***

Shirye shiryen bikin Hilwa yana ta matsowa, hidima tama su Samha yawa, batada isashen time na kanta.

Gyaran jiki mom tasa ake mata sosai duk ta chanza sai haske take da sheki, ta kara kyau da haske. Wasu daga cikin friends dinta har sun fara zuwa kasancewar saura sati biyu bikin, yan uwa da dangi ma sun fara cika gidan.

“Ya Hilwa ki godewa  Allah amarya ce ke da na maki rm, da sai na shake ki yau dinnan”
Ta fada tana taya ta parking kayanta a akwati.

“Ya Allah me kuma nayi?” Ta tambaya tana turo baki.

“Kinga tun safe nake aiki kuma yanzu kince sai na tayaki parking”

“Am sorry ok? In kin gaji ki bari kawai zan karasa”

“A’a don’t worry we are almost done ai” ta fada tana cigaba da arranging wasu kayan cikin wani akwatin.

***

Hope you are enjoying this story? And thanks for reading! 😊

No comments: