Friday, 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 57-58

πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’  

Written by MSB✍🏻
Story by Maryam Sb (MSB) πŸ˜˜πŸ’•    

πŸ‘„πŸ’‹    



Page 57-58  



Sai da akayi isha’i suka shigo gidan shida Baffa da sallama suka karasa ciki, Gwaggo ta mike da ladabi ta masa sannu da shigowa gami da kar6ar ledar daya shigo da ita, gyara masu tabarma tayi suka zauna ita kuma ta shiga kitchen gamida kwala wa Shatu kira. Bayan second ashirin shiru “Ke Shatu! Kizo mana bakajin kira ne?” Ta fito bakin kofar dakinta tana soshe kai sai zum6ura baki takeyi “Gwaggo wadu muya (kiyi hakuri) ina kintsawa ne” “Zo ka karasa dama ma Baffa furannan bari na kai masu abincin” Daukar kwanon tayi ta samu wuri ta zauna ta cigaba da dama fura, ita kuma Gwaggo ta kawo masu abinci da ruwa da kwanon wanke hannu, wuri ta samu ta zauna su kuma suka fara cin abincin, jim kadan Shatu ta gama damawa ta hada masu furar ta zuba masu kankarar da Gwaggo ta bada aka siyo ta dire masu gabansu “Miyotti Shatu” Baffa yace yana cin tuwo “Shatu ga abincin marar lafiya ka kai mashi ka tabbatar yaci fa” Tayi shiru kamar bataji ba “Bakaji me nace ba Shatu?” “Naji yanzu zan kai” Ta wuce ta dauka ta kai mata. Baffa ya gyara zamansa yana kallon Gwaggo sosai “Ladingo yaya jikin wannan yaro?” “Dasauki sosai Baffa, idon ne nace sai yaushe za’a bude shi?” “Wallahi bansani ba, sai abinda mai bada maganin yace Ladingo, Allah ya kara mata lafiya” “Ameen Baffa” “Sai maganar wadannan yaran nakeso nayi maki ma’ana Shatu dashi wannan yaro Barkindo, maganar aurensu nakeso a saka karshen shekarar nan tunda shekarar ta kusa zuwa karshe, duka duka wata hudu ya rage so nake a saka bikin karshen shekarar nan” “Eh duk yadda kace Baffa yayi, Allah yasa alkhairi” Tsame hannu Barkindo yayi daga kwanon abincinsa ya fara kokarin tashi tsaye. Baffa ya daga ido ya kalle shi “Ah ina kuma zakaje Barkindo? Baka karasa cin abincinka ba, sannan bamu karasa maganar nan ba burinku ne ya kusa cika” “Eh... Baffa na koshi ne ina so na dan fita ne gidansu Jauro” “Toh toh... amma kar kayi dare Barkindo” “Jippu jam (a dawo lafiya)” Gwaggo tace tana kokarin tattara wurin. “Miyotti Gwaggo (thank you Gwaggo)” Fitowa Shatu tayi daga dakin sai faman washe baki take wane gonar auduga. “Shatu” “Na’am Gwaggo” “Yaci abincin?” “Eh” “Toh bari naje na bashi maganin” Kitchen ta kai kwanon abincin ta fito tana tsaye jikin katangar kitchen “Yar jakar uba ji yadda kika fito daga jin magana bukinku da Barkindo marar kunyar wofi” Baffa yace yana kai ludayin fura a baki Gwaggo ta kyalkyale da dariya “Hoo Baffa wannan irin zagi haka!?” Yayi kwafa “Yaron yanzu ba kunya sam sam” “Haka suke ay. Ke zo ka wuce ciki” Gwaggo tace tana kallon Shatu dake sunna kai wane munafuka dakinta ta shiga da wuri tana xuwa tayi tsalle kan yar katifarta.    Washe gari tun bakwai tayi wanka tayi kwalliyarta irin ta yan kauye aka wani fito sai kwarkwasa ake. Gwaggo ta iske tana share tsakar gidan ta rissuna ta gaishe ta “Shatu nikam a 6aaneke? (Kinyi bacci)?” “Eh Gwaggo nayi” “Toh ina zakije haka da sassafe?” Ta sosa kai “Zan kai maki markaden jiya ne na manta daman ban kai ba” “Tun yanzu?” “Eh Gwaggo” “Shatu kenan, toh kiyi sauri don Allah kar ka dade” “Toh”  Kwanon markaden ta dauka ta fito a guje sai gidansu Jummala.  Mika ya shiga yi daga bakin kofar dakinsa yana salati, kallon Gwaggo yake dake sanya hijabinta da alama fita zatayi “Gwaggo ina zakije haka da safe?” “Ah Barkindo har ka manta yau ranar kasuwa ce?” “Aw wallahi na manta Gwaggo, tun yanzu xaki tafi?” “Eh” “Ina Baffa?” “Ay ya fita tun dazu” tace tana daukar yar jakarta tare da sa6awa a kafada “Yawwa Barkindo batun marar lafiyar nan tunda kai kadai ne a gidan yau ki kula dashi kafin mu dawo, yanzu yana bacci, so nake in dan shiga kasuwa in siyo mashi kayan sawa bashida kaya kuma kinsan halin Shatu bazai bashi nashi ba” “Toh Gwaggo” “Abincinshi da magani suna nan a madafi na aje mashi zaki gansu a tare” “Toh Gwaggo Saito (bye)” “Minfotti (sai anjima) or (see you soon)” Daga haka ta fita yana mata a dawo lafiya  Dakin Samha ya leka ganinta a zaune yayi murmushi “Har kin tashi?” Tayi murmushin itama “Na tashi Fawzan kana ina?” Ya girgiza kansa yace  “Barkindo dai” Tayi yar dariya “Kai dai har yanzu baka yarda dani ba ko?” Shigowa dakin yayi ya zauna gefenta “Bazan ta6a yarda da kai ba, saboda xancenka ba gaskiya bane” Tayi murmushi mai sauti, kallonta yakeyi zuciyarsa na ayyana masa kyawunta “Komai lokaci ne zaka yarda dani” “Uhm ki fito tsakar gida na baki abinci kici, daga nan sai ki bani labarinki”  Gabanta yayi mummunan faduwa tuna Haidar da tayi shin in ya biyo ta nan ya zatayi da ranta? Tasan duk inda yake yanzu nemanta yake ido rufe! Kallonta yake duk ta daburbuce ta hada gumi lokaci daya “Lafiya?” Yace yana kallonta da mamaki “Ba...bu” tace tana kokarin saita kanta “Anya kuwa?” Tayi shiru, tsai yayi can kuma yace muje kici abincin, sandar ya miko mata ta kama ta mike tsaye ya jagorance ta har tsakar gida kan tabarma, kitchen ya shiga ya dauko abincin da maganin ya dawo ya zauna gefenta, ya bude langar ya bata cup din kokon. “Ci” yace da ita bayan ya matsar da abincin kusa da ita sosai Ci take a hankali shi kuma yana kallonta. “Kibani labarin hato a’ifti?” “Uhm?” Yayi dariya “Ashe bakijin fulatanci ko? Nace daga ina kike?” “Abuja” “Ina kenan?” “Wani gari ne” “Ya akayi kika zo nan kauyen daga can?” Tayi ajiyar zuciya “Labari ne mai tsawo Fawzan” “Barkindo dai” Tayi murmushi mai sauti “Barkindo ko?” “Eh ina jinki” Hadiye abincin tayi da kyar feeling hurt tunawa da irin kalar rayuwar da tayi da Haidar “Labarin yanada ban al’ajabi, mamaki, ban tsoro, cin zali da kuma tsantsar mugunta” “Toh bani inji toh” Nan ta shiga bashi labarin tun zamanin Fawzan da bayan mutuwarsa Da shigarta university da haduwarta da Haidar da kalar son da ya nuna mata kamar zai cinye ta, har aurensu da irin zaman da tayi da shi, da halayenshi da guduwarta har sake kamata da yayi ya cigaba da azabtar da ita da yayi, har ta samu ta sake guduwa sannan ta shigo kauyennan ba tare data san yadda hakan ya faru ba, har kade ta da akayi ta tsinci kanta cikin gidansu. Ta gama tana kuka mai ban tausayi, jinjina kai Barkindo yayi cike da tausayawa “Yanzu kana nufin kina da aure?” “Eh ina dashi”

No comments: