๐Fawzan ko Adeel?๐
Written by MSB✍๐ป
Story by Maryam Sb (MSB) ๐๐
๐๐
Page 97-98
Tun karfe 7 na safe Fawzan ya shirya zuwa aiki, asibiti ya kwana tare da Samha ba yadda ba’ayi dashi ba akan ya dawo gida tunda gasu Amal su kwana fir yaki sai da safe ya dawo, key dinsa ya dauko ya sauko downstairs yanufi dining inda ya aje food warmers making sure everything was set da zai kai asibiti, he made her favorite meal, duk abinda yasan zata bukata ya hada, fita yayi ya rufe gidan ya saka kayan a mota ya shiga ya tada motar, horn yayi mai gadi ya bude masa ya fice. Yana isa asibiti ya fito ya dauko kayan a daidai reception ya hadu da Aliyah tana sanye da riga da wando sai gyale. They both stopped at the same facing each other saboda ta tare masa inda zai wuce, wani irin mugun kallo yake ma Aliyah wanda yan hanjinta suka kada amma da yake yar duniya ce sai ta basar ta kalle shi da fara’a gyara murya tayi ta doka masa sallama ya ansa da kyar sannan yabi Ta gefenta zai wuce tayi sauri ta kamo masa hannu ta rike, hannunsa ya fizge sannan ya kalle ta cikin ido yana nuna ta da yatsa “Aliyah! Mind your own business and let me mind mine! And let me give you the final warning ki fita daga harkata kinaji na? Let me leave peacefully with my wife, bana sonki bana kaunar ki I only love you as my sister no more, but na tsani halayenki Aliyah, nasha fada maki ki rabu dani na by force ne wai? Bana sonki bana sonki and bazan ta6a sonki ba! Get that straight into your dull brain! And ki bari a sallami Samha zan gamu dake ne you just have to pay for what you did to my poor wife naki sai yafi worse!” Yan cikinta suka juya kar dai ya gano mu? No please! He can’t find out! Wucewarsa yayi ya barta nan tsaye tana tunanin maganganun da ya mata. A hankali ya tura kofar dakin ya shiga ciki,kwance take akan aqalla pillow uku tana ta baccinta sallama yayi a hankali and carefully placed the basket and a small bag bisa wani table. Yana zama kan wata kujerar dake gefen gadon Samha ta bude idonta tana ganinshi ta saki murmushi weakly. Kusa da ita ya koma ya zauna ya dora kanta bisa fad’ad’an kirjinsa yana shafa gashinta a hankali “Hope ban tashe ki ba Habibty?” “Nop! Ay nayi enough bacci kafin kazo yaushe ka shigo?” “Ban dade ba just a few minutes ago, I hope you’re feeling much better today?” “Yeah Alhamdulillah, I just need some custard or tea” Murmushi yayi ya mata light kiss saman kanta yana rike da free hannunta “Don’t worry Habibty nazo miki da duk abinda kike so” Murmushi tayi lokacin ne ya tashi tabi shi da ido inda ya shiga zuba mata abinci garlic mashed potatos ne da chicken soup, cup ya dauko ya zuba mata custard dinta ya sa sugar kadan, mikewa yayi ya dawo inda ya tashi ya zauna. Da kanshi ya mata brush sannan ya bata abincin inda ta kafe sai dai suci tare ba yadda ya iya haka sukecin abincin har suka gama, yabata custard dinta ta shanye abinta tas, ya mayar ya dawo this time around facing her. “Can you please stop staring at me like that?” Ta fada cikin jin kunya ganin yadda ya tsareta da ido “You’re beautiful...” Hannunta tasa ta rufe masa baki to stop him from speaking “And you’re handsome” Hannun ya kamo ya shiga mata kiss ta fara dariya sosai shi kuma ya dinga binta da ido komawa tayi ta kwanta feeling weak “Are you ok?” Ya tambaya cike da damuwa “Yeah am ok, I think dariyan da nayi ya gajiyan dani ne” “Ohh my poor baby, you need rest that’s why, stop stressing yourself ok? Who’s coming to stay with you while na tafi aiki, Amal?” “Yeah and Yasmin” “Get well soon please love” “I will” Zama yayi take yanayinsa ya chanza ya kamo hannuwanta duka biyun cikin nashi “Habibty am sorry once again... about how I have been treating you, no words to tell you how sorry I am, wallahi I am feeling ashamed of myself right now, can you find it in your heart to forgive your dearest husband?” Idanunta suka kawo ruwa she blink to push back the tears but a single stubborn one managed to escape “It’s really ok Habiby, am just happy that you realized the truth, I know life is full of ups and downs but all you we need to learn to is to exercise patience, I know an shiga tsakaninmu ne. What happened ko waye in your shoes haka zaiyi acting, I don’t blame you what only pains me the most da kaki yarda dani you rather believe our mai gadi, but really Habiby I forgive you with all my heart, daidai da rana daya ban ta6a regretting aurenka ba that I’m very sure you make me infinitely happy and that’s all that matters, Habiby zan cigaba da mana addu’a it will always be like that” Tunda ta fara magana Fawzan yake kallonta, Samha daban take a cikin mata she has a heart of gold who forgive so easily, irin macen da ya dade yana mafarkin mallaka, gaba daya ta mallake masa zuciya da kuma ruhinsa, itace haskensa! His peace! Kuma yasan baiyi regretting aurenta ba, Samha ta zame masa wani gurbi na rayuwarsa without her he don’t think he can survive, he love her smile, innocent, scent snd she is his strength he love everything about her, all he knows is that he love Samha more than life itself and can sacrifice himself for her happiness.
Matsawa yayi kawai tare da hugging dinta, she hugged back letting her tears fall freely. “I promise you no more tears kinji? No more fights insha Allah duk da nasan zaman aure ya gaji haka, but I will make sure I keep you happy” Samha’s heart melted, kuka tasa amma na farin ciki, shafa bayanta yake a hankali alamun rarrashi, sun dade a haka Suddenly the door flung open they quickly pulled away from each other suka juya suna kallon kofa only to see Yasmin and Amal looking at them “Opps! Sorry guys we didn’t know you were busy right Amal?” Jin Amal tayi shiru yasa ta dan bige mata hannu “Ahh! Well yeah, bari mu tafi mu dawo, sorry for interrupting your little...” “Samha I think zan tafi office I will see you later!” Ta dan yi murmushi kanta kasa da haka yayi sauri ya fita, Yasmin suka shigo suna dariya, Yasmin ce ta dinga tsokanar Samha har sai da ta dauki pillow ta wurga mata. ****** The next day da misalin karfe 8:30 na dare aka sallami Samha wanda ta warware sosai, tattara kayakinsu sukayi suka tafi, a hanya ne ya tsaya dominos pizza, haka ya shiga ya dade can ya dawo hannunsa dauke da kaya, yana shigowa ya miko mata ice cream ya bude kwalin pizza din, tare suke ci yana driving kafin su isa gida har sun gama. They arrived home suka fito daga motan Fawzan ya shigar da kayan, Samha ta gaji ga bacci, rufe motan yayi zai yi hanyar cikin gida. “Habibyyyyy....! Ya juyo yaga tana bubbuga kafa kasa yace “Menene?” Bayansa ta nuna tace “Goyo” he sigh before bending down Samha kuwa ta dale “It’s yours baby, forever and always” He walked into the house. A bakin kofar daki ne Fawzan yace “Close your eyes baby” Tayi murmushi and slowly close her eyes, “Now open...” she smiles sweetly at what Fawzan did, there were bunch of flower petals scattered on the floor, the room smells of mint and strawberry, the small scented candled were arraigned in lines, dakin duhu sai hasken candles. A hankali ya sauko ta daga bayansa tare da turning dinta and moving her close to him he slowly join their lips, they pulled back Samha na kara adoring dakin There was a big heart made with flower petals on the bed. “Awwn Habiby, thank you so much” “Shhh” yace yana dora hannunsa saman lips dinta yana kallonta cike da so itama shi din taka kallo. Shiga toilet yayi ya hada masu ruwan wanka sukayi especially Samha ta gasa jikinta sosai. Candles din ya kashe ya jawo ta ta fado jikinsa “I love you so much Habibty” “I love you too Habiby...” “I know” yace cikin murmushi That night promised were sealed sun kafa tahirin da bazasu ta6a mantawa dashi ba a wannan dare! ******** Kare goma da kusan rabi ta farka, ganin ba Fawzan kusa da ita, she smiles sweetly remembering each and every detail of last night, toilet ta shiga daman tayi wankanta da asuba, but still sai da ta kara bayan ta fito ta kimtsa cikin jeans da top ta sauko downstairs A dining ta hango shi yana arranging warmers. “Awwn! That’s sweet of you Habiby” Juyowa yayi ya bita da kallo yana murmushi “Anything for my darling wife” Fried yam sukaci da egg sauce and sausage, then tea and garlic toast. Samha taci sosai wanda hakan ya faranta ma Fawzan rai ba kadan ba, bayan sungama ya tashi can da ya dawo hannunsa dauke da plate ajiyewa yayi yace “Let’s eat” Chocolate donut ne “O’o ni na koshi” tace tana turo baki “O’o sai kinci” ya kwaikwayeta, ta fashe da dariya yana taya ta, da haka har suka gama. Hannunta ya kama suka tafi dakinsa ya cire shirt dinsa zai shiga wanka, Samha stared at his well build chest as it heaved up and down. “If you’re done checking me out your highnesses, now may I take my shower?” “I was not checking you out” “Kinsan dai karya haram ko?” Yace yana poking kumatunta “Ok sheik Fawzan, and yes you can go and have shower now, you don’t wanna be late do you?” “Ok just one kiss please” “Fawzaaan!” “Please...” Rolling eyes dinta tayi ta tashi tsaye tace “Close your eyes” Yayi yadda tace Sai jin kiss yayi a gefen kumatunsa, kafin ya bude ido har ta bar dakin a guje, shafa wurin yayi yana murmushi kafin ya shige bathroom don yin wanka. Koda ya shirya shi yayi dropping dinta school da niyyar in ta gama zaije ya dauke ta.
Yana kaita school yayi deciding yagaida Abba kawai sai ya wuce gida, Hajara mai aikinsu ce ta fada masa Mama ta fita kasuwa, yasan Abba na gida resting tunda yanzu ba office yake fita ba sai once In a while, bayan sun gama gaisawa ya dan jima ya fito zau tafi kawai sai ya rika jin maganganu ta dakin da Aliyah ke sauka tunda ta maida masu gida kamar nasu bata fiya zama gidansu ba sai dai ta kwaso ta taho gidansu, definitely yasan itace a dakin ba wani ba. A bakin kofa ya tsaya yana jin kamar waya take “Shatu! Wallahi Fawzan ya gano mu fa!.... we’re in trouble! and I know zai hadani dad dina wallahi am in deep shit!” “You sure are in deep shit” Fawzan yace yana tsaye daga bakin kofarta ya sa hannunsa daya cikin aljihu “I will call you back!” Tace tare da kashe wayan da sauri “Ina kwana ya... Fawzan” “What’s good about the morning!?” Yace yana matsawa inda take “Yanzu ke a tunaninki abinda kikayi is fair?” Yace yana kokarin danne anger dinshi “Fawzan I did all this because of you... I love you so....” “Shut the hell up! I asked you a simple question just answer yes or no! Do you think what you did to my poor wife is fair? Answer me now!!!!” “No... but...” “Good, no right? What the hell did I tell you to stay away from me i can’t marry you right, that I don’t love you? Yes or no?” “But it’s your fault! Why ya Fawzan? What is my fault da nace ina sonka is it a crime? Meye Samha ta fini dashi? Na fita shekaru me kagani a jikin qwaiilar nan ni da baka gani a nawa ba? Na tabbatar ba banza ba asirce ka tayi if not meyasa zaka fifita bare akan jininka?” Dauke ta da wani wawan mari yayi hagu da dama har sai data ga stars ihu ta fasa tare da dafe wurin. “You’re a pathetic excuse of a human being, yanzu ma na tabbatar you’re dumb as well, let me make something clear to you, Samha is far better than you wallahi you can never be like her even if you try, and kinsan bambancinku? She has a heart of gold she has been nothing but nice to you, you and Shatu disgust me! How can you both stoop this low? You try to ruin our happiness but let me tell you something, our bond is even stronger than before ni kun taimaka mun ma yanzu cuz I have realized just how much more I love my wife, and no matter how hard you try to break our bond it won’t work! And no matter what you did I will never ever marry you ever! I only love Samha no one else! Again kin bani kunya da abinda kikayi da ita kanta Shatu after all they did to her da abinda zata saka ma iyayenta kenan? And don’t you ever dare come to my house wallahi duk ranar da naga kafarki gidana sai na kakkaryaki. Black magic or whatever you call it, she has my heart I love my Samha more than anything in the world you can go ahead and use that your big dirty mouth and announce it to the world for all I care! Whenever kikayi hurting Samha ni kikayi hurting and we’re one insha Allah till death do us part, none of you can break it not even you Aliyah! Change or else I assure you you’re gonna die in this world alone cuz ba wanda zaiso ya auri mace mai irin halinki as his wife da wannan bakin halin naki!” Juyowa yayi yaga Abba tsaye bakin kofa yayi crossing hannayensa. “Abba... I....” “What happened?” Nan Fawzan ya kwashe komai abinda sukayi ya fada masa. “Abba yarinyar nan ta matsa mun ta hanani sakat inyi rayuwana yadda nakeso, ta hanani farin ciki, ta hanamu zaman lafiya! Ina so ayi mana katanga da ita ta kyale mu!” Zubewa tayi kasa tana kuka saboda tsananin shakkarsa da takeyi “Kayi hakuri Abba, na tuba please forgive me” “Forgive you? Sake fadi kiga idan ban farfasa maki kai yanzun nan ba, nonsense! You have wronged an innocent girl you should ask for her forgiveness not me, I know exactly how to deal with you! I have a friend Alhaji Buba wallahi shi zan aura maki cikin satinnan zan ce masa ya turo, daman matarsa ta rasu yana neman mata, shikenan sai nace masa ga mata har gida I will just talk to my brother your father! And I know zai yarda! This is pure stupidity!” “Abba please no! Innalillahi wa inna ilahir rajiun! Abba please forgive me kar ka aura mun Friend dinka Please Abba!” Ta fada cikin tsananin kuka “Ya Fawzan please help me beg Abba wallahi bazan sake ba, bazan sake shiga harkaka ba and I will ask for her forgiveness but please Abba kar ka aura mun shi...” Fawzan ya gimtse dariyarsa “No! I think is a good idea gaskiya since you’re been picky kin tsaya ruwan ido kin kasa za6ar mijin aure, am with Abba on this one! In fact zaku dace da juna ma” yace yana washe baki “Noooo! We won’t wallahi! Abba don’t do this to me!” Tace tana girgiza kai hawaye na zuba daga idonta kuka take bilhaqi. “I have said it! And there’s no going back! I have made my decision you better start preparing for your wedding!” Ware ido tayi ganin da gaske Abba yake ta kurma ihu tare da fashewa da wani irin kuka.
God bless y’ll! ๐
No comments:
Post a Comment