πFawzan ko Adeel?π
Written by MSB✍π»
Story by Maryam Sb (MSB) ππ
ππ
Page 37-38
Bayan kwana 2 sai ga kayan sallah Haidar ya kawo mata atamfa guda 2, lace, takalmi, jaka, kayan kwalliya, turare and 3 matching veils, ba karamin mamaki tayi ba, da farko batasan waya aiko ba sai dai akace gashi akace a bata.
Daki ta koma tana budewa taci karo da note ta bude
_How’s my princess doing today? Hope good? I love you with all my heart Barka da sallah in advance_
Batasan lokacin da murmushi ya su6uce mata ba, wayarta ta dauka ta kirashi a karo na farko a rayuwarta.
“Baby na” yace cikin shaukin so
“Your message arrived just now”
“Yea, do you like it?”
“I do but I can’t accept them”
“Why? Saboda baki sona or ban isa ba?”
Nan take ta gane ranshi ya baci
“Ba haka bane wallahi”
“Then explain...”
Shiru tayi ba tare data ce komai ba.
“Yanzu har rashin son da kike mun ya kai kiyi denying kyautar dana baki?”
“Wallahi a’a, nagode sosai Allah kara budi na alkhairi”
Tanaji yana dariya
“Haba har naji dadi, toh ranar sallah dai I will be expecting pictures ko?”
“Okay, but on one condition”
“What?”
“You send me yours too”
“Really princess? That means you want to see your handsome boyfriend’s kwalliyan sallah”
Murya kasa kasa tace
“Done”
“And su Ayman”
“Yes ma”
Yaji tayi dariya, a beautiful laugh
*****EID DAY
Samha batasa kayanta masu tsada ba wanda Dad dinta ya mata ba, na Haidar ta saka tashiga daukan pictures tana sending masa.
Ba 6ata lokaci taga call dinsa na shigowa
“You look stunning my love”
“Thank you, you all looked beautiful too”
Ya turo mata family pictures din da suka dauka gaba daya. Ba karya sunyi kyau sosai.
“So ya sallah din?”
“Alhamdulillah”
“Masha Allah, ya kamata nazo na biya kudin kwalliyan nan ay ko?”
“Uhm”
“My princess kenan, ko kar nazo?”
Tayi murmushi
“Toh sai nazo take care of yourself for me, I love you”
“Thank you” tace kafin tayi disconnecting call din.
****After magrib
Bayan sallah yazo for the first time gidansu Samha, yasamu kyakkawan tarba daga iyayenta, nan ya shaida ma mahafinta yana so a bashi dama ya turo da iyayensa suzo, dad yace an bashi amma ya tabbatar ya samu kyakkwan fahimta daga yarinya ma’ana su daidaita kansu.
Sun sha hira da Samha inda ya bata kudi 20k yasha gwagwarmaya kafin ta kar6a, bankwana sukayi ya tafi ita kuma ta koma gida.
***
Ba 6ata lokaci Haidar ya turo gidansu Samha da niyyar formal introduction amma sai dad ya bukaci saka rana da duk abinda ya kamata, an sa 2 weeks immediately after their second semester exams.
Washe gari aka turo kayan sa rana, tadai sha zolaya wurin Yasmin kamar me.
__*___*___*__*__*__*
School resumed a week after sallah, everything went in full speed, nan lecturers suka dinga rushing dinsu with tests and lectures gaba daya batada lokacin kanta hakan yasa Haidar ya daina matsa mata yana so tayi karatu da kyau.
*
“What part of I’m studying for my exams you didn’t understand?
No... ba haka bane I will let you come as soon as muka gama...
Noo I just want to study ne fa...
I promise I will let you come as soon as exams are over... alright toh... bye...”
“What was that about?” Samha tace Yasmin na ajiye wayan
“Wallahi wani maye ne ya matsa man”
Samha tayi dariya
“Oh that man at the wedding?”
“Shifa mtsss” she hissed
“Yasmin kikace kin fara sonsa?”
“Its just that he love me too much, he disturbed my life bana son takura haka da yawa”
“Mtss I feel like punching you right now! So if a guy loves you too much is a crime kuma? You better enjoy it while it lasts”
*****
Ranar da suka gama second semester exams Dr Haidar yazo, they took a long walk da daren.
Suna cikin tafiya ne yace
“Yanzu gobe zaki tafi?”
“Eh”
“Wow, so nan da 2weeks kin zama tawa?”
Shiru tayi tana kallon kasa
“Nasan bakiso na kamar yadda nake sonki, amma insha Allah with time zakiso ni”
Tayi shiru
“Ko ba haka ba princess?”
“Uhm”
Sun dade suna hira har dare ya soma tsalawa.
“Do you want me to pick you up tomorrow?”
“No dad zai turo driver ne”
“Oh okay”
Motansa ya bude ya fiddo mata wata leather
“Here take this”
Kallonsa tayi
“Wai kam baka gajiya da wahala ne?”
“A kanki bazan ta6a gajiya ba, kar6a in bakiso kiga 6acin raina yanzu” ya wani hade rai
Ba don taso ba ta kar6a ta shiga masa godiya sosai sannan ta wuce hostel.
“Lover birds” Yasmin tace Samha na shigowa dakin
“Uhm kedai kika sani”
Kar6an leather din tayi daga hannunta nan ta bude taga dankareren wristwatch mai tsadar gaske.
Bude baki tayi tana kallon agogon
“Wow, lallai gayen nan akwai kudi kinga agogon nan mai tsada ne fa sosai”
“Yeah” kawai tace tana brushing kanta gaban dan mirror dinsu.
***** one week later
Samha ce taje gidan Hilwa
“Samha don Allah zanci dan wake” Hilwa tace her baby bump was already showing
“What happened to the one you made?”
“I can’t eat it, amai yake sani”
“Gaskiya ya Hilwa wannan ciki naki ya cika kwashe kwashe tam, ki gode Allah is my little baby da bazanyi ba”
“See this amaryan nan last week da mukaje jerenki do you consider my situation kika ce na bari ba sai naje ba?”
“Kai ya Hilwa mom even told you kar kije but kika kafe”
Rolling eyes nata tayi
“Toh naji sarkin iyayi, go and make it please in banci ba akwai matsala”
Haka taje kitchen ta dora mata sadda ta gama har Hilwa tayi bacci, murmurshi kawai Samha tayi ta zauna ta fara kallo.
Tana farkawa ta tambayi dan wakenta. Kasan carpet ta baje ta fara ci
“Wonders shall never end, yau ya Hilwa ke cin danwake, the last time I checked bakya son danwake”
“Pregnancy does change a person kinji yarinya, nima mamaki abin ke bani, abinda baki tunani ci nake”
Tana gamawa ta tashi taje tayi brush, ta dawo
“Kin san yadda na tsani warin toilet dina yanzu bana son shiga kwata kwata, and bana son warin turare na”
“Wow, thats...” Samha tasa dariya
“Don’t worry naki na tafe”
Samha tayi rolling eyes nata. Adnan na dawowa ta fara shirin tafiya.
“Samha I don’t understand why do you always run away when my hubby comes back”
“Because karna zama bare a cikinku, yanzu zaku manta dani”
Adnan da Hilwa suka sa dariya
“We’re sorry Samha bazamu sake ba” Adnan yace yana dariya.
Murmushi kawai Samha tayi ta fice daga parlon tana waya da Salisu akan cewa gashi ya dawo daukanta.
*****
Satin bikin Samha ya kankama, abu kamar wasa, daman tuni an kawo lefe akwati set 8, kayan sunyi ba karya.
Tuni mom ta fara shirin gyara amarya dilka ake mata kasancewarta fara tuni ta kara haske kamar wata balarabiya, skin dinta yayi lub lub kamar sabuwar haihuwa.
“Tashi ki sha” mom tace tana miko mata wani abu marar kyan gani
“What’s this?”
“Ina ruwanki? Zaki tashi ko kuwa!”?
Tashi tayi ta kar6a ta rufe ido ba don taso ba ta shanye mom na tsaye kanta, bayan ta gama mom tace
“Tashi ki shirya mai lalle tazo” ta tashi ta saka simple doguwar riga ta fita.
Lallen ya mata kyau ya kuma zanu, gwanin ban sha’awa.
It was the day of the awaited event, wani dankararen pink lace tasa gaba daya shigar pink tayi, tayi kyau kamar a sace ta a gudu.
“Amarsu ta ango” Amal tace tana gyara mata head nata
“Uhm Amal kin zama marar kunya ko?” Hilwa tace tana shigowa dakin
“Wow masha Allah amarya kinyi kyau sosai, oya tashi za’a fara tafiya, ke kadai ake jira”
Suna isa event din inda amarya kawai ake jira, wurin ba karamin kyau yayi ba, best friend dinta tana nan makale da ita har suka iso.
Hankalinta ya tashi itafa batasan crowd, yanzu ya zatayi gashi duk saboda ita akazo?
She felt a warm hand hold her tana dagowa taga Haidar ne, tadan ji sauki nan hankalinta ya dan kwanta.
Hand in hand suka shiga event din, nan aka shiga dukansu hotuna, har suka zauna. Nan mc ya shiga aikinsa har akayi announcing it was time to cut the cake.
LOVE was spelled and they cut the cake, shi ya fara bata, sannan ta bashi a kunyace.
Bayan nan aka umarce su da suyi rawa filin, nan aka shiga masu liki, har finally suka koma seat nasu.
Da haka akaci aka tashi har event din ya kare kowa ya nufi gida.
**
Washe gari karfe 2 aka daura aure immediately after Friday prayer.
Wanka mom tasa tayi na fresh mint and strawberry flavored soaps, tana wanka tana tunanin yau shine last day nata a gidansu kenan?
Bayan ta fito aka shiryata, nan aka mata fadan nan da ake yi kuka kam baa magana duk sunsha kuka barin ma Amal kamar ita za’a kai ba Samha ba.
Finally aka fito da ita aka tafi kaita gidanta, saida suka fara kaita gidan mother Inlaw dinta then to her house.
Kowa ya watse sai su Amal wadda suka gaji da jiran angwaye suka tattara suka tafi.
Ita kadai ke zaune kan makeken gadonta har yanzu ta kasa daina kukan.
Tun tana sa ran shigowar ango har ta gaji bacci ya kwashe ta.
A gigice ta farka sakamakon karar buga kofa da akayi, da sauri ta tashi zaune gabanta yayi mummunan faduwa, tashi tayi a hankali ta taka bakin kofa tana zuwa taji an damko ta, kara ta saki a tsorace tana kallon ko waye, ganin Haidar yasa ta tsorata da ganin yanayinsa.
“A...H? Lafiya?”
Jawota yayi da karfi ya wullata cikin dakin, tim ta fadi kasa, kuka ta saki a hankali
“Are you really ok?”
“Idan kika kara magana sai na baki mamaki, tashi ki bani hakkina!”
“Wane hakki?” Ta fada cikin rashin fahimta
Cakumo ta yayi da karfi, ya wullata kan gado. Toshe hanci tayi sakamakon warin giyar da taji yanayi
“Innalillahi daman AH na shan giya?” Ta fada cikin tashin hankali
Saukar mari taji a kumatunta ta saki kara a gigice.
“Kikace bakisan hakkin ba? Zan nuna maki!”
Kokarin rabata da kayan jikinta yakeyi ta karfi ta yaji, ita kuma tana kokarin kwace kanta tana ihu kamar ranta zai fita.....
Thanks for reading! π
No comments:
Post a Comment