Thursday, 13 June 2019

FAWZAN KO ADEEL Page 02

💄Fawzan ko Adeel?💍


By MSB✍🏻 
Story by Maryam Sb (MSB) 😘 


Page 02

“My baby”

Husky voice dinsa ce ta daki dodon kunnenta. Lumshe ido tayi tare da dora kanta bisa pillow saboda dadin kalmar da ya furta har cikin kanta tsabar dadi. 

“Meyasa kikayi shiru? Are you alright? Is everything ok? Are you sick?”
Duk ya furta lokaci daya a rude. 

Da kyar ta bude baki a dalilin jikinta da ya mutu tace

“Lafiya lau. Don’t worry”

Ajiyar zuciya ya sauke, sannan yace
“Alhamdulillah, yau nakejinki ba kamar yadda sa saba ba, that’s why”

Tayi murmushi 

“Wallahi I am ok, kawai gajiya ce school especially da muke preparation na WAEC and islamiyya hadda and all”

Murmushi yayi
“Hakane just take it easy ok? Allah ya bada sa’a”

Tace 
“Insha Allah love, thanks”

Yace
“I love you so much”


Murmushin jin dadi tayi tace
“Nima haka”

Yace
“Kema me?”

Tayi murmushi mai sauti hade da sunne kai kamar yana ganinta.

Yace 
“Ina jinki kema me?”

Tace 
“Nima I...”

Sai kuma tayi shiru saboda kunya, abinda ke burgesa kenan da ita, duk dadewan nan da sukayi Samha najin kunyarsa sosai”

“Shikenan bazan sake kiranki ba tunda haka ne”

“No!” Yaji ta fada da sauri, yayi dariya 

“To fadi man mana baby”

Da kyar tace
“I love you more”

Kit! Ta katse kiran, Fawzan dariya kawai yakeyi saboda nishadin da yakeji a duk sadda sukayi waya da Samha. Haka ya kwanta cike da mafarkinta kala kala.

Washe gari kasancewar Saturday ce ba school, suna tashi misalin karfe 8 na safe kowa ya fara aikin gida kamar yadda suka saba. Bayan sun kammala wurin 10 suka zarce kitchen suka fara hada breakfast, kafin 11 sun kammala da taimakon Bisola mai aikinsu, bisa dining suka kai komai suka jera, suna kammalawa yayansu ya shigo daga shi sai yar riga marar hannu da gajeren wando.

“Ya Areef morning”
Suka furta gaba daya 

“Morning yan matan mom, an tashi lafiya?”

“Alhamdulillah”

“What’s for breakfast today?”

Amal ce ta furta “Garlic bread da tea, sai chips and egg with kidney sauce”

Yace “ok” dakinsa ya koma a yayinda kowa ya shiga nasa dakin don yin wanka. 

Ba’a jima ba Samha ta shirya cikin multi color doguwar riga ta material, sai zuba kamshi take. 

Kowa ya hallara dining, ita kawai ake jira, nan ta gaida mom dunsu, da dad dinsu wanda ya shirya da alama office zai je. Shima Areef yayi wanka tare suke fita office da dad shima can yake aiki. 

Nan kowa ya shiga serving kansa, wurin yayi tsit sai karar spoon kawai kakeji. 
Bayan sun kammala ne dad ya mike tare da Areef inda zasu tafi office, nan mom ta raka dad bakin mota tare da fatan a dawo lfy. 

***

Fawzan ne yayi shiri cikin black shirt da jeans, rigar ta dan kama sa kasancwarsa ginannen mutum, Fawzan yana da tsayi daidai misali sannan yana da jiki, shi ba fari ba shi ba baki ba, yanada da yalwataccen gashi kuma coiled hair mai santsi da kyau, yana da sajen sa da ya kara bayyana kyansa sosai. Yanada manyan idanu mai yala yalan lashes masu tsayi kai kace macece. Hancinsa kuwa shi ba dogo ba shi ba guntu ba, bakinsa dan daidai misali, daka kanshi kasan bazai haura 32 years ba. A natse ya kammala shirinsa ya dauki wayoyinsa guda biyu dake kan dressing mirror da key din motarsa ya fito. Tun daga nesa take kallonsa yana taku dai daya akan stairs har ya sauko gaba daya. Hango ta yayi take ya murtuke fuska murtuk kai kace bai taba dariya ba.

“Ya Fawzan ina kwana?”
Tace tana masa kallo kamar zata cinye sa.

“Fine” yace da ita yana cigaba da tafiya side din dad dinsa.

“Ya Fawzan...” 

ta furta da dan karfi. Juyowa yayi yana mata kallon (What do you want?)
A hankali ta tako inda yake sai da tazo dab dashi tace

“Saboda kai fa nazo gidannan”

“And so what?” Yace yana duba agogon hannunsa.

“Haba Ya Fawzan, kafa san dalilin da yasa nake zuwa, kuma ko ba komai you are my cousin ka daina mun wulakanci”

“Idan kin tsaya limits naki zan yi respecting naki, but if not, i will not, so I beg you let me be, kinsan bana sonki I told you this before, wai wace irin brain ce dake? Bakya gane bayani, ina da wacce nake so kowa yasani, kema kinsani, so kiyi hakuri ki rabu dani please”

Hawaye ne ya cika idonta
“Haba ya Fawzan... ka taimake ni, tunda kaga nakasa daurewa har na furta maka kasan ba karamin so nake maka ba, ka tausaya min...” kuka ne yaci karfinta, nan ta juya da gudu ta fita.

Ajiyar zuwa yayi
“Am sorry Aliya but I can’t love you back, my heart belong to Samha’s, only her alone”

Ya fada sannan ya juya ya shiga side din dad dinsa.




Issaaa long chapter right? Thanks for reading!

No comments: