Thursday, 13 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 04

πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’

Written by MSB✍🏻
Story by Maryam Sb (MSB) 😘 πŸ’•

πŸ‘„πŸ’‹

Page 04

A lokacin data shiga Amal bata nan da alama ta fita, gyaran murya tayi saboda yadda ya tsare ta da idanu har ta zauna bai sani ba.

“Meyasa kake kallona haka? Sai kace yau ka fara ganina”
Ta fada tana murmushi

Murmushi yayi shima yace

“Nothing... you just look so beautiful”

Murmushin jin dadi tayi tace a hankali
“Thank you”

Nan suka cigaba da hira irin ta masoya har Hilwa ta shigo da sallama, Bisola na biye da ita a baya, dauke da katon tray, nan suka shiga sauke kayan inda basu gama ba, bayan sun fita suka sake dawowa da wasu trays din shidai sai kallonsu yake har suka gama, daman sun gaisa da Hilwa don haka ficewa kawai sukayi.

Ya dinga bin kayan da kallo sannan yace
“Kar dai wannan duk a cikina?”

Ya fada yana zare idanu

“Yes of course! I spent hours preparing all this for you with love, don haka dole kaci”

Yace
“Dole ma naci koda cikina zaiyi gobara, but on one condition”

Ta dan zaro idanu
“What condition?”

Ya gyara zama yana nuna abinci
“Komai tare zamu ci, if not bazan ci ba”

Ta sunkuyar da kai tana murmushi
“Nidai a koshe nake”

Ya dan murtuke fuska “daman ki sauko muci, if not bazan ci ba nima”

Ba yadda ta iya haka ta sauko tayi musu serving, suka fata cin abincin, yana ci yana zuba santi, Samha ita dai dariya kawai takeyi cike da jin dadi. Bayan sun gama ta masu serving dessert, nan ma dai santi yake ta zubawa Samha na dariya.

Suna gamawa ta kwashe komai ta kai kitchen, bayan ta dawo ne kuma suka dasa hira cike da nishadi, har sai da ya kalli Hublot wristwatch din dake hannunsa 9:30 ya gani, ya dan zaro ido kadan.

“Dare yayi ashe bari na tashi na gudu haka nan”

Nan Samha ta shiga ciki, jim kadan ta dawo da leather a hannunta, daman ta masa packaging donut, cookies da cake dinsa. Har bakin mota raka sa.

“Good night baby, Will surely miss you”
Ya fada yana kokarin shiga mota. Bayan ya shiga ne ya juyo yana kallonta cike da so.

“Koma ciki sai na tafi gida ko, to make sure you are safe”

Murmushi ta sakar masa tace
“Good night Habibi!”

Sannan ta juya da gudu tayi cikin gida, binta yayi da kallo har ta shige yana ta murmushin da bai san yanayi ba, yafi minti 2 kafin ya tada motarsa ya bar unguwar cike da kewarta.

***

“Ahh yah Rabb!! I think am regretting zaban Arctic! Wallahi ina tsoron next paper din da za’ayi, gashi lecturer din mugu ne bayada mutunci”

Hilwa tace tana flinging pages na book nata dake gabanta.

“Toh ba wanda yayi forcing dinki ki zabe shi daman ai ko?”

Banza ta mata tana cigaba da flinging pages din sai kace tana karantawa.

She started her exams some days ago
and she’s going crazy.

“Kinsan akwai subject din da nake tsoro nima”

Wani irin kallo ta bi Samha dashi daga sama har kasa sannan ta kwashe da dariya.

“What?” Tace tana kallonta da mamaki.

“Zauna nan, karatun Uni daban na secondary daban so stop comparing”

“Da gaske nake ki tambayi kawata Yasmin mana kiji”

“No” Hilwa ta fada tana rufe books nata.

“Sis ki yarda dani kawai ku yanzu ba abinda kukeyi sai wasa”

Harara Samha ta daka ma Hilwa

“Kin manta!”

“Believe me zaki gane idan kika shiga”

Samha tayi murmushi tace

“Toh naji amma dai ki daina jin tsoro, and kisani cewa da Ci da Faduwa duka suna cikin good grades na rayuwarmu, you should write your exams without any fear”

“Hakane kam”

“Bring a book na baki wata addu’a alright?”

Ta girgiza kanta alamar ok tare da bude jakanta ta fito da book nan take jotting duk wata addu’a da take bata, Alhamdulillah Samha tana da ilimin addini daidai gwargwado Saboda dagewa da takeyi a islamiyya.

_Kiyi alwalla, kiyi nafila raka’a biyu, kiyi salatul-nabiyy sai ki karanta- Allahumma innee As-Aluka wa atawajjahu ilaika bi Nabiyyina Muhammadin Nabiyyir Rahamati. Ya Muhammadu innee Atawajjahu bika ilaa Rabbee fa yagdhee hajjatee. Nafilar nan tanada matukar amfani ya Hilwa, it’s called Salatul Haajah, and kinga batada tsayi kiyi kokari kiyi_

“Jazakallahu bil jannah, Allah ya kara basira Samha, and thank you so much zanyi insha Allah”

Tayi rolling eyes nata

“Don’t thank me”

***

A kwana a tashi yau saura 1 week Samha su fara exams, shiri takeyi sosai ta dage tana ta karatu, batada lokacin kanta bale ma na masoyinta Fawzan, so shima yasan tana shirin exams ne sheyasa bai fiya takura mata ba.

***

Ana saura kwana uku su fara exams Yasmin tazo gidansu Samha, ba karamin murnan ganinta tayi ba, nan aka cika ta da snacks da drinks kala kala.
Sun sha hira mostly akan samarinsu ne da kuma shirin exams.

Bayan sallar la’asar suna zaune a daki Yasmin ta kalli Samha tace
“Don Allah ki raka ni salon”

“Ok toh bari na fada ma mom”

Nan ta tashi taje ta sanar da mom tace ok Salisu ya kaisu, ta kuma bata kudin salon din.

Shiryawa sukayi suka fita zuwa salon inda Salisu ya kaisu.

Salon din a cike yake da mutane, amma da yake sun saba da wurin don nan Yasmin take zuwa koda yaushe, ba yadda suka iya haka zasu zauna su jira.

Tana fada ma Yasmin labarin yadda zasu sha bikin Hilwa da ake shirin sakawa ne wasu mata su biyu suka shigo. Kallo suka bisu dashi inda suke sanye da matsatsun kaya kamar ba musulmai ba sai taunar chewing-gum sukeyi unlike ladies manners.

Yan matan na ganin su Samha ne suka murtuke fuska don ko ba’a fada mata ba tasan itace budurwan ya Fawzan, tsaki tayi suka zauna opposite kujeransu Samha.

Harara kawai suke watsa ma Samha inda ta kula amma ta share don batada lokacinsu.

Nan suka gama abinda ya kawo su suka tashi zasu tafi Aliya tasa kafa ta harde Samha saura kiris ta fadi take Yasmin ta fara zazzaga bal’ai daman tunda suka shigo suke raina ma mutane hankali.

“Are you stupid?” Yasmin tace murya dage

Samha ce ta jawo hannunta. “It’s ok rabu dasu Yasmin”

Aliya ta watsa masu harara tare da jan uban tsaki sai taunar chewing-gum taka kas,kas, kas...

Fita su Samha sukayi waje inda motan da zai kaisu gida yake suka nufa bayan sun shiga ne Yasmin tace
“Da kin kyale ni naci ubanta, na lura batada manners sam”

Samha tayi dariya tace
“It’s ok kinsani ance shiru ma magana ce da kin rabu da ita”

Amma duk da sai da Yasmin tayi tsaki cike da jin haushin yan matan.

“Wannan yarinyar ta shiga uku kin dinga maganar ta kenan har next week”

Hararan Samha tayi cikin wasa inda tace yamma nayi ko suyi dropping nata gida kawai.

***

Da daddare ne Hilwa na gyara gadonta zata kwanta bacci ne Samha ke bata labarin incident na dazu.

“Da kunci kaniyansu yan rainin wayau kawai”

“Su suka sani bazan biye masu ba, so ya exams?”

“Good Alhamdulillah”

“Are you sure ya Hilwa? You didn’t sound like it was good”

“Aswear it is, kawai na gaji ne” ta fada tana hamma

“Toh ki kwanta mana”

“Yanzu insha Allah, yau bakuyin magana daa Fawzan?”

“Ahh ya Hilwa sa ido tab”

“Yes, my regards and good night”

9:32 “Assalam” ta masa message ta whatsapp.

9:45 “Wa’alaikumusalam, is my princess missing me?”

9:47 “Yes” 😒

9:48 “I missed you more” πŸ’‹

9:50 “Yasu Mami da Abba?”

9:59 “Alhamdulillah kowa fine”

10:01 “masha Allah”

10:04 “Let me call you”

10:04 “Okay”

Nan ya kirata suka cigaba da hira mai cike da nishadi, har sai da Samha ta fara jin bacci, shima bai kashe ba har sai da yaji tayi bacci daman haka yakeyi baya kashewa har sai tayi bacci sannan yayi disconnecting call din. Itama kanta Samha ta saba da hakan.

***

No comments: