Friday, 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 79-80

๐Ÿ’„Fawzan ko Adeel?๐Ÿ’


  Written by MSB✍๐Ÿป
Story by Maryam Sb (MSB) ๐Ÿ˜˜๐Ÿ’•    


 ๐Ÿ‘„๐Ÿ’‹



    Page 79-80     “Kamar yadda kasani mu biyu ne a gurin mahaifinku marigari, kuma nice matarsa ta farko, tun baida shi nake tare dashi wanda talauci yayi mana katutu da kyar muke samun meal daya muci a rana, kafin a auro Safina matarsa ta biyu Allah ya jarabemu da abubuwa da dama, na farko talauci mai tsanani, na biyu haihuwa na uku tsana daga uwar mijina, matar bata sona bata kaunata kamar yadda ta tsaneni take fadi mani juya aka auro aka aje mata. Sannan tasha fada mani cewar tunda aka auro ni danta yake ci baya abin alheri bai ta6a samunsa ba tunda na shigo gidan, tayi tayi ta raba auren abin ya faskara saboda tsananin son da mijina ke mani. Haka muke zaune da ita a gida daya ga daki ga daki, duk abinda mijina zai mani idonta na kai, ko leda ya shigo da ita sai ta kwace ta raba mana biyu ta dauki rabi ta bamu rabi. Haka nan nake zaman hakuri nima soyayyar da nake ma mijina ita ta zaunar dani gidan ba don raina yaso ba, kuma duba da yadda ya jajirce yaki bin umarnin mahaifiyarsa na rabuwa dani naga ban kyauta masa ba indai har na guje sa.   Wata rana na fita kasuwa ina dawowa daga bakin kofar zaure naja na tsaya jin maganganun da uwar mijina ke fada ma Jamil mijina. “Jamil kanka daya kuwa? Yanzu a matsayina na uwar data tsugunna ta haifeka amma ka kasa yi mun abinda nakeso? Kana neman albarka kuwa dannan?” “Inna duk abinda kikeso fa ina yi miki indai baifi karfina ba”  “A’a karya haram, tun yaushe nake binka ka kara aure kaqi? Ko shima kayi mun abinda nakeso kenan?” “A gaskiya Inna bazan iya kara aure ba Allah ma yasani” “Dalili?” “Haba Inna a cikin wannan halin talaucin nawa zan kara aure ina kike so na aje ta? Sannan gaskiya bana jin zan iya adalci a tsakaninsu, ke kinsan yadda nakeson Maryam a cikin zuciyata” “Wannan juyar? Har akwai abinda ta ta6a tsinana maka tunda ka auro ta?” “A gaskiya Inna bazan iya jure ana ci ma Maryam fuska ba, Maryam yar halak ce, ga hakuri ga juriya, ga uwa uba ladabi da biyaya, duk yadda take daraja ki sam bakya gani, yanzu baki gudun in auro wadda bata ganin mutuncinki da kima sa6anin ita Maryam?” “Kar ta gani din mana, nidai burina kawai inga yan dugui dugui suna yawo”  Yayi shiru hade da rafka tagumi  “Indai kana neman albarkata ya zama dole sai kayi aure, kaji na gaya maka”  Tana fadin haka ta tashi ta shige dakinta. Murmshin dole na qaqalo sannan na sa kai cikin gidan da sallama, Jamil dake zaune ya tare ni da murna yanata kokarin kar6ar ledar dana shigo da ita. Hanashi nake sonyi yana hanawa nace “Kayi hakuri Jamil, kudin dake hannuna basu isa mu siya abinci ba sai dai garin kwaki da gyada da sugar na siyo mana” murmushi yayi yace  “Kar ki damu sarauniyar mata, a jiqa mana mu sha”  Bayan mun gama cin abinci ne muna daki ina linke kayan Jamil na dago ina kallonshi “Wai nikam ka kai takardunka sunqi daukarka aiki?” Ya numfasa “Wallahi Maryam duk inda baki tunani nakai sai dai ace inje in jira, toh kinsan yanzu dole sai kai wani ne ko dan wani kake samun aiki da gaggawa” Na numfasa Komawa nayi na zauna gefensa na kamo hannunsa “Mijina meyasa bazaka iya kara aure ba?” “Aure kuma? Waya ce miki zanyi aure?” “Ba kowa amma kasan abinda Inna takeso kenan” “Kiyi hakuri amma bazan iya kara aure ba” “Haba mijina abin alfaraharina, a gaskiya ka daina wasa da uwa, koda baka so ka daure kayi kodan ka faranta mata rai, uwa ba abar wasa bace, ka manta Allah (SWT) da kansa yace mana mu kyautata masu muga haske a rayuwarmu, mu kuntata masu muga kunci, don haka ka jure ka daure kodan ka faranta mata rai, kar ka manta ita kadai fa ta rage maka a duniya, kudai samu ku rabu lafiya” Murmushi yayi “Sheyasa a kullum nake alfarahari dake a matsayin matata, da zarar na kauce hanya xakiyi saurin dawo dani saiti, nagode Allah yayi maki albarika, insha Allah zan yi kokari inyi, amma wani hanzari ba gudu ba” “Me?” “Ina naga kudin aure a wannan hali?” Murmushi nayi na miqe na bude wani dan akwatina na fiddo wani dan madaicicin box na miqo masa. “Wannan kuma fa?” “Bude ka gani” Razana yayi ganin dan kunne set daya na gold. Miqo mun yayi yana girgiza kai “Meyasa zaki bani abinda kike adanawa saboda amfaninki?” Bata rai nayi “Toh meya amfaninsa indai bazan iya baka ba kayi amfani dashi ba? Kar ka manta abuna naka ne haka naka ma nawa ne, indai baka so inyi fushi da kai ka kar6a ka saida kayi aurenka, Allah ya bamu zaman lafiya” Godiya ya shiga zuba mun harda kukansa na nuna masa ba komai.  Tunda ya sanar da Inna aurenshi ya tashi ta fara murna kullum cikin sako mun habaici take, ban ta6a nuna abin na damuna ba na shanye na jure na cigaba da taya mijina hidimar aurensa.  BAYAN AURE  Safina itace wacce Inna ta za6a masa a matsayin matarsa, da farko yarinya ce mai hankali da nutsuwa, muna zaman lafiyar mu duk da Inna tana nuna bambanci a tsakanin mu hakan ma ban nuna ya dameni ba. Wani abin tashin hankali ya sameni wanda na rasa dalilin faruwarshi, Jamil ya daura man karan tsana babu gaira babu dalili, ya daina bani kulawa, ya daina mani magana, amma in suna tare da Safina kamar yayi mata sujjada, yunwa har ta fara kamani saboda bana samun abinci gidan gana daya sun hade mun kai daga Safina har Jamil da kuma Inna, na rasa yadda zanyi, abu kadan zai hauni da duka da zagi, na rasa wannan chanji daga ina yake. Haka na zauna duniya ta mun qunci, gashi banida iyaye duk sun rasu da sai in tafi wurinsu, haka nan nayita hakuri har Safina ta samu cikin farko, murna a wurin Inna ba’a magana nan da nan ta fara tarairayarta sai abinda takeso zataci a gidan koda babu dole sai Jamil ya nemo mata, haka tayita rainon cikin har ta haifi ya mace, wai wai tunda ta haihu rayuwata ta sake fadawa cikin qunci fiyeda da, ko kusa da diyar ban isa na matsa ba, Inna zatace zan shafa mata talauci, iskanci Safina ta 6ullo dashi kala kala, ga ta raina Inna kuma Jamil ya kasa komai a kai. Ranar suna yarinya taci suna Shukrah, nan aka cigaba da bata kyakyawar kulawa, tana yin shekara daya cif a duniya Safina ta sake haihuwar wata macen aka sa mata Zuwaira, tunda Shukrah da Zuwaira suka taso Allah ya dora man sansu suma haka, duk yadda uwarsu da Inna sukaso hanasu hulda dani abin ya faskara, dole daga karshe suka hakura suka barmu tare, tunda Zuwaira ta fara wayau bata yarda kowa sai ni, sai mamanta tayi da gaske take kwace ta hannuna tayita kuka kamar zata siqe, dole zata hakura ta maido man ita. Haka zalika Zuwaira na shekara daya kuma ta sake haihuwa wannan karon namiji ne aka sa masa Fawwaz, naga habaici wurin Inna ta kara tabbatar man ni juya ce, Jamil kuwa har yau ba ruwansa dani, tunda aka haifi Fawwaz al’aumurra suka soma chanzawa wato Jamil ya samu aiki, nan kudi suka fara shigo masa har ya fara ginin dan gidansa, da tsohon cikin Safina ya kammala gini, sai naga ya kwashi Inna da Safina da yaranta ya maida su can ni kuwa ya barni nan, a cewarsa ya raba mana gida da matarsa, ranar naci kuka na tabbatar namiji ba dan goyo bane. Haka rayuwar ta cigaba da kasancewa har ta sake haihuwar Muhammad, can suka sha shagalin sunan da ba’a ta6a irinsa ba, an kashe kudi ba kadan ba, bayan wata shekara ta sake haihuwar Zayyan, bayan ta yaye shi yasa ta shiga makaranta ta cigaba da karatunta, na dage da addu’a Allah ga dube ni ya kawo mun d’auki don yunwa na neman halakani, ba ruwan Jamil dani hakkinsa kawai yake kar6a ya kama gabansa. Ina cikin wannan halin Allah ya azurta ni da ciki mai laulayi, nayi kukan farin ciki, koda na fada ma Jamil ciki ne dani banga wani farin cikin da yayi ba sosai, na kalleshi nace “Ya naga bakayi murna sosai ba?”  “Murnar me? Sai kace wani sabon abu? Yayana biyar fa, sai kace wani na farko” wani qululun abu ya tokare mun wuya, na dai daure na cigaba da sabga ta, haka nan cikin yayi qwari a wahalce, dari biyar din da yake bani duk sati ciki nake cin abinci, nake kuma tara yan kudin da nake siyan kayan jarirai, da kyar na siya riga biyar ciki, bayan na haihu na samu da namiji, wato Aliyu Haidar shine sunan da yaci, shima tunda na haifesa muke a wahalce, inaso in fara sana’a banida jari, ko abinci ba muda isassun kudin ci, bare in samu na sana’a a ciki. Haka ya taso cikin baqin talauci wanda babansa da matarsa suna can cikin daula amma shi gashi nan yana cin abinci da kyar, a gaskiya Jamil ya bani mamaki ba kadan ba. Bayan ya girma na kuma samun ciki wannan karon mace na haifa Asma’u tun daga kanta ban sake haihuwa ba. Haka muka cigaba da rayuwa kullum yayana cikin kukan yunwa sukeyi, na rasa yadda zanyi dasu, haka nan nake shiga maqota ba don naso ba naje na roqo masu abinci, daga karshe suka gaji dani suka daina bani, suna isa shiga makaranta na kaisu makarantar gwamnati, daga baya Inna ta rasu, bayan an gama zaman makoki arzikin Jamil yaja baya kadan, baya samu kamar da. Haka xanyi tagumi ina tunanin mafita don zamannan bazai yuwa haka ba, naga Aliyu ya shigo a guje yana haki, bayana ya 6uya yana kuka. A razane nace “Lafiya?” Kafin ya bani ansa har naga wasu mutane sun shigo a guje nasa salati ina tambayar meyake faruwa? “Wannan 6arawon danki ya bani kudina” A razane nace “Waye 6arawon?”  Sukace Aliyu ne ya satar masu kudi, nan na kama tambayarsa inda gaske ne yace eh amma wallahi ba da son ransa bane yunwa yakeji, kuka nasa na kwace kudin na basu hakuri na haushi da duka, kome suka gani kuma suka miqo man kudin cike da tausayi suka ce muci abinci, nace a’ah mungode. Nan nayita masa fada da nasiha akan sata ba kyau kar ya sake.  Danaga xamannan bazai yuwu haka ba na kwashi kafa na tafi gidan Jamil, inda Safina tasa akayi man korar kare itada shi haka na fito ina kuka takaici kamar xai kasheni.   Bayan wani lokaci   A farkon dana fara saka Aliyu cikin wannan sana’ar shine wata rana muna zaune tsakar gida nida shi nace “Aliyu ya zama dole ka nemo aiki ko sana’a ka rika yi ko wace iri ce” “Maama wace sana’a ce ban gwada ba? faskare, yin furnitures, noma, babu irin wadda banyi ba kina gani dai anqi daukata” “Hakane, amma akwai wata mafita” “Ta mey?” Na gyara zama “Fashi da makami”  A razane ya dago yana kallona  “Fashi da makami kuma?” “Eh Haidar ko so kake mu mutu da yunwa ne? Kalli kanwarka tana ciwon yunwa yau satinta uku kwance, irin wannan sana’ar kuwa take ake samun kudi” Ya girgiza kansa “A gaskiya bazan iya ba maama, haka kurum aje a kamani” Nasa kuka “Ka taimaka mana Aliyu kar mu mutu da yunwa” shima cikin kukan yace “Toh naji, amma duk abinda ya sameni ke zan ba laifi” “Na yarda”  Tun daga wannan ranar Aliyu ya fada sana’ar a hankali ya dinga bunkasa, arziki ya bude sosai, amma wallahi bayan wannan ban ta6a sanin yana wani abin ba, wallahi wallahi, daga baya mahafinsa da Safina suka rasu ta hanyar gobara inda Allah ya auna arziki yaran kaf basu nan, sai daga baya na dauko su na cigaba da rike su a matsayin yayana, wanda duk sunsan cewar bani ni haifesu ba, ban ta6a nuna masu banbanci tsakaninsu da nawa ba, a gafarce ni ya mai girma mai shari’ah, nice na jawo wa dana wallahi, ni naja masa rashin tawwakali, da rashin hakuri da rashin imani a zuci” Ta karasa cikin kuka Alkali yayi rubuce rubucensa ya dago yana kallonta. “Hukuncin da aka yanke ma Aliyu Haidar yana nan za’a kashe shi ta hanyar rataya, ke kuma kotu zata daure ki gidan yari na tsawon shekara goma tare da horo mai tsanani na jefa danki cikin sana’ar data takaisa ga yin kashe kashe, nan gaba komin takaucinki kar ki kuskura ki jefa kanki ko waninki ga aikata 6arna, court is dismiss” “Couuuuuuuurt....!” Alkali ya miqe kowa ya miqe aka wuce da Aliyu Haidar inda ya rokemu gafara take muka yafe masa tare da fatan alkhairi, mahaifiyarsa ma aka wuce da ita nan yan gidansu suka yi ta kuka, tabbas ba dadi amma hukuncin kisa dole ne tunda shima kisa yayi shine hukuncin da ya cancanci ayi masa. Da wannan kowa ya nufi gidansa, inda take aka kashe Aliyu Haidar ta hanyar rataya.    



************    


6months later........          



God bless y’ll! ๐Ÿ’•

No comments: