Friday, 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 07

 πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’


Written by MSB✍🏻 
Story by Maryam Sb (MSB) πŸ˜˜πŸ’• 




πŸ‘„πŸ’‹




Page 07




Kai kawo yakeyi a tsakanin dakinsa daga bed nasa zuwa kofar fita ta dakinsa, minti kusan 20 ya dauka sannan daga karshe ya samu gefen gadonsa ya zauna tare da zurfafa cikin tunani.

“I can’t do this, I just can’t” ya saki ajiyar zuciya. 


Shigowa cikin dakin tayi da dan karamin tray a hannunta da ya kunshi glass of milk, ajiyewa tayi a side bed drawer dinsa sannan ta kira sunansa har sau kusan uku, ganin yaki motsawa ya sa ta dafa kafadunsa...

“Ya Fawzan...”

Firgit! Yayi tare da dago daran daran idanunsa wanda suke farare tas amma yau sun koma ja saboda tsananin damuwa. 


“Ya Fawzan lafiya na ganka haka?” Ta fada cike da damuwa.


“Ba lafiya ba Yusra” 



“Yaya menene?”

Nuna mata gefensa yayi alamun ta zauna,ba musu ta zauna tana kallonsa cike da natsuwa.

Numfasawa yayi sannan yace


“I received a message from the agency, wai sai naje Iceland nayi 2 months, nan da 2weeks zan tafi and work starts immediately na isa can”


“Kai yaya to shine abin damuwa?” Ta fada cike da mamaki


Kallonta yayi cike da takaici
“Ya zaki mun wannan tambayan? I can’t believe this! My wedding is in 3 months, I have alot to do here, shirye shirye and all, ina kike so naje at this very moment? And kina tunanin ma zan iya 2weeks ne banga Samha ba talkless of 2 months?”

Murmushi Yusra tayi

“Huh calm down yaya, I know how you must be feeling now, aure ba wasa bane I know, but this is all about been a pilot daman ya gaji haka, yawo from one place to another right? Kuma da kake maganar you have alot to do now baga Abba nan ba? Am sure idan ka bar masa aikin bakada wata matsala, daman ai shine problem dinka, gini Abba zai taimaka, lefe mom zata dauki nauyin or daga can ka hado, and lastly Samha, yaya wannan ne karo na farko daka fara tafiya kana barinta? Sau nawa kake traveling kaje ka dawo? Sai yanzu? Why yaya? Sahma ba inda zataje har ka dawo, ba abinda zai same ta then why are you worried for no reason?”

“No Yusra I have a bad feeling about this, gani nake kamar wani abu zai faru idan na tafi, that’s why ni sam bana so naje sai naga anyi auren nan an gama...”

“Haba yaya ya kake magana haka ne? Wane irin bad feeling kuma? Insha Allah ba abinda zai faru har ka dawo, kana dawowa just 1 month zai rage bikin, and zaka iya karasa duk wani shirye shirye”

“I know Yusra, is just that...”


“Shhh, Insha Allah nothing will happen, Allah bada sa’a, everything will be fine”


“I hope so”


Tashi tayi ta dauko masa milk nasa

“Smile, and drink this”

Karba yayi yana sha a hankali, ita kuma Yusra ta fice daga dakin.






*****


“But kullum zan koya miki tuka keke fadowa kike I wonder how you are ever gonna drive a car”
Ya fada yana dariya sosai


“What’s funny? It’s not even a girly thing”


“But it’s fun baby, ya ma akayi kika iya tukawa tukunna?”


“Ban iya ba, I was scared gani nake kamar zan fado”

 Dariya kawai Fawzan yakeyi sosai, don yana tuna sadda take JSS2 yasha fama da ita akan tuka keke amma ina.


Awa daya kenan yana waya da Samha, yana so ya fada mata game da batun tafiyarsa zuwa Iceland.


Daga karshe dai yayi gathering courage wane wannan ne first time da zai fada mata irin haka.


“Babe”


“Uhm?”


“I have something to tell you”


“Yes ina jinka dear”


“In 2 weeks time zan tafi Iceland zanyi 2 months tukunna zan dawo”


Shiru yaji ba response, take ya fara regretting sanar mata ma da maganar gaba daya. 


“Sweetheart why are you quiet?”


“Na’am?”


“Bakiji me nace ba?”


“Sorry I did”


“Then what do you think? Idan kikace kar na tafi wallahi ba...”


“A’a ya Fawzan, ba haka bane wallahi, kawai dai abin yazo mun a bazata, you know ga auren mu na matsowa kuma ace baka tare dani, and it’s just that I will miss you badly”

Sai ta fara kuka, ya rude ya dinga rarrashinta da kyar tayi shiru 

“Haba baby na, ya haka? Kina so ki karya mun kwarin gwiwar tafiya ne? Idan kina kuka ai bazan iya tafiya ba”


“Kayi hakuri dear, ba haka bane am sorry” tace tana share hawayenta

“To ya isa haka nan kukan, am sorry kinji, kamar gobe ne zakiga na dawo fa”


“Nasani, yanzu nan da 2weeks zaka tafi?”


“Insha Allah baby”


“Toh Allah kaimu, Allah ya tsare mun kai ya kare ka, ya bada sa’ar abinda akaje nema”


Dadi ya kama shi da jin wannan addu’ar

“Ko kefa baby, ameen ya Allah”


Nan suka cigaba da hira irin ta masoya wanda basa gajiya da junansu...

















Thanks for reading !

No comments: