Friday, 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 10

πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’


Written by MSB✍🏻 
Story by Maryam Sb (MSB) πŸ˜˜πŸ’• 




πŸ‘„πŸ’‹




Page 10




Dafa ta Amal tayi a kid’ime, tare da kiran sunanta.


“Ya Samha! Lafiya dai haka?”


Girgiza kai ta shiga yi
“Bazaki gane ba Amal”

“Bazan gane me ba?”

“Wani irin mummunan mafarki nayi” ta fada tana goge zufa a fuskanta

“Mafarki kuma? Daga yin mafarki sai ki bi rude jifa yadda kike zufa”

“Dole nayi zufa Amal” ta fada tana murza goshinta da yatsunta

Zama Amal tayi gefenta 
“Mafarki fa ba gaskiya bane ya Samha”


Daga mata hannu tayi
“A’a Amal, wannan mafarkin bai mun kama da karya ba, it looks so real” 

“Toh naji me kika gani a mafarkin?”


Ajiyar zuciya taya sannan tace
“Wai ya Hilwa na bacci, kin tashe ta wai kina mata nasiha and kika ja hannunta kuka je wasu kofofi kala kala and kuna zuwa kika nuna mata gawar Fawzan yana kwance...” tace all in one breath.


“Ok ok first of all take a deep breath, and relax” 

Tayi yanda tace 

“Ya Samha na kara fada maki mafarki ba gaskiya bane, kima daina daga hankalinki nothing will happen”

Kallonta kawai takeyi kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, a hankali ta shiga saukowa daga kan gado sai da ta sauko gaba daya sannan ta kalli Amal

“Daman bance something will happen ba bamu fata, just mafarkin looks so real bazaki gane ba”


Amal tayi murmushi 
“Jekiyi wankanki kawai”

Toilet ta shiga ta rufo kofar, tana shiga Amal ta tashi ta shiga gyara dakin. 

Mintina kusan 20 ta dauka kafin ta fito, bayan ta gama shafe shafenta ta saka wata doguwar rigar atamfa, fitted gown light pink color, turare ta feshe jikinta dashi, gaba daya batada walwala tunanin Fawzan takeyi da dalilin da yasa har yanzu bai kira ba. 

“Ya Samha na gama dafa indomie ga taki ko nan zakici?”

Yamutsa fuska tayi
“Nace miki ina jin yunwa ne?”

“Ya Samha please” 

“Okay kawo mun nan,  ina Hajiya?”

“Tana wanka”

“Okay”


Tura indomie din tayi da kyar Ta samu taci rabi, dauka tayi ta ba Samira yar aikin Hajiya. 

“Ya Samha na lura bakya son cin abinci kwanan nan” Amal tace tana cin indomie 

“Ko? Sarkin sa ido”

“Ya Samha! Basa ido ba muna tare ai dole na gani ko?”

“Please sharrap and mind your business”

“Ahh! Sorry”

“Sorry for yourself abeg”


Dariya ta su6uce ma Amal.
“Temper din ta mecece kuma daga tambaya?”

“Oho” tashi tayi ta shiga dakin Hajiya, zaune ta iske ta tana gyara ganyen zogale

“Kai Hajajju kedai kina son kwadon zogale”

“Ku ai bakusan dadi ba”

“Nidai bai mun ba”

“Kaji yan gayu, bakusan komai ba sai shamarma take ko me? Da wannna abin pitta”

Dariya ta kwashe Samha
“Wayyo Allah kauyis, shawarma ake cewa da pizza”

“Ohon maku”


“Toh kawo na taya ki tsigewa”

Bige mata hannu tayi cikin wasa

“Banso”

“Yi hakuri kawo har kwada miki zanyi”

Ta dalla mata harara
“Sai kace iyawa kikayi”

Ta turo baki
“Na iya mana kawo na baki mamaki”

Mika mata tayi
“Bani mamakin toh”

“Angama”

Tsigewa ta shiga yi har ta gama, sannan ta kwada mata yaji albasa da tumatir, yaji kuli
Kuli ma, bayan ta gama ta mika mata
“Gashi kici ki fada mun yadda yayi”

Tana ci ta soma yamutsa fuska
“Tir ba dadi ungo kayanki”


“Kai kai kai!” Samha ta fada tana kokarin kwace kwanon

Hajiya ta rike gam
“A’a saki Khadija”

Samha tasa dariya
“Amma kikace ba dadi?” 

“Babu”

“Bani toh”


Amal ce ta shigo
“Ya Samha lafiyanki?”

“Lau” bayan ta karbi kwanon 

“Bata abinta” cewar Amal tana hayewa kan gado

“Tace ba dadi”

“Wai kin raina yar baiwar Allahn nan”

Hararanta Samha tayi bayan ta mika Hajiya kwanonta.

“Tashi ki bani wuri toh”

“Yi hakuri Hajiya”

“Naki”

“Please”

“Nayi” 


Tashi Samha tayi, daki ta tafi don ta manta wayanta saman gado. 5 missed calls ta gani na Yusra.

“Yeey! Nasan zata fada mun wani abu  dangane da Fawzan” 

Da sauri ta kira sai dai har ta tsinke ba’a dauka ba, ta kara kira a karo na biyu nan ma dai ba’a dauka ba. 

Sai kuma taji hankalinta ya dan tashi, nan ta dinga kira amma ba’a dauka ba.


Da sauri ta shiga dakin Hajiya 
“Hajiya don Allah sa direbanki ya kaini wani wuri”

Ta dago tana kallonta”
“Ina zakije da safe haka?”

“Gidansu Yusra” ta mata karya

“Toh kice yankaiki mana, kar ki dade amma dai”

“Toh Hajiya” ta fita da sauri, Amal ta lura da yanayinta yasa ta tashi ta biyota

“Ya Samha lafiya?”

“Amal yaya Yusra ta kirani amma inata kiranta bata dauka ba”


“Toh shine me?”

“Ina ji a jikina ba lafiya ba, can gidan zanje”
Ta fada tana zura hijabinta black color 

Amal ma hijabin ta dauko
“Toh muje na raka ki”
Bata tsaya jiran me zatace ba tabi bayanta da sauri.


Tunda suka shiga mota take kiran layin Yusra tun ba’a dauka har aka kashe gaba daya.



“Ya Samha don Allah ki kwantar da hankalinki”


Shiru tayi kurum in banda faduwa ba abinda gabata keyi.



Tunda suka doso unguwar gabanta ya tsananta bugu, duk yadda Amal taso kwantar mata hankali abin ya gagara.

Motoci ta gani ko ta ina a layin, gabanta yayi mummunan faduwa, a hankalinki take karanta Innalillahi wa inna ilahir rajiun.

Kofar gidan mutane ne birjit, har da kyar mota ke ra6awa in zata wuce. Tuni Samha ta rude, tun kafin motar ta tsaya ta bude ta fito a guje, Amal ta fito tabi bayanta da gudu tana kwala mata kira amma ina hankalinta baya jikinta, tun daga waje ta soma jin koke koke...


















Hmmm! Nayi shiru dai 🀫

No comments: