Friday, 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 55-56

๐Ÿ’„Fawzan ko Adeel?๐Ÿ’  


Written by MSB✍๐Ÿป
 Story by Maryam Sb (MSB) ๐Ÿ˜˜๐Ÿ’•    

 ๐Ÿ‘„๐Ÿ’‹


     Page 55-56  


 Fitowa Gwaggo tayi tsakar gida tana kalle kalle, hango Adeel tayi jikin katangar kitchen yana zuba fura cikin dan kwano, yana ganin Gwaggo ya aje kwanon da sauri ya nufo ta yana zuwa ya shiga jan hannunta suka fita zaure. “Kai lafiya Barkindo?” (The blessed one, haka take kiransa) Kalle kalle ya fara yi sannan ya dan yi kasa kasa da murya “Gwaggo anya yaronnan banda idonshi daya samu matsala bakaganin kwalwanshi ma ya ta6u?” “A gaskiya Barkindo ni har tsoro ya fara kamani ga wannan yaro, ko zaki ruga ka kira mahafinka Gidado tare da mai maganin da ke duba shi?” “Eh Gwaggo bari na kirasu, amma kema ki tafi wurinshi ki zauna dashi ko?” “Yanzu kuwa bari na shiga ciki” Da sauri Adeel ya fita waje inda Gwaggo ta koma ciki, kwantar mata da hankali ta shiga yi inda da kyar ta samu tayi shiru duk ta birkice ta rikice ita Fawzan ne kawai wannan Adeel din.   Tafe suke ko wane dauke da robar fura da nono saman kai suna tafe suna hira jefi jefi. “Shatu” Jummala tace tana dan rage saurin tafiyar da takeyi “Na’am Jummala” “Niko in tambaye ki mana” “Dakatawa tayi tare da juyowa saitin Jummala “Ina jinki” “Wannan yarinyar da ke gidanku dinnan har yanzu bata farfado ba ko?” “Eh toh bata farfado ba har da safe da zan fito talla tana bacci” “Toh yaushe zaku maida ita garinsu?” Ta6e baki Shatu tayi “In banda abinki Jummala waya san garinsu? Dole sai ita da kanta idan ta warke zata nuna hanyar garinsu sai a maida ita” “Yanzu kina nufin nan cikin gidanku zaku  barta? Bakusanta ba, bakusan daga ina take ba, sannan bakusan asalinta ba wannan duniyar sai ku yarda ku barta cikin gidanku?” “Toh ya kike so muyi? Baffa ne ya kade ta fa dole dawainyarta zata dawo hannunsa har sai ta warke har kin manta al’adar garinnan? Muddin kai kayi sanadin ta6uwar lafiyar wani ko wata dole kai zaka dauki nauyinsa...” “Ban manta ba amma ina jiye maki abinda zaije ya dawo ne” “Kamar yaya Jummala?” Dafata tayi suka koma gefen hanya  “Kinsan dai Barkindo dan uwanki ne na jini ko? Ma’ana da babanki da babansa uwarsu daya ubansu daya, sannan duk garinnan ba wanda baisanku tare ba da kalar soyayyar da kike masa ko ba haka ba?” Ta gyada kai “Tabbas hakane, duk duniya ba wanda nakeso sama da Barkindo, shima kuma yanaso na kamar yadda nake sonshi” “Alhamdulillah, toh matsalar kwara daya ce tak” “Menene?” “Wannan bakuwar mana, tabbas yarinyar kyakkyawa ce komu da muke fulani ba abinda zata nuna mana, kinga gashinta kuwa har gadon baya, ni da nake mace ta birgeni balle namiji, toh tabbas sai kinbi a sannu don kina ji kina gani za’a ruguza maki ginin da kika dade kina yi lokaci daya zai ruguje” “Kamar ya fa?” “Wannan yarinyar nake nufi, kisan yadda kikayi ko da wasa kar Barkindo ya fara sonta, in ba haka ba zaki koma yar kallo” “Jakar uba! Wallahi bazata sa6u ba, ke har naji na tsani yarinyar da farko naji tana bani tausayi amma yanzu haushi take bani!” Jummala ta kyalkyale da dariya “Meye abin jin haushi a nan? Tunda ba cewa yayi yana sonta ba? Mune da hasashe fa, amma wannan zancen zai iya zama gaskiya, nidai fada maki kawai nake don kisan irin takunki tam!” “Lallai ya zama dole nasan yadda zanyi a maida ita garinsu tun wuri kafin ta gama dani, don rabani da Barkindo kamar rabani da rayuwata ne baki daya, bazan jure ba” “Da yafi kawata, kinga yamma nayi kizo mu wuce gida kafin magrib ta riske mu a hanya” Tafiya suka cigaba da yi suna tattaunawa har suka rabe ko wace tayi hanyar layinsu.   Da sallama ta shiga gidan, Gwaggo ta iske bakin murhu tana fama da itace, tsugunnawa tayi  “Gwaggo jam hilliri?” “Jam ni, sai yanzu Shatu?” “Wallahi Gwaggo yau ba cinkin sosai, ga wanda nayi” ta mika mata “Allah yo6o, (may Allah reward you)” “Ameen” “Ungo wannan ki kai ma marar lafiyar nan ki tabbatar yasha maganin” Ta yamutsa fuska “Gwaggo zan zagaya bayi ne ko ki bata” Kafin Gwaggo tayi magana Adeel ya shigo da sallama “Gwaggo jam hilliri?” “Jam ni, Barkindo ungo ka taimaka ka bata maganin nan, ina talge ne na riga da na fara kuma lokacin shan maganin ya wuce ma” “Toh Gwaggo kawo” Da gudu Shatu ta dawo wacce har ta kai bakin kofar toilet “A’a Gwaggo bari na bata nama fasa shiga bayin” ta fadi tana warce kwanon maganin a hannun Adeel.  “Toh! Allah wallu! (May Allah help)”  A hankali take tafiya dakin tana zuwa bakin kofa taja ta tsaya tana kare mata kallo tana ta6e baki. “Waye nan?” Samha ta fada tana kalle kalle sai kace tana gani, har yanzu idonta nade yake ba’a bude shi ba. “Ke nice fa Shatu” “Wacece Shatu?” “Yar masu gidan” ta fada tana karasawa cikin dakin tana hararan Samha Mika mata kwanon tayi sai kace ganinta take “Ke ki kar6a mana!” “Menene?” “Maganin” Lalube ta fara yi tana neman maganin, ita ko Shatu taki mika mata shi yadda zata ji saukin ansa Sai harara take watsa mata, gajiya Samha tayi ta daina laluben “Zanfa zubar maki dashi a jiki!”  “Ke Shatu lafiyanki? Menene haka?” Husky voice dinsa ce ta daki dodon kunnenta, juya kanta ta farayi tana neman shi. “Kai Shatu bakida hankali amma, marar lafiyan kike ma tsawa? Kuma da haka zata kar6i maganin? Kawo nan idan bazaki bata ba ni na bata” “A’a zan..” “Kawo nace” ya fada yana mika hannunsa alamun ta bashi Zum6uro baki tayi idanunta cike dam da hawaye, dungura masa kwanon tayi sannan ta fice da gudu daga dakin. “Yi hakuri kaji tashi kasha magani” “Fawzan?” Tace tana murmushin jin dadi Bai tanka ta ba ya bata maganin bayan ta tasha ta kara maimaitawa tana ta murmushi “Fawzan? Kaine ko?” Kura mata ido yayi yana kallon pink lips dinta yadda suke motsawa “Fawzan daman nasha fada masu kana raye sukace ka mutu” ta fada tana ta murmushi “Waye Fawzan? Ni sunana Adeel(Barkindo) wannan Fawzan din da kike kira wani ne daban bani ba” “Wallahi kaine, ga muryar nan inaji” “Ay murya kace, zai yuwu munada murya iri daya, amma har yanzu bakaga fuskana ba, bakasan ya nake ba, kaga murya kawai kaji” Rungume hannyenta tayi hade da langwa6ar da kai “Ko banga fuskarka ba zuciyata ta aminta dakai a matsayin Fawzan” “Bani bane, ni nan na tashi tun ina yaro, wancan wani ne daban kaji kam?” Tayi murmushi mai sauti “Fawzan kenan, duk ranar da Allah yasa na fara gani xan tabbatar maka da zance na” Shima murmushin yayi mai sauti “Wai har yanzu bamu san sunanka ba?” “Fawzan har ka manta sunana? Nice fa Khadijanka your beloved Samha” “Ni bana gane wannan yaren” Tayi dariyi “Turancin? Kai fa kake koya mun turanci a gida” “A’a yake koya miki dai” Tayi murmushin jin dadi “Ina so nayi alwalla zanyi sallah” Tashi yayi ya samo sanda ya sa mata cikin hannu. “Taso muje na kaiki kiyi”  “Kokarin mikewa tsaye, bayan ta mike ya rike mata sandar tana rike da sandar itama suka fito daga dakin” Ba kowa tsakar gidan da alama Gwaggo na sallah itama Buta ya cika mata da ruwa sannan ya jagorance ta har bakin toilet ya bude mata kofa “Shiga ki fito zan jira ki a nan” Shiga tayi tana lalube da sandar shikuma ya rufo mata kofar, bayan minti uku ta fito ya taimaka mata tayi alwalla, har daki ya kaita ya shimfida mata prayer mat ya bata hijabi, saitata yayi daidai gabas yace tayi sallarta zaije masallaci ne, gyada kai tayi shi kuma ya fita daya tabbatar ta fara. Shatu dake lekensu tun dazu daga dakinta ta fito gaba daya rike da kugu, cizon yatsa tayi ta shiga girgiza kanta. “Lallai zancen Jummala na shirin xama gaske, indai hakane kuwa ba yarda zanyi ba, ba wace shegiyar da ta isa ta kwace man Adeel ba, wallahi tayi kadan...” tana gama fadin haka ta shige dakinta ta kullo kofar da niyyar da safe zata koma wurin Jummala ta taimaka mata da mafita.                 God bless y’ll ❤️ Allah kara lafiya MSB ๐Ÿ‘๐Ÿผ

No comments: