Friday, 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 65-66

πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’  


Written by MSB✍🏻
Story by Maryam Sb (MSB) πŸ˜˜πŸ’•    


πŸ‘„πŸ’‹    


Page 65-66  


Wani irin razanannen ihu Shatu ta kurma sannan ta dora hannu saman kai tace “Wayyo Allah na shiga uku na....!” Da sauri Samha ta toshe mata baki tana watsa mata da wani mugun kallo tace “Shhh!” Adeel kuwa bige mata bakin yayi cikin rada rada yace “Bakida hankali ne?” Ta zum6uro baki tana watsa ma Samha harara gaba daya haushinta takeji  A hankali suka shiga barin wurin iccen suna ritsawa cikin daji a hankali.  Tsayawa Haidar yayi jin ihun mutum yana dube dube yace “Wace dabbar ce ke mana ihu akai haka?” Sannan ya cigaba da tafiya inda ya jiyo sautin ihun. Dubawa yakeyi sosai yana surfa masifa da bala’i akan Samha ta fito tun kafin ta bari ya kama ta. Cigaba da tafiya su Samha sukeyi Adeel na rike da sandarta, sunyi nisa sosai inda Samha tace ta gaji suka samu wani wuri suka 6uya. Sai da ta huta suka cigaba da tafiya sosai inda Adeel yace bari yayi facing dinsa “A’a Fawzan baka san waye Haidar ba sheyasa kace haka, amma koda wasa kar ka fita ya ganka fitanka na nufin kai kanka ga hala ne...” “A’a Khadija nifa namiji ne bana tsoronsa, bari na fita kawai na nuna masa shi karamin kwaro ne” “A’a Fawzan bashi kadai bane yanzu haka da mutanensa ya taho nan wanda zasu taimaka masa a harkar muguntarsa...” “Toh ya kike so ayi? Muyita 6oyewa haka?” “Eh idan ya gaji bai ganmu ba nasan zai hakura”  “Khadija gaskiya na kasa samun sukuni banga su Baffa ba idan yayi masu wani abin fa?” “Hakane amma idan har ka fita rayuwarka na cikin hadari, Haidar baida imani ko kadan” “Wai waye ne wannan mutumin zai zo ya takura ma rayuwar mu haka kawai” cewar Shatu “Shhh!” Naji tafiya  “Billahillazai ki fito Samha! Bazan maki da sauki ba kika bari na fiddo ki, ki fito kiga gawarwakin yan garinku yashe kasa” Wucewa yayi yana dube dube still bai gansu ba, haka akayita abu daya yana nemansu suna guduwa har gari ya fara haske, fitowa sukayi suka koma cikin gari inda da gaske sukaga gawarwakin mutane kwance kasa duk sun kone, wasu kuma da rai amma sunji ciwo da yawa matan sai kuka suke suna neman agaji. “Innalillahi wa inna ilahir rajiun” kawai Samha ke fadi inda Adeel ke fadi mata halin da garin ke ciki, kuka ta fashe dashi tace “Ka gafarce ni Fawzan duk wannan bala’in nice na jawo maku shi, Innalillahi wa inna ilahir rajiun kuyi hakuri kuyi hakuri” “Kar ki sake fadin haka Khadija, ba ruwanki wannan azzalumin ne kuma insha Allah zai ga karshensa amma yanzu muje mu nemo su Baffa, kinji?”  Shatu ta fashe da kuka itama tace “Allah yasa basu mutu ba” sauri sukeyi, suna cigaba da tafiya still Adeel ke rike sandar Samha shida Shatu suna dube dube inda mutane ke kwance, can wani wuri suka hango su Baffa yashe suna zuwa suka zube kasa, Adeel ne ya shiga duba su inda ya gane Gwaggo ta rasu Baffa ne keda sauran rai. “Baffa!” Cewar Khadija cikin kuka “Wayyo Allah na Gwaggo ta rasu? Baffa kar ka mutu ka barni” shatu ta kurma ihu tana kuka sosai shima Adeel hawaye ke kwarara. Kallon Gwaggo yayi yaga yadda taji ciwo sosai duk jini jikinta, Baffa ne yayi tari mai wahala inda ya kone a hannu da kuma rabin fuska, sai wani 6angare na jikinsa. “Bar...kindo...” yace da kyar da sauri yace  “Na’am Baffa sannu” “Barkindo mutuwa zanyi amma akwai wani alkawari da zaka daukar man” “Bazaka mutu ba insha Allah Baffa, Wane alkawari ne fadi ko meye zan maka indai baifi karfina ba in Allah ya yarda” Tari ya sake yi cikin azabar ciwon da jikinsa ke masa yace “Ina so ka daukar mun alkawarin ko bayan raina zaka auri Shatu da Khadija, kar ka wulakanta su Barkindo, ka rike su amana, tun tuni na fahimci abinda ke ranka gameda Khadija, don haka ka aure su gaba daya kaji?” Girgiza kansa yayi yana hawaye  “Insha Allah Baffa zan maka abinda kakeso, tashi mu tafi asibiti” Girgiza kansa Baffa yayi “Kayya Barkindo! Ka barni nan kawai na ida cikawa, akwai wani abu da zan fada maka kuma” “Menene?” Yace yana rike masa hannu “Da...man kai... ina so kaje ka nemi iyayenka, ba nan bane tushenka Barkindo...” “Kamar yaya Baffa?” “Ina nufin... ba... nan... bane...” (coughing)  “Ba...mu bane... iyayenka na asali kamar yadda na fada maka a baya... amma ban fada maka gaskiyar al’amarin ba...” “Baffa ka fada man sannu” “Barkindo...Bark.... la’ila ha illallah Muhammad rasulillah....”  “Innalillahi wa inna ilahir rajiun” yace tare da fashewa da kuka mai tsanani. Samha da Shatu kuka suka sa sosai.  Huci Adeel ya fara yi kamar zaki ya mike tsaye tare da dunqule hannu. “Khadija! Yau sai na koya ma Haidar hankali”
“A’a Fawzan! Kar kaje!” Ina har ya kama hanya yana tafiya wane kura taga nama.  “Haidar! Haidar! Kana ina ka fito ina jiranka nan!” Nan ya cigaba da kwala masa kira inda Haidar da guards nasa sunfi su biyar suka mara masa baya. Fitowa yayi inda Haidar yace “Kai kuma waye kake kirana?” Kukan kura Adeel yayi ya shako masa wuya da dukkan karfin da Allah ya bashi. Guards sukayo kan Adeel gadan gadan Haidar ya tsaida su ta hanyar daga masu hannu.  “Mugu! Azzalumi! Shaidani!” Adeel yace yana kara kai masa shaqa Kokarin kwace kansa ya shiga yi inda da kyar ya 6an6are hannun Adeel sannan ya watsa shi kasa, da sauri ya tashi inda ya kai masa wani wawan duka a baki da hanci, tuni jini ya balle masa, cikin azabar ciwo Haidar ya jefar da Adeel kasa sannan yayo kansa gadan gadan ya kai masa naushi a ciki, shima Adeel ya mike ya rama nan fada ya 6arke tsakaninsu.  “Waya baka damar kashe mutanen garinnan tare da iyayena, mugu kawai dan iska!” Ya kai masa naushi a fuska, Haidar ya rama nan sukayi ta fada kamar ba gobe, sai da Guards sukaga Adeel na neman kashe masu Boss sukayi sauri suka 6an6are Adeel daga jikin Haidar suka rirrike shi, ya shiga neman kwacewa ya kasa. Jinin dake fuskarsa Haidar ya goga a hannunsa ya kalla, wani irin nishi yayi yana huci ya damqo masa kai ya matse gam gam, Adeel ya nemi kwace kansa ya kasa saboda rikon da guard suka masa. “How dare you? I said how dare you challenge me! Me Aliyu Haidar fighting with a useless and filthy villager like you? No way!” Nan ya shiga naushinsa ta ko ina kafin kace me ya masa jina jina, nan ya sake sa Adeel ya zube kasa yana maida numfashi, da kyar ya tashi tsaye ya nemi ya kai ma Haidar naushi guards suka rike sa gam gam. Kallon shi yake “Where’s my wife? Nace ina matata Samha? Ka fito man da ita yanzu!” “Ashe kasan kalmar mata? Ban tsammanin kasan me ake nufi da wannan kalmar ba!” Halbinsa yayi a ciki da kafarsa. Ya sa yar kara. “Fawzan!” Muryar Samha ya jiyo, ya kalli Adeel dake yashe cikin jini yana lumshe ido yayi dariya, dariyar mugunta yakeyi sannan yace yana clapping hannunsa “Wow! Wow! Lost but found! My adorable run away wife, tana ina?” Kara kwala ma Fawzan kira tayi da karfi “Why are you standing? Are you stupid or what? Go and bring her here!” Yace da guards din. Guda hudu suka tafi suka bar wasu wurin Adeel.  Ba’a jima ba suka dawo rike da Samha da Shatu dake kwala ihu a tsorace “Kar ka ta6a ta!” Adeel yace yana kokarin kwace kansa daga hannun guards din.  Sakinsu Samha  sukayi suka zube kasa. Kallonta yakeyi yace “What’s this baby?” Yace yana ta6a fuskarta, faske masa hannu tayi tace “Don’t touch me Aliyu Haidar!” Ya kyalkyale da dariya “Are you blind baby?” Yace yana kai bakinsa wurin kunnenta. Matsar da fuskarta tayi da sauri ya sake sa dariya.  Guards din yayi ma alamar da su kadai suka gane, damqo Adeel sukayi da shatu suka fara tafiya inda ya finciko Samha tasa ihu. “Fawzan!” Wani kukan kura Adeel yayi ya kwace kansa ya fara gudu yana zuwa ya finciko Haidar tare da shako masa wuya ya kaisa jikin wani icce ya matse shi nan, shaka bata wasa ba  yayi masa take Haidar ya fara neman numfashinsa, guards uku suka yo kansa inda sauran ke tsare da Samha da Shatu wacce ko motsin kirki bata iya yi tsabar tsoro. Kokarin kwace Adeel sukeyi sun kasa, da kyar suka finciko sa da karfi suka yashar da shi kasa. Nan Haidar ya zube yana maida numfashi. Karar jiniya suke ji, inda guards sukace “Kamar fa police!” Kokarin tashi Haidar yakeyi inda kafin kace mey motocin yan sanda sunfi goma sukayi surrounding dinsu, wasu da kayan sojoji suka dinga durowa daga motar suna zagaye su, guards din suka dinga kamawa suna sa masu handcuffs suna tura su mota, Samha, Adeel da Shatu suka saka cikin wata mota daban, inda suka sa ma Haidar bindiga akai. “Aliyu Haidar you’re under arrest, you have the right to remain silent or anything you said will be used against you ina court of law.....!!!” Tuni Haidar yayi surrender ya daga hannayensa sama gamida zubewa kasa. Ogan ya kallesu “Arrest him now  And take care of all the wounded people and the dead...!”                    


God bless y’ll! ❤️

No comments: