Friday, 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 77-78

๐Ÿ’„Fawzan ko Adeel?๐Ÿ’  


Written by MSB✍๐Ÿป
Story by Maryam Sb (MSB) ๐Ÿ˜˜๐Ÿ’•  


  ๐Ÿ‘„๐Ÿ’‹  


   Page 77-78  


 Shiru nayi bayan na natsu ina kallon alkali, Barrister Sufyan ya soma magana “Khadija shin kinji duka laifukan da ake tuhumar mijinki dasu inaso ki bude baki ki fadi duk abinda kika sani”  Shiru nayi kaina kasa, na dago muka hada ido da Haidar ya watsa mun da mugun kallo, na sauke sassanyar ajiyar zuciya nace “Tabbas duk laifukan nan Haidar ya aikata su, tunda aka kaini gidansa yake gana mun azaba har kusan kashe ni yakeyi, wani lokaci kuma yayi mun jina jina, akwai sadda ya kusa halaka ni sai dai na tashi na ganni ana saka mun karin ruwa, sati na kusan daya ina jinya, abu kadan zai hauni da duka, babu magana mai dadi kullum daga fada sai zagi...” hawaye suka gangaro mun ba shiri nayi sauri na goge zuciyata na tafarfasa. Cikin muryar kuka nace “Ya mai girma mai shari’ah Haidar mugu ne azzalumi...” “Wallahi karya kikeyi! Karya take yi mun ya mai girma mai shari’ah” Alkali -“Haidar ka daina karya mana doka ka bari sai kotu ta baka damar maganar sai kayi! Barrister cigaba” “Nagode ya mai shari’ah, Khadija watanku nawa da aure keda Haidar?” “Wata hudu ne” “A cikin wata hudun nan ya ta6a baki wata kulawa da miji ya kamata ya ba matarsa?” Na girgiza kaina a hankali  “A’a bai ta6a ba, sai ma baqar wahala da yake bani” “Shikenan jeki zauna, ya mai girma mai shari’ah inaso zan gabatar da shaidata ta gaba” Alkali- “Bismillah Barrister” “Ina Saudat a cikin kotun nan?” Alkali “Saudat kotu na bukatarki a nan”  Nan da nan Saudat ta bayyana Barrister ya soma magana “Ya sunanki?” “Sunana Saudat Isma’il” “Menene dagantarki da wanda ake tuhuma?” “Mijina ne” “Tsawon wata nawa kika dauka tare dashi?” “Shekara biyu ne” “Inaso ki fada ma kotu irin azabar da ya gana maki ke kuma?” Da sauri Barrister Sunusi ya mike  “Objection my lord! Bai kamata Barrister yana yin shisshigi a yayin tambayarsa ga client dinsa ba” Alkali- “Korafi bai kar6u ba Barrister Sunusi, Barrister Sufyan cigaba” “Nagode ya mai shari’ah, Saudat inaso ki bani amsa ki fada mun irin zaman da kukayi dashi Haidar din?” “Ya mai shari’ah Haidar tun daren farko yayi mun fyade, sannan kamar yadda yake treating Samha haka yake treating dina, azabar yau daban ta gobe daban” “Kinsan irin zaman da sukayi da ita Khadija?” “Nasani duk abinda Khadija ta fada babu karya a ciki, irin zaman da sukayi kenan” “Ko kinsan ko mata nawa ya auro kafin ke da kuma bayan ke?” “A’a bansan wadanda ya aura kafin ni ba, amma bayan ni nasan ya auri mata sama da bakwai a ciki kuwa harda Samha”  “Ya mai girma mai shari’ah ina so kotu ta bani dama zan shigo da matan da ya aura a cikin kotu” Alkali- “An baka” Fita yayi can ya shigo dasu suna biye dashi a baya. Gaban Alkali duk suka tsaya, take Haidar ya fara kakkarwa gumi ya keto masa, kauda fuskarsa yayi tare da runtse ido, tabbas a yadda sharia’r nan ke tafiya baiga alamaun nasara ba, daga kai yayi ya kalli mahaifiyarsa da tuni itama hawaye ya wanke mata fuska. “Ya mai girma mai shari’ah wadannan sune matan da Haidar ya aura bayan ya lalata masu rayuwa ya sallame su, a yanzu haka duk suna dauke da cutar kanjamau wanda shi Haidar din ya goga masu, ina so ku fada mun dankatarku da Haidar?” All- “Matansa ne”  “Da gaske Haidar yana azabtar da mace bayan ya aure ta?” All- “Haidar yana azabatar da mace ta hanyar duka tare da horo mai tsanani, Haidar ya wahalar da mu ba kadan ba” “Kun dade tare dashi?” All- “A’a daga masu wata hudu, biyar, bakwai, shekara daya zuwa biyu dai haka” “Shikenan kuje”  “Ya mai shari’ah akwai sauran shaida kwara daya tak da zan gabatar yanzu idan an bani dama”  Alkali- “Bismillah Barrister” Laptop nasa ya kunna ya saka CD ciki, wani dogon table ya jawo ya daura yadda kowa zai iya gani, dannan play yayi, take incidence din da suka faru tun bayan ya auri Saudat har kan Samha, duk wani mai imani idan ya gani dole hankalinsa ya tashi ganin yadda yake wurgi da dan Adam, kamar wata diyar roba marar rai, duk irin dukan da yake masu komai sai da ya bayyana, take zufa ta jike Haidar jikinsa ya fara kakkarwa, bayan ya gama playing CD din ya kuma cirewa yasa wani, shi kuma yan matan daya kashe ne duka gawarwakinsu ya bayyana.  “A cire mana zuciyar wannan yarinyar, saboda aikin da za’ayi da zuciya da za’ayi shi”  Yana fadi wani yana rubutawa, wata gawar sukaje “Wannan qodarta za’a cire” haka yayita fadi bayan sun gama suka fita. Wani CD ya kuma cirewa wanda mahaifin Samha yayi kafin ya rasu yana kan gadon jinyarsa.  Ina hango mahaifina na miqe da sauri jikina ya fara kakkarwa na tsaya ina saurare “Yata Samha! Ina so ki bani hankalinki nan, da farko dai zan fara da baki hakuri akan aurenki da muka bada ga mutumin da bamusan halinshi ba, tabbas mun tafka kuskure a bisa rashin sani, ba abinda zance sai dai mu baki hakuri kiyi hakuri! Kiyi hakuri ki gafarce mu munyi ne bisa rashin sani, abu na biyu kisani Haidar shi ya tare ni yayi mani fashi inda ya harbeni da bindiga, nasan rayuwata bamai tsawo bace amma inaso idan videon nan ya riske ki, ki danne zuciyarki kibini da addu’a saboda ita nafi bukata kinji yata? Duk ranar da aka qwatar miki yancinki ki cigaba da rayuwarki kamar kowa, sannan ki cigaba da karatun ki, shine kadai abinda ya rage miki yanzu, Allah ya baki wani mijin mafi alkhairi a rayuwarki wanda zai kula dake tsakani da Allah ba tare da cutarwa ba, nine mahaifinki Alhaji Ahmad Shehu, na barku lafiya Allah yayi maku albarka gaba dayan ku” Bansan sadda na zube kasa ba hawaye kuwa wani na bin wani, har wani kakkarwa nakeyi ina jefa ma Haidar Allah ya isa.  “Tashi Samha, ki bar kuka addu’a ita kadai mahaifinku ke bukata, tashi” mom tace tana kokarin daga ni sama, da kyar na tashi ina ganin jiri muka koma mazaunin mu, sai kace sabuwar mahaukaciya duk maganar data tari bakina sai na jefe Haidar da ita, da kyar mom tasa nayi shiru na cigaba da kukana tamkar raina zai fita. Jikin kowa na kotun yayi matukar sanyi, Alkali yayi ajiyar zuciya bayan ya gama kallon videon, rubuce rubuce yayi ya kalli Barrister Sunusi yace “Barrister Sunusi kanada abin cewa?” A sanyaye ya tashi tsaye  “A’a ya mai girma mai shari’ah babu” Alkali- “Barrister Sufyan akwai abinda zakace?” Ya tashi “Babu ya mai girma mai shari’ah” Alkali ya cigaba da rubutu can ya dago tare da gyara zama.  “A bisa tarin hujjoji, tare da duba da laifukan da ake tuhumar Aliyu Haidar, a dalilin haka kotu ta yanke masa hukuncin kisa dashi da muqarrabansa ta hanyar rataya” Wani kukan kura maama tayi ta shake Barrister Sufyan “Qarya ne wallahi! Qarya kukeyi! Dana za’a yanke ma hukuncin kisa? wallahi karya kuke hakan bazai ta6a yuwuwa ba” da kyar Barrister ya 6an6areta, tayo kan Haidar yayi saurin daga mata hannu yana hawaye “A’a maama kar ki ta6ani, ni tawa ta kare amma kafin a yanke kasheni, ina so ki fada ma kotu kece sanadin wannan halin dana tsinci kaina a ciki, kece silar faruwar komai, ki fada masu maama, ki fada masu ke kika jefa danki cikin wannan sa’anar tasa da ya tsinci kansa a ciki, ki fada masu kece da hannunki kika sa danki cikin wannan halin...” ya girgiza kansa “Wallahi duk laifinki ne, duk abinda nake aikatawa kin sani, wallahi tasan komai, hasali ma da taimakonta nake aikatawa”  Gaba daya kotun ta dau salati, jikin maama ya dauki kyarma ta girgiza kanta cike da nadama tana hawaye “Tabbas bakayi karya ba Haidar, duk abinda ya faru dakai nice sila, amma kar ka manta ba’a son raina hakan ya faru ba” “Yanzu ba wanda zai fahimce ki sai kin bude baki kinyi bayani maama, ki fada masu ta yadda kika jefa danki cikin wannan mummunar sana’ar tasa” Kuka takeyi sosai ta zube qasa “Innalillahi wa inna ilahir rajiun, zan fada, tabbas ni na janyo maka halin da kake ciki shekaru masu tsawo da suka wuce a baya....”                



God bless y’ll!  ❤️

No comments: