Friday, 14 June 2019

FAWZAN KO ADEEL PAGE 06

 πŸ’„Fawzan ko Adeel?πŸ’

Written by MSB✍🏻
Story by Maryam Sb (MSB) 😘 πŸ’•

πŸ‘„πŸ’‹

Page 06

Henna ake sa ma Samha lokacin duk suna zaune garden din gidan da yan mata da yawa, wanda yawanci friends na Hilwa dana Amal da Samha ne, sai yan uwa da neighbors kuma da abokan arziki.

Amarya kuwa tana can gefe guda wata daban tana mata henna din irin na amare. A
Hankali wakar Iskaba ke tashi, bayan an gama yin henna din kuma aka shiga serving snacks da drinks.

Bayan an gama kuma akayi kamu wanda ya kayatar amarya ta saka blue lace while yan matan sun saka pink, sunyi kyau sosai.

Washe gari karfe 2:30 aka daura auren Adnan da Hilwa akan sadaki dubu 100, akayi yinin biki kuma bayan nan. Bauchi za’a kaita amma daga baya zasu dawo kaduna da zama.
Don haka ana gama daura aure aka fara shirin kaita, wanda nan kuma aka kaita wurin mom and dad dinsu aka yi mata nasiha sai kuka sukeyi itada su Samha da Amal, nan suka sa mata albarka, Anty Hauwa kanwar dad dinsu ta jawo hannunta suka yi mota da ita, rungume Areef tayi tana kuka itada su Samha, shima idanunshi sunyi ja, nan ya rarrashe ta da kyar aka rabasu inda ya shiga mazaunin driver don shi zai tuka, Samha na gaban mota while Anty Hauwa, Anty Zainab yayar mom da amarya suna baya, Amal tana cikin wata motar daban, nan suka dauki hanya sai Bauchi.

Message ta ma Habibinta sending akan sun kama hanyar Bauchi, nan da nan ya kira ya fara ce mata zaiyi missing dinta, ta dawo soon.

***

2 days later

“Wayace miki kiyi girki da yawa don yan uwanki zasu zo gidanki?”

“Bansani ba” tace a gajiye

“Bafa party bane ya Hilwa” tace tana kallonta

“Na sani, i felt like cooking for all of you, gobe fa zaku tafi Abuja ku bar ni nan Bauchi ni kadai, I just have to make sure I show you how much am gona mish you” ta fada tana mai hudding Samha

Amal na can tana daukan selfie a kowane sako da lungu na gidan wai zata nuna ma Yasmin idan ta koma gida.

 Sauran cousin dinsu kamar Amna, Aysha, Siddiqa da Fatima suna can suna kallon The Johnsons, har dai Samha ta fara kalla ganin yadda suke sonshi.

Samha na zaune amma hankalinta naga masoyinta Fawzan kwana nawa rabon da ta ganshi gaba daya kewarsa ta dame ta, tunanin yadda yake nuna mata kulawa da so take tayi gaba daya hankalinta baya jikinta.

“Samha zaki iya fada mun meyasa kike murmushi ke kadai?”

“Mur...mushi kuma?” Tace cikin rashin fahimta

“Eh mana” cewar Amna tana dariya

“A’a kawai ina tunanin mom ne fa..” ta fada sounding serious

“Toh... bari nayi pretending kamar bansan me kika ce ba”

Dariya Samha Ta kwashe dashi tana hararan Amna.

“Next time da zamu hadu a bikinki, I cant wait to partyyyy”

Bayan an kammala abincin rana ne kowa ya hallara dining aka ci aka sha. Da yamma Adnan yayi dropping dinsu gidansu Fatima da yake nan garin suke da zama.

________

Da safe suka fara shirye shiryen komawa Abuja, dangi duk an fito rakiya, Hilwa kam harda su kuka nan kuma tasa Amal da Samha kukan suma. Da kyar suka rabu ko wane na goge hawayensa.

Suna fita daga Bauchi ta kira Fawzan ta fada masa suna hanya, dadi sosai yaji don yayi missing dinta ba kadan ba, yayi mata addu’ar sauka lafiya. Amal latse latse take a wayanta, Amna kuwa karatun novel takeyi. Aysha da Mufida da Areef labarinsu kawai sukeyi Areef Na driving yana mayar masu idan ta kama.

Samha kuwa jingina tayi da window tayi bacci don idan ta tashi taga an kusa isa ko ma an iso.

See you next episode! Thanks for reading!

No comments: