๐Fawzan ko Adeel?๐
Written by MSB✍๐ป
Story by Maryam Sb (MSB) ๐๐
๐๐
Page 53-54
Zaune yake kan katifar dakin ya wani tisa plate din apple gabansa da yar karamar wuka yana yanka yana kaiwa baki, yana ci yana ma Samha irin kallon zaki sani ne idan na kama ki. Ita dai kallonsa kawai takeyi bata tanka ba. yankowa yayi yasa wukar ya dauko piece din ya taso ya dawo kusa da Samha. “Open your mouth” Kara datse bakinta tayi gam gam, matse bakin nata yayi da hannunsa, ba shiri ta bude bakin ya ingiza mata apple din ciki. “Chew it baby” Taki tauna take ta wullo masa shi a fuska. A hassale ya daka mata tsawa “Ya za’ayi na baki apple with so much love ki zubar mun dashi? Are you kidding me?” Dariya tayi “With so much love fa kace? Lallai na tabbatar bakada hankali yau” A gigice ya kalle ta “Nine banida hankali ma? Samha har rainin wayonki ya kai haka? Iye?” Ta harare shi hade da jan tsuka “Mtss har abinda yafi rashin hankali ma xan iya kiranka dashi, you’re lucky ma marar hankali kawai nace maka, you deserve worse than that” “Samha...!” Ya wani dauke ta da mari mai zafi, dukewa tayi, kafin ta dago ta fara kecewa da dariya kamar mahaukaciya “Hit me again you moron!” Shakota yayi da karfin gaske. “If you utter another word Samha, I promise you’ll pay for it, I’ll make sure I make your life a living nightmare understood!?” Sakinta yayi da karfi ya mike ya fice. “Today Samha I will get what I want and you will do nothing, yau zan gama da rayuwanki, i’ll make sure I destroy your pride! Ba zaki sake daraja ba Khadija Ahmad! Ha! Haa! Haaa!!! Today i’ll get what I want, and you will get pain for the rest of your stupid life! Guard!!!” Daga haka ya fice kamar wani guguwa. Ganin wukar tayi yashe daidai kafarta, tunanin yadda zata dauki wukar tayi, ganin batada wata mafita yasa ta harde kanta tuni ta wulkita kasa daga ita har kujeran yar kara tayi saboda yadda ta bigi kanta da kasa, kalla tayi taga kuma tayi nesa ta kujerar, da sauri ta dinga jan kanta har Allah ya taimaketa tazo daidai wukan, da kyar ta jawo ta da hannunta sai nishi take tsabar wahala, gagara wukar ta dinga yi a wahalce da kyar wayar ta yanke hannunta guda biyu suka warware, gagara na kafarta ta dinga yi da kyar ta yanke, na jikinta ma haka, bayan ta yanke duka tayi Sauri ta zare wayar ta mike, dingishi ta dinga yi har ta isa bakin kofa ta leka taga guard sai sharar bacci yake kamar matacce, da sand’a ta dinga tafiya ganin kofofi har uku ta rasa wace zata bi, kawai tabi ta farkon da dingishi ta dinga tafiya, ga uban duhu wurin kasancewar dare ne, wata window ta gani ta leka, ganin waje yasa ta fara kokarin durawa, amma tsoro takeji ganin nisan wurin, kafarta ta sako ta waje taji akwai abin takawa, tafiya ta dingayi a daddafe bisa siririyar katangar, tana zuwa edge din ta runtse ido ta dura, tana sauka ta mike da kyar ta fara gudu kamar zata tashi sama. Gudu ta dinga yi ba tsayawa, ta dinga ratsa jeji a tsorace amma ta dake kawai burinta ta bar wurin. Sai da tayi gudun kusan minti 30 sannan taja ta tsaya tana maida numfashi, tafiya take da kyar har wani jiri take gani, zubewa tayi kasa tana maida numfashi, ji tayi kamar motsin mutane ta tashi ta fara tafiya a hankali a tsorace, tafiya ta dinga yi kamar wacce ta sha giya har tayi nisa sosai, kwakwata batasan ina take ba kawai ita dai jefa kafarta takeyi, sam ta gagara ganin titi kalle kalle ta farayi har gari ya dan fara haske. Ganin kamar wani kauye tazo yasa taja ta tsaya tana kalle kalle da mamaki, jiri ta dinga ji yana dibarta batasan ya akayi ba sai dai ta ji wani abu ya ture ta bata ankare ba ta fadi tim kasa! Yana dawowa sai wani cika yake yana batsewa lekawa dakin yayi da mamaki yaja ya tsaya yana kare ma dakin kallo ganin ba Samha ba almunta, a fusace ya shigo dakin ya shiga dube dube kamar mahaukaci. “Oh no!” Fita yayi da sauri ya damqo wuyan guard din ya shiga kai masa naushi a fuska “How dare you! Meye amfaninka? Ina Samha? Nace ina Samha!?” “Ban...san...” kafin ya amsa ya sake kai masa naushi “You’re useless! Find her now! Idan baka dawo da ita ba ka tabbatar sunanka matacce kawai” Fitowa yayi ya cigaba da dubawa yana kwala mata kira wane mahaukaci. ^^^^^^^^^^^^^*^^^^^^^^^^^^^^ A hankali ta bude idonta da sukayi mata nauyi, kokarin tashi zaune take kasa “Mihofnima! (Hello!)” Muryar wata tsohuwa taji, sauarenta Samha ta tsaya yi tana kokarin tashi zaune ta kasa. “No’awani? How are you?” Ita sam bataji wane yare take ba, hakan yasa tayi tsai tana sauraronta kamar wata sabuwar hallita, “Meyasa bana gani? Me aka sa mun a ido?” Cikin harshen fulatanci amma hausa tsohowar tace “Kontar da hankalinka yaro, bakada lafiya ne, kaji ciwo a ido, yanzu za’a zo a duba ka” Tsoro ya cika ta, ita sam bata ganin komai, gashi an nade mata ido da wani abu mai nauyi. “Assalamu Alaikum” muryarshi ce ta daki dodon kunnenta, ko a mafarki ko a farke bazata taba manta muryar ba, a zabure ta mike zaune tana lalube “Faw... Fawzan...!” Shima cikin harshen fulatanci yace “Gwaggo, meke damunshi? Waye Fawzan kuma?” “Zauna ADEEL! yaron da babanka ya banke ne toh ya farka” “Allah sarki sannu! Allah bashi lafiya” “Ameen” “Fawzan! Kana ina? Nice Samha! Ashe baka mutu ba?” Ta fada tana lalube “Toh! Kodai kwalwanshi ya ta6u ne Gwaggo? Naji tana kiran wani wai bai mutu ba” Tashi Gwaggo tayi tana rike Samha amma ina Fawzan kawai take kira duk ta haukace. “Ku bude mun idona na ganshi! Ku bude mun ido na naga Fawzan! Shine wallahi nasan muryarshi ko a ina nake! Ku taimaka ku bude mun idona!” “Yaro bazaka sake gani ba kaji yanzu sai a hankali, ka kontar da hankalinka kaji kam?” “Toh ina Fawzan dina? Kice masa yazo wurina” “Bansan waye haka ba yaro, wannan Adeel sunansa ba Fawzan ba” “Wallahi Fawzan ne! Naji muryarshi fa” “Tam shine kaji kam! Konta ka huta zan masa magana yanzu” Da kyar ta kwanta amma bata fasa kiran Fawzan ba.......! God bless y’ll ❤️ and GWS MSB ๐
No comments:
Post a Comment